Putin da Trump sun tabbatar da aniyarsu ta kawo karshen rashin jituwa da warware batun Ukraine
Published: 16th, August 2025 GMT
An kammala taron tattaunawa tsakanin shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Alaska na kasar Amurka, inda bangarorin biyu suka bayyana taron a matsayin mai matukar amfani.
Fadar Kremlin ta tabbatar da cewa tattaunawar ta yi armashi, yayin da manzon musamman na Rasha Kirill Dmitriev ya bayyana cewa yanayin taron ya yi kyau.
Putin ya jaddada aniyar kasashen biyu na kawo karshen kiyayyar da suke yi da kuma bukatar cimma matsaya domin kawo karshen yakin Ukraine. Ya yaba da yadda Trump ya fahimci muradun Rasha da kuma burinsa na fahimtar ainihin rikicin.
A nasa bangaren, Trump ya tabbatar da cewa tattaunawar ta kai ga cimma matsaya a kan batutuwa da dama, yayin da wasu manyan batutuwa suka rage. Ya yi nuni da cewa, zai ci gaba da tattaunawa da sauran bangarorin, ya kuma yi tsokaci da cewa a ganawarsu ta gaba za ta kasance a birnin Moscow.
A jiya ne aka fara taron koli tsakanin shugabannin biyu a filin tashi da saukar jiragen sama na Alaska tare da tattaunawa a cikin motar shugaban na Amurka.
Trump ya shaida wa Fox News cewa yana son ganin an tsagaita bude wuta a Ukraine kuma ba zai ji dadi ba idan hakan bai faru a yau ba. Ya kara da cewa Turawa ba sa gaya mani abin da zan yi, ni ke daukar shawarar abin da zan da kaina.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Takht-Ravanchi: Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa kan hakkinta na nukiliya August 16, 2025 Sudan: Al-Burhan ya ce babu sulhu tsakaninsu da dakarun RSF August 16, 2025 Mali: An kama wasu Manyan Sojoji da Wani Bafaranshe bisa zargin yunkurin juyin mulki August 16, 2025 Wata Kotu a Canada ta ayyana APC da PDP a matsayin kungiyoyin ta’addanci August 16, 2025 Hizbullah Ta Ce Ba Zata Ajiye Makamanta Ba August 15, 2025 China Tace Bata Goyon Bayan A Sake Dorawa Iran Takunkuman MDD August 15, 2025 An Gano Gawar Wani Sojan HKI Wanda Ya Kashe Kansa Saboda yakin Gaza August 15, 2025 India Ta Dage Kan Maida martani da hana Shigowar Kayakin Amurka Kasar August 15, 2025 Duniyarmu A Yau: Ranar 40 Ta Imam Hussain (a) A Bana August 15, 2025 Larijani: Iran Zata Mayar Da Martani Mai Tsanani Kan Duk Wanda Ya Kai Mata Hari August 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’Ila Har Sau Shida
Sojojin Yemen sun sanar da cewa: Sun kai hari kan muhimman wurare hudu na haramtacciyar kasar Isra’ila da jirage marasa matuka guda shida
Sojojin Yemen sun sanar a yammacin jiya Talata cewa: Sun kai farmakin soji ta hanyar amfani da jiragen sama marasa matuka ciki guda shida, inda suka kai hari kan wasu muhimman wurare 4 na haramtacciyar kasar Isra’ila a yankunan Haifa, Negev, Umm al-Rashrash, da kuma Bi’ersheba na Falasdinu da aka mamaye.
Kakakin rundunar sojin kasar Birgediya Janar Yahya Sari’e ya tabbatar da cewa: “Ayyukan sun cimma nasarar cimma manufofinsu,” yana mai jaddada ci gaba da ayyukan bayar da tallafi har sai an daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza.
Sari’e ya ce: Ci gaba da aiwatar da shirin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi na da nufin kawar da al’ummar Falastinu ta hanyar kisan kiyashi da kakaba yunwa da tilasta musu gudun hijira daga mahaifansu zai haifar da mummunan sakamako ga dukkanin kasashen Larabawa da na musulmi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Wakilan Hamas sun isa Alkahira don shawarwarin tsagaita wuta a Gaza August 13, 2025 Iran: Amurka Da Isra’ila Ne Da Kansu Suka Bukaci Dakatar Da Bude Wuta August 13, 2025 Habasha: Madatsar ruwanmu amfanin dukkanin kasashen yankin ne August 13, 2025 Bankin Duniya Zai Kashe $300m Don Inganta Rayuwar ’Yan Gudun Hijira A Arewacin Nijeriya August 13, 2025 Nijeriya Da Isra’ila Na Kara Karfafa Alaka A Tsakaninsu August 13, 2025 Kasashe 27 Sun Bukaci Isara’ila Ta Kawo Karshen Hana Shigar Da Abinci A Gaza August 12, 2025 Iran: Duk Wani Sabon Hari, Zai Fuskanci Mummunan Martanin Soji August 12, 2025 Larijani: Iraki Ba Ta Karbar Umarni Daga Iran August 12, 2025 Iran: Ma’aikatar Harkokin Waje Ce Ke Kula Da Lamarin Makamashin Nukliyar Kasar August 12, 2025 Armenia Ta Tabbatarwa Iran Zata Kula Da Muradunta Bayan Yarjeniya Da Azarbaijan A Amurka August 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci