Saliba Ya Sabunta Kwantiraginsa Da Arsenal Har Tsawon Shekaru 5
Published: 25th, September 2025 GMT
Sabon kwantiragin ya nuna Arsenal na son kare shi daga ƙungiyoyi manya na ƙasashen Turai irin su Real Madrid da Manchester United.
Arteta na fatan hakan zai taimaka wajen cika burinsa na lashe gasar Firimiya.
Haka kuma, abokin Saliba a tsaron baya, Gabriel Magalhães, ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2029.
Arsenal za ta kara da Newcastle a filin St James’ Park a ranar Lahadi, inda ake sa ran haɗin Saliba da Gabriel zai ƙara ƙarfafa bayan ƙungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Arsenal Kwantaragi
এছাড়াও পড়ুন:
Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi
A ranar Alhamis, 27 ga watan Nuwamban 2025 ce Allah ya yi wa fitaccen malamin addinin Musuluncin nan kuma jigo a Darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi rasuwa.
Ya rasu yana da sama da shekaru 100 a duniya.
Allah Ya yi wa Sheikh Dahiru Bauchi rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi: Malamin da zuri’arsa ta fi kowacce yawan mahaddata Alkur’aniBaya ga tarin iliminsa da yawan shekaru, akwai wasu tarin baiwa da Allah Ya ba malamin, wadanda ba kowa ne ya san da su ba.
Aminiya ta yi nazari a kansu, inda ta zakulo muku abubuwa 18 da ya kamata ku sani a kansa.
Ga wasu daga ciki:
Ya fi kowa yawan zuri’ar da ta haddace Alkur’ani a duniya, inda yake da ’ya’ya da jikoki da tataba-kunne kusan 300 da suka haddace Alkur’ani mai girma Kundin tattara bayanai na Cholan Book Of World Records, ya ba shi shaidar girmamawa saboda yawan zuri’a mahaddata Yana da ’ya’ya 95 Yana da jikoki 406 Yana da tattaba-kunne 100 ’Ya’yansa mahaddata Alkur’ani 77 Jikokinsa mahaddata Alkur’ani 199 Tattaba-kunnensa mahaddata Alkur’ani 12 Shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Koli da ke bayar da fatawa a addinin Musulunci a Najeriya An haife shi a watan Janairun 1927, wanda ya yi daidai da watan Muharram 1346 Bayan Hijira A ranar Laraba aka haife shi a a garin Nafada da ke Jihar Gombe a yanzu Kwararre ne a fannin Alkur’ani da Tafsiri da Ma’arifa da Hadisi da Harshen Larabci da Li’irabi da Fikihu Jami’ar Tarayya da ke Lafiya a Jihar Nasarawa ta ba shi Digirin girmamawa Gwamnatin Najeriya ta ba shi lambar girmamawa ta kasa ta OFR Ya musuluntar da dubban mutane Yakan yi saukar Alkur’ani duk bayan kwana biyu Mutane fiye da 140,924 suka haddace Alkur’ani a makarantunsa da ke fadin Najeriya Ya kafa makarantun haddar Alkur’ani sama da 1,500 a Najeriya da wasu kasashen Afirka Karkashin gidauniyasa, an gina dakunan karatu guda 133,060 a Arewacin Najeriya Ya shafe shekaru sama da 50 yana gabatar da tafsirin Alkur’ani a cikin watan Ramadan