HausaTv:
2025-11-02@18:11:14 GMT

E3 za su gabatar da bukatar dawo da takunkuman MDD a kan Iran: Reuters

Published: 28th, August 2025 GMT

Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa Birtaniya, Faransa da Jamus suna shirye-shiryen mayar da takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakabawa Iran a shekarun baya.

Kasashe uku na Turai, da aka fi sani da E3, sun gana da jami’an Iran a ranar Talata a wani abin da aka bayyana a matsayin dama ta karshe na ceto huldar da ke gabansu na yin amfani da batun yarjejeniyar nukiliyar 2015, wanda wa’adinsa zai  kare a tsakiyar watan Oktoba.

Duk da cewa jami’an diflomasiyyar Turai sun yi iƙirarin cewa tattaunawar ba ta samar da hanyoyin warware batun kamar yadda suke bukata ba, amma Tehran ta nanata cewa tana nan a shirye don tattaunawa mai ma’ana, muddin aka mutunta haƙƙinta da kuma kawar da duk wata barazana daga waje.

E3 na shirin ƙaddamar da matakan ne mai yiwuwa daga wannan  Alhamis. Wadannan takunkuman dai za su sake shafar muhimman harkokin kudi, makamashi, hada-hadar bankuna, da kuma bangaren tsaro na Iran, lamarin da zai kara yin tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Kamar yadda wani jami’in diflomasiyyar kasashen yammacin duniya ya yarda, “Za a fara tattaunawa kan batun da zarar an mika wasikar (ga kwamitin sulhu na MDD).

Berlin ta tabbatar da cewa wannan batu yana kan nazari, yayin da London da Paris suka yi gum da bakunansu. A nata bangaren, Tehran ta bayyana karara cewa za ta mayar da martani mai tsauri idan aka kakaba mata takunkumi, wanda ke nuni da matakin da ta dauka na kin mika kai ga matsin lamba na bai daya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Shugaban Rwanda ya musunta zargin sojojin kasarsa da hannu a rikicin Congo August 28, 2025 ASUU: Gwamnatin Najeriya ba ta aiwatar da ko daya daga cikin bukatunmu ba August 28, 2025 Iran da Rasha Sun Zasu Hadakai A fagen Watsa Labarai August 27, 2025 IRGC Sun Halaka Yan Ta’adda 13 A Yankin Sistan Baluchestan August 27, 2025 Zanga-Zanga Ta hana Wakilin Amurka Ziyara A Kudancin Lebanon August 27, 2025 Hamas: Isra’ila Tana Rike Da Gawawwakin Falasdinawa 726 August 27, 2025 Isra’ila Ta kashe Falasdinawa Fiye da 1000 A Yamma Da Kogin Jordan August 27, 2025 Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Za Su Iya Komawa Zaman Tattaunawa Da Amurka A Kan Wasu Sharudda   August 27, 2025 Masu Binciken Hukumar IAEA Ba Za Su Shiga Wajen Da Amurka Ta Kai Hari Ba A Cibiyoyin Nukiliyar Iran August 27, 2025 Kasar Venezuala Ta Jinjinwa Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Kyakkyawar Hadin Kai Da Ke Tsakanisu August 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya

Shugaba Trump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya, yana mai zargin gwamnatin kasar da kyalewa ana kashe kiristoci.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Trump ya ce Washington na iya shiga Najeriya da ƙarfin soji don kakkabe abin da ya kira ƴanta’adda masu kishin Islama da ke aikata ta’asa.

Ya kuma yi barazanar dakatar da duk wani taimakon da Amurka ke bawa  Najeriya.

Tuni Najeriya ta yi watsi da ikirarin cewa ana kashe kiristoci ba gaira ba dalili a yankin arewacin inda galibi musulmi suka fi yawa.

A bayanin da Trump ya wallafa a kafar sadar zumuntarsa ta Truth a ranar Asabar ya ce ya ba wa ma’aikatar tsaron Amurka damar ta fara shirin daukar mataki kan Najeriya – “Idan har gwamnatin Najeriya ta bari ana ci gaba da kashe Kirista,” in ji shi.

Shugaban wanda ke da’awar samun lambar yabo ta zaman lafiya a duniya ya kuma yi mummunan kalamai ga Najeriya inda ya ce “Amurka za ta shiga cikin kasar da a yanzu ta wulakanta.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Majalisar Dinkin Duniya ta damu da hare-haren Amurka a Caribbean da Pacific November 1, 2025 Israila Ta Kai Hari  Kan Ofishin kungiyar UNICEF Dake Gaza A November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • IAEA : Babu wata shaida da ke nuna cewa Iran na kera makaman nukiliya
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya
  • Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan
  • Iran Ta Sanya  Da Ranar 30 Ga Watan Nuwamba A Matsayin Ranar Kasa Ta Tsibirai 3
  • Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
  • Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta