’Yan ta’adda sun kashe mutum 63 a Borno
Published: 7th, September 2025 GMT
’Yan ta’adda sun kashe aƙalla mutum 63 a wani mummunan hari da suka kai a garin Darul Jamal, kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru, a yankin Bama na Jihar Borno.
Gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da cewa daga cikin waɗanda suka rasa rayuka akwai sojoji 5 tare da fararen hula 58.
Tsagin NNPP na ƙasa ya yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin Kofa ’Yan bindiga sun kashe jami’an Sibil Difens 8 a EdoWannan harin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, inda maharan haye a kan ɗaruruwan babura, suka fara harbe-harbe da ƙone gidaje.
Wani mazaunin garin, Malam Bukar, ya shaida wa manema labarai cewa: “Sun shigo suna ta kabarbari da harbi kan mai uwa da wabi.
“Mun tsere da iyalanmu cikin daji, da safe da muka dawo mun tarar da gawarwaki a ko’ina.”
Rahotanni sun nuna cewa gidaje fiye da 20 da kuma motocin bas 10 sun ƙone ƙurmus a lokacin harin ƙarƙashin jagorancin wani kwamandan Boko Haram mai suna Ali Ngulde.
Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito cewa mutanen da aka kashe da dama na daga cikin ’yan gudun hijira da aka dawo da su daga sansanin makarantar sakandare ta Bama.
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta yi luguden wuta tare da sojojin ƙasa, inda suka kashe ’yan ta’adda kusan 30.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa harin ya nuna ƙalubalen da ke tattare da dawo da ‘yan gudun hijira daga sansanoni zuwa ƙauyuka.
A zantawarsa da menama labarai, gwamnan ya ce, “mun zo ne domin jajanta muku bisa abin da ya faru a Darajamal, wanda ya yi sanadiyar kashe mutane da dama.
“Abin baƙin ciki ne, wannan al’umma an dawo da su watanni kaɗan da suka gabata, yanzu kuma sun gamu da wannan masifa,” in ji shi.
Boko Haram da ISWAP sun shafe sama da shekaru goma sha biyar suna tayar da ƙayar baya a arewa maso gabas, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 40,000 tare da raba fiye da miliyan biyu da muhallansu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babagana Umara Zulum Boko Haram jihar Borno
এছাড়াও পড়ুন:
Sojoji Sun Harbe Wasu ‘Yan Ta’adda 2 A Taraba
Danja ya ce, sojojin a yayin da suke aiki da sahihan bayanan sirri dangane da shirin kai hari kan al’ummar Chanchangi da kungiyar ta’adda ta Bojo ke shirin yi a ranar 15 ga Satumba, 2025, sun yi artabu da ‘yan ta’addan a kan hanyar Demeva zuwa Chanchangi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp