Yemen: Ansarallah Ta Yi Kira Ga Hadin Musulmi, Don Kawo Karshen Yaki A Gaza
Published: 5th, September 2025 GMT
Miliyoyin mutanen kasar Yemen sun fito zuwa dandalin taron mutane a dukkan garuwan kasar a bikin murnar zagayowar ranar haihuwar manzon All…(s) a kasar a jiya Alhamis.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Sayyeed Abdulmalik al-houthi, a jawabin da ya gabatar a karshen tarurrukan, zuwa ga hadin kan kasashen musulmi saboda ma’abucin wannan ranar (s).
Ya kuma yi tir da allawadai da ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza. Ya kuma yi addu’a ga shahidan gwamnatin kasar wadanda HKI ta kashe a makon da ya gabata. Har’ila yau a cikin Jawabinsa Sayyid Huthi ya bayyana cewa, mutanen yemen da yardarm All..suna daga cikin wadanda suke raya addinin musulunci bayan rauninsa. Sannan daga cikin ayyukan raya wannan addinin akwai raya wannan ranar ta haihuwar manzon All…(s) da kuma tsayin dakan da suka yi wajen tallafawa al-ummar Falasdinu. Daga karshe sayyeed Huthi ya bayyana cewa, abinda ke faruwa a Gaza, wanda ya hada da hana jarirai madaran sha, yayi muni, kuma yakamata ya tada hankalin dukkan mutane wadanda suke da yan’adamtaka gwagwadon kwayan zirra a cikin zukatansu. Ya kuma yi tir da HKI a kan ta’asan da take aikatawa a ko wace rana a yankin yamma da kogin Jordan.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Fallasa Shirin Natanyahu Da Google Na Farfagandar Ta Dalar Amurka Miliyon $45 September 5, 2025 Majid Takht-Ravanchi Ya Bayyana Halin Da Iran Take Ciki Kan Sabon Zagayen Tattaunawa Da Amurka September 4, 2025 Sakataren Kwamitin Kolin Tsaron Kasar Iran Ya Tattauna Da Takwaransa Na Birtaniyya Kan Shirin Nukiliyar Iran September 4, 2025 Baqa’i Ya Jaddada Cewa; Iran Zata Kare Muradunta Daga Bukatun Tawagar Tuari September 4, 2025 Jami’in Siyasar Kungiyar Hamas Ya Mayar Da Martani Kan Kalaman Shugaban Amurka September 4, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Janyo Shahadan Falasdinawa 79 A Yankin Zirin Gaza September 4, 2025 Araqchi: Iran ba ta fargabar tattaunawa kuma ba ta tsoron kare kanta idan aka kallafa mata yaki September 4, 2025 Najeriya ta ba da izinin binciken danyen mai a karkashin teku ga kamfanin TotalEnergies September 4, 2025 Yemen ta sanar da kai hare-hare biyu kan ‘Isra’ila’ September 4, 2025 Afirka ta Kudu ta aika da wakilai 30 zuwa IATF 2025 September 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya
Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya yi gargadi a matsayin martani ga sanarwar Washington na ci gaba da gwajin makaman nukiliya, yana mai kiran hakan a matsayin wani mataki na koma-baya da Rashin yin da’a ga dokokin kasa da kasa.
Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya soki Washington saboda sauya wa Ma’aikatar Tsaron kasar suna zuwa Ma’aikatar Yaki, kuma ya yi Allah Wadai da Shirin Amurka na yin gwajin makaman nukiliya, tare da bayyana hakan a matsayin yunkurin tayar da zaune tsaye da jefa duniya a cikin bala’i.
Wanda yake aikata irin wannan halayya ne ke ci gaba da yin barazanar sake kai hari kan cibiyoyin nukiliya na Iran bisa hujjar hana Iran mallakar makaman nukiliya da sunan kare kansu daga Iran domin kada ta mallaki makaman kare dangi.” in ji ministan harkokin wajen Iran.
Ya yi Allah wadai da Amurka saboda sukar da ta dade tana yi wa shirin nukiliya na zaman lafiya na Iran yayin da ita kuma take ci gaba da gwajin makamanta na nukiliya, wanda hakan ya saba wa dokokin duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump a ranar Laraba ya bayyana cewa makaman nukiliya na Washington su ne mafi girma a duniya, kuma ya danganta wannan matsayin da gyare-gyare da aka yi a lokacin gwamnatinsa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci