Aminiya:
2025-09-17@23:15:47 GMT

Yadda dawowar makarantu ta zo mana cikin tsadar rayuwa — Iyaye

Published: 8th, September 2025 GMT

Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu.

Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba.

Kukan Iyaye

A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida.

Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros Riba, ta ce, “Ilmi yanzu ya koma alfarma, ba haƙƙi ba. Duk lokacin da zangon karatu ya zo sai zuciya ta yi nauyi. Duk abin da ka tara sai ya ƙare a kuɗin makaranta.”

A Kano, wani mazaunin unguwar Kurna, Malam Musa Ibrahim, ya yi zargin cewa masu makarantu sun mayar da harkar ilmi kasuwanci mai kama da kasuwancin fetur. “Amma ilmi ba kamar mai ba ne, domin ba za ka iya tsayawa ka yi masa yajin ciniki ba.”

A gefe guda, masu ’ya’ya a makarantun gwamnati suna korafi kan “ƙananan kuɗaɗe” da malaman makarantu ke dorawa, duk da cewa gwamnati ta ayyana ilmi kyauta a matakin firamare da sakandare.

“Sau da dama ana tilasta iyaye su bayar da kuɗin tsaftace makaranta, sayen alli ko ma gyaran kujeru. Wannan ba kyautata ilmi ba ne, illa azabtar da talaka,” inji wata uwa daga Kaduna.

Halin da makarantun gwamnati ke ciki

Daga birane zuwa karkara, rahotanni sun nuna makarantu da dama na gwamnati sun shiga wani hali, inda a wasau waurare ɗalibai da ke yin karatu a ƙarƙashin bishiyoyi saboda rashin ajujuwa.

A jihohin Zamfara da Taraba, wasu makarantu ba su da kujeru balle tebura, dalibai na birgima a kasa suna rubutu. A wasu wurare ma, iyaye ne ke haɗa kuɗi domin ɗaukar malamai masu aikin sa-kai saboda ƙarancin malamai a gwamnatance.

Dakta Ahmed Umar, masanin harkokin ilmi, ya ce, “Yaro da yake zaune a zaune a ƙasa a aji, ba zai taɓa samun daidaito ba da yaron  da ke koyon kimiyya cikin ɗakunan kwamfuta ba,.”

Rashin ingancin makarantun gwamnati ya wajabta wa ma’aikata da matsakaita sanya ’ya’yansu aa makarantu masu zaman kansu, inda suke biyan kuɗaɗe masu tsada fiye da ƙarfin aljihunsu.

A Kaduna da Jos da Legas da Abuja, iyaye sun ce duk da tsadar kuɗin makarantu masu zaman kansu, babu yadda za su yi dole sai sun kai ’ya’yansu zuwa can, saboda ana ganin suna da ƙarfi a bangaren koyarwa da kuma shiryawa jarabawa.

Amma ga talakawa, babu wani zaɓi face su bar yaransu a makarantun gwamnati.

“Tsarin ilmi a Najeriya ya zama hoton bambancin karfin arziki. Yaran masu hannu da shuni suna samun ingantaccen ilmi, yayin da na talakawa ake turawa makarantu marasa kayan aiki,” in ji Farfa Fumilayo Adebiyi daga Jami’ar Obafemi Awolowo.

Iyaye na neman rance

Yawan kuɗin makaranta ya tilasta wasu iyaye neman basgu daga bankuna ko kungiyoyin adashin gata.

A Bauchi, wani ma’aikaci mai yara hudu, Malam Abdullahi, ya ce gaba ɗaya albashinsa na watan Agusta ya tafi wajen biyan kuɗin ɗaya daga cikin ’ya’yansa.

“Na biya N100,000 kuɗin makaranta, N120,000 na mota, sannan na kashe kusan N100,000 wajen littattafai da kaya. Wato N330,000 ke nan ga yaro ɗaya, alhali ina da sauran uku. Idan ba da rance ba, ba zan iya ba,” in ji shi.

Matakan Jihohi

A Kaduna, Hukumar Kula da Ingancin Makarantu (KSSQAA) ta fitar da umarni cewa babu makarantar da za ta ƙara kuɗin karatu ba tare da sahalewar hukuma da amincewar Kungiyar Iyaye da Malamai (PTA) ba.

Haka kuma, hukumar ta hana buga littattafai da aka tsara domin “a rubuta aiki kai tsaye a ciki,” saboda hakan na tilasta iyaye su sayi sabbi duk shekara.

A Jihar Filato, Majalisar Dokoki ta amince a rika amfani da littattafai tsawon shekaru hudu kafin a sake maye gurbinsu, domin rage radadin kuɗaɗen makaranta ga iyaye.

Masana sun yaba da wannan mataki, amma sun ce tilas ne a samu tsauraran matakan doka, in ba haka ba, za a koma halin da ake ciki yanzu.

Koken iyayen dalibai

Malama Halima Mu’azu daga Hayin Malam Bello a Jihar Kaduna ta ce kuɗin makarantar ’ya’yanta ya tashi daga N27,000 zuwa N32,000. “Dole na rage abinci a gida saboda kuɗin makaranta.”

A garin Jos na Jihar Filato kuma, wani mazaunin Anguwan Rogo, Ibrahim Isa, ya ce, “Makarantu masu zaman kansu sun fita daga aljihun talakawa. Mutum ba zai iya biyan N80,000 ba alhali abincin ma ya gagara.”

A Makurdi, Jihar Binuwai, Attah Ede ya ce makarantar ’ya’yansa ta ƙara kudi daga N60,000 zuwa N120,000 cikin shekara ɗaya. “Wannan ƙaruwa ba ta da hujja.”

Misis Funke Adeyemi ta ce ta ƙi sayen sabbin uniform saboda na da suna da kyau. Wani uba, Ismail, ya ce yanzu ya fi Naira miliyan biyu yake kashewa duk zangon karatu kan ‘ya’yansa uku.

Malam Habu Adam ya ce kawai littattafan ɗa ɗaya ya biya N62,000. Wani kuma, Abdulhamid Yusuf, ya bayyana ya kashe sama da N500,000 kan yara biyu.

A Abuja, wani uba ya ce makarantar ɗansa ta ƙara kudin kwana daga N550,000 zuwa N725,000 a zangon da ya gabata. Wani kuma ya ce ya biya Naira miliyan 2.6. Wani ma’aikaci, Michael John, ya ce yana shirin mayar da ’ya’yansa jihar Kogi saboda tsadar Abuja ta gagare shi.

Masu makarantu sun kare kansu

Wasu masu makarantu sun ce ba su da niyyar cutar da iyaye, kawai hauhawar farashin kaya da harajin gwamnati ne suka tilasta su ƙara kudade.

Abdulganiyu Abdurrahman Giwa, wani mai makaranta a Kaduna, ya ce “Gwamnati ta yi mana tarin haraji. Dole muke canja kuɗin makaranta domin kada makarantar ta durƙushe.”

Ustaz Hussein Onitira, wani mai makaranta a Legas, ya ce, “Farashin littattafai da kayan ofis sun tashi sosai. Da gwamnati ta rage haraji da kuma farashin bugawa, da za mu sauƙaƙa.”

Kiran masana

Masana harkokin ilmi sun ce dole ne gwamnati ta gyara makarantu na gwamnati idan ana son rage wahala ga iyaye.

“Idan gwamnati ta ci gaba da sakaci da makarantunta, to masu zaman kansu za su ci gaba da mulki. Wannan zai haifar da wariyar ilmi tsakanin talaka da mai kudi,” inji Dr. Adekola Lasisi daga Jami’ar Al-Hikmah.

Masanin tattalin arziki, Dakta Tunde Adesina, ya ce hauhawar farashin kaya da rashin karin albashi na ma’aikata na ƙara tsananta matsalar. “Gwamnati na bukatar tallafin kai tsaye ga iyaye domin gujewa rushewar tsarin ilmi.”

Kira ga Ƙungiyoyin PTA

Shugaban PTA na ƙasa, Malam Ɗanjuma Muhammad, ya shawarci iyaye su yi amfani da ƙungiyar PTA wajen hana tilastawa da wasu makarantu ke yi.

“Wasu makarantu ma ba su da lasisi, amma suna cajin kuɗaɗe kamar jami’a. Iyaye su tashi tsaye su nemi hakkinsu,” in ji shi.

Barazanar yawan yara marasa zuwa makaranta

Rahotannin UNICEF sun nuna Najeriya na da fiye da yara miliyan 13 marasa zuwa makaranta — adadi mafi yawa a duniya. Masana sun yi gargadin cewa idan aka ci gaba da wannan tsadar, yawan zai ƙaru.

“Yaro da aka fitar daga makaranta yau, gobe na iya zama ɗan daba ko ɗan ta’adda. Ilmi ba wai na mutum kaɗai ba ne, tsaro ne na ƙasa,” inji Farfa Adebiyi.

Duk da ƙalubalen tattalin arziki, iyaye da dama sun ce za su ci gaba da ba da fifiko ga ilmin ’ya’yansu, koda kuwa za su rage cin abinci ko su rika tafiya a ƙafa zuwa aiki.

“Ina da ’ya’ya uku a Makurɗi. Koda kuwa sau ɗaya a rana za mu ci abinci, ba na son su zauna a gida. Ilmi shi ne gadon da kawai zan iya barin musu,” in ji Misis Angela Tyongun.

Maganarta ta zama murya ga miliyoyin iyayen Najeriya da ke ganin ilmi tamkar hasken fata cikin duhun tattalin arzikin da ake ciki.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: iyaye makarantu yara makarantun gwamnati kuɗin makaranta tattalin arziki zangon karatu a makarantun makarantu ma gwamnati ta

এছাড়াও পড়ুন:

Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi

 

Haka kuma, wannan na faruwa ne makonni biyu bayan yin garkuwa da Pastor Friday Adehi na Christian Evangelical Fellowship of Nigeria (CEFN) tare da wani abokin cocinsa bayan kammala wa’azi. Wannan ya kara nuna yadda matsalar garkuwa ke ta’azzara a yankin Kogi East.

 

A gefe guda, kungiyar lauyoyi ta Najeriya (NBA), reshen Idah, ta bukaci gwamnati a matakai daban-daban da ta dauki matakan gaggawa don kawo karshen satar mutane a jihar. Shugaban kungiyar, Barr. James Michael, ya ce yawaitar garkuwa a kan titunan yankin ya jefa rayukan jama’a cikin hatsari, don haka gwamnati ya kamata ta dauki tsauraran matakai domin kare lafiyar al’umma.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnati ta ƙaddamar da jiragen ruwa na zamani 20 a Sakkwato
  • Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Karatun Tarihi A Makarantu
  • An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • An kama mabaraci da kuɗaɗen ƙasar waje a Ilorin
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa