Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi
Published: 28th, September 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa za ta gwammace ta fuskanci mayar da takunkumin da aka kakaba mata, maimakon ta mutunta bukatar Amurka da ke neman Iran din ta mika dukkanin tataccen Uranium da take da shi.
Da yake zantawa da manema labarai kafin ya bar birnin New York zuwa birnin Tehran, Pezeshkian ya yi karin bayani kan kokarin diflomasiyya a lokacin babban taron Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya hada da ganawa da shugabannin kasashen Faransa, da Finland, da Switzerland, da Norway, da Iraki, da Bolivia, da kuma majalisar kungiyar Tarayyar Turai.
Yayin da yake nuni da cewa an cimma yarjejeniya da bangarorin Turai, ya nuna rashin jituwar da cewa duka daga bangaren Amurka ne.
“Mun cimma yarjejeniya da bangarori na Turai, amma ra’ayin Amurka ya bambanta, kuma abu ne na hankali kan cewa Iran ba zata mika wuya ga dukkanin abin da Amurka take bukata ba, wanda hakan ita kuma ya yi hannun riga da maslaharta.
A ranar Jumma’a, Amurka da kawayenta, wadanda ake kira da E3, suka ki amincewa da wani daftarin kuduri daga Rasha da China, wanda ya nemi jinkirta aiwatar da tsarin dawo da takunkumai kan Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliya ta JCPOA.
Pezeshkian ya kara da cewa Amurkawa “suna son mu ba su dukkan sinadarin uranium da aka tace, wanda ba za a amince da shi ta kowace hanya ba.”
Shugaban na Iran ya nanata cewa da alama Amurka za ta matsa kaimi don “fara mayar da martani” na takunkumin a cikin watanni mas zuwa, yana mai kara jaddada cewa idan aka tilastawa Iran yin zabi, to za ta zabi abin da ya dace da maslaharta da al’ummarta, mai makon biyan bukatar da ba ta dace ba, yana mai shan alwashin cewa “duk da haka, za mu magance dukkan matsalolinmu.”
Ya ba da tabbacin cewa, an dauki matakan da suka wajaba don wannan yanayin, yana mai nuni da kawancen Iran da kasashe makwabta, BRICS, da kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai, da kuma juriyar al’ummar Iran, za su taimaka wajen shawo kan wannan lamarin.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka September 28, 2025 Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba September 28, 2025 Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Shugaban Argentina ya nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar Sayyid Nasrullah September 27, 2025 Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba. September 27, 2025 Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne September 27, 2025 Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran Dr Ali Larijani Ya Isa Birnin Berut . September 27, 2025 Iran ta kira jakadunta daga Birtaniya, Faransa, da Jamus domin tuntuba September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. (1980-1988).
Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki.
Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100. Sannan sauran gawakin shahidan, wadanda aka ganosu a tsibirin Maimoon da Shalamce, an yi masu jana’iza a lardin Golestan, Qom, Fars, Sistan da Baluchestan, Ardabil, gabacin Azerbaijan da wasu wurare.
Wadannan shahidan sun yi shahada ne a ayyukan farmaki na Kheibar, Karbala-4, Karbala-5, da kuma Valfajr-1.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci