An Biya Falcons Duk Kuɗin Alawus, Kyautar $100,000 Da Gidaje Ga Super Falcons
Published: 15th, August 2025 GMT
Shugaban hukumar kula da wasanni ta ƙasa (NSC), Bukola Olopade, ya ƙaryata rahotannin da ke cewa Super Falcons ba su samu kuɗin alawus ɗin da aka yi musu alƙawari ba, yana mai cewa an riga an biya duk ƴan wasan, sai kaɗan daga cikinsu da ke da matsalar asusun banki. Ya ce ya tabbatar da hakan ne daga shugabar ƙungiyar, Rasheedat Ajibade, da kuma hukumar kwallon ƙafa ta ƙasa (NFF).
Olopade ya ce ba daidai ne a yi iƙirarin cewa ba a biya kuɗin ba, inda ya ƙara da cewa bai kamata a jefa Ajibade cikin matsalar musanta kalaman da ba ta faɗa ba. Ya bayyana cewa waɗanda ke da matsalar asusun banki su kaɗai ba su samu ba, amma sauran duk sun karɓi hakkokinsu.
Gwamna Aiyedatiwa Ya Bai wa Ƴar Super Falcons Tosin Demehin ₦30m Da Gida Sin Ta Dauki Matakan Mayar Da Martani Kan Bankuna Biyu Na EUGame da kyautar $100,000 da gidajen masu ɗakuna uku da Shugaba Bola Tinubu ya yi wa kowacce ƴar wasa bayan lashe kofin WAFCON na 2025, Olopade ya ce gwamnati na kan shirin cika alƙawarin nan da ba da komawa ba. Ya bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da ma’aikatar gidaje da shirin Renewed Hope Homes domin ganin an kammala aikin cikin lokaci.
Ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu tana da tarihin cika alƙawari ga ƴan wasa, inda ya ce ba sa sakaci da batun lada ko shirin tura su gasar ƙasa da ƙasa. A ranar 28 ga Yuli, 2025, Shugaba Tinubu ya karɓi tawagar Super Falcons a Fadar Aso Rock, inda ya sanar da kyautar kuɗi, da gida, da lambar yabo ga kowacce ƴar wasa, lamarin da daga baya ya jawo ce-ce-ku-ce bayan rahoton da aka danganta wa Ajibade.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.
Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an zuwa 50,000.
Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.
Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.
Ƙarin bayani na tafe…