A yanzu haka yankuna da dama wadanda a baya ba su fuskanci kalubalen matsalar tsaro ba, a yanzu haka sun fara dandana ukubar ta’addanci da bakuntar sansanin ‘yan gudun hijira.

Kalubalen tabarbarewar tsaro da kiran da shugaban rundunar tsaro ta Kasa, Janar Christopher Musa ya yi kan ‘yan Nijeriya su dauki matakan kare kai ya haifar da cece- kuce musamman ga galibin jama’a da ke ganin gwamnati ta kasa.

Da yawan jama’a na ganin duk da makuddan kudaden da gwamnati ke kashewa a sha’anin tsaro da kwarewar jami’an sojoji amma ‘yan ta’adda sun rinjaye su har suna ikirarin jama’a su dauki matakan kare kai.

Janar Musa wanda daga baya ya janye kalamansa, tun da farko ya bukaci ‘yan Nijeriya da su samu dubarun kare kai domin ceton rayukan su daga hannun ‘yan ta’adda.

Da yake magana a gidan talabishin na Channels, Musa ya bayyana cewar ya wajaba jama’a su koyi karati da judo baya ga muhimman abubuwa kamar iyo da tuki.

Ya ce ba wai domin kasa na cikin yanayin yaki ba, yana da muhimmanci jama’a su koyi kare kan su, a cewarsa kasashe da dama wajibi ne jama’a su koyi dabarun ceton kai da kai.

Ya ce “A Turai iyo wajibi ne. Haka ma koyo da karatun sha’anin tsaro wajibi ne saboda dole ka fahimci abin da ya shafi tsaro. Abubuwa ne da ko a kasar nan bai kamata mu yi wasa da su ba, duniyar da muke a yanzu ta na cike da hadari, akwai mutanen da ke kisa ba dalili.” Ya bayyana.

Hafsan hafsoshin ya bayyana cewar ya kamata Hukumar Kula da Masu Hidimar Bautar Kasa (NYSC) da su saka horon da ba ba na makami ba a cikin shirin domin matasa su samu horon kare kai a yayin wata barazana.

To sai dai a bisa ga yadda jama’a suka fassara kalaman hafsan hafsoshin kan daukar makami domin kare kai, Janar Musa ya bayyana cewar ba a fahimci kalamansa na batun kare kai ba.

Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaro, Birgediya Janar Tukur Gusau ya bayyana cewar Janar Musa bai taba kiran jama’a da su dauki makami domin kare kai ba, a maimakon hakan ya bukaci ‘yan Nijeriya da su dauki dabi’ar da duniya ta runguma kamar koyon dambe, judo, kokuwa, gudu, iyo a matsayin hanyoyin kare kai a yayin shiga wani kalubale.

Ya ce hafsan hafsoshin bai ce wa al’ummar kasa su tunkari ‘yan ta’adda da makamai ba, kawai yana karfafawa jama’a ne kan daukar matakan kare kai, misali a yayin fada a cikin unguwa ko kwacen waya ta yadda za a iya kare kai ba tare da makami ba.

Gusau ya bayyana cewar daukar makami ba tare da amincewar hukuma ba, haramun ne a dokar kasa kuma duk wanda aka kama da laifin zai fuskanci hukunci.

Hedikwatar tsaron ta bayyana cewar karin bayanin ya zama wajibi domin kawar da sabanin fahimtar jama’a kan kalaman hafsan hafsoshin wadanda wasu suka fassara da cewar yana kira ne da a dauki makami.

A kwanan nan ne dai dan majalisar da ke wakiltar kramar hukumar Funtua a majalisar dokoki ta jihar Katsina, Honarabul Abubakar Muhammad ya rabawa al’ummarsa kyautar bindigogi 50 domin su kare kai daga barayin daji. Ya ce ya ba su bindigogin ne ba domin tashin hankali ba, sai dai domin su taimaka wajen kakkabe ayyukan ta’addanci da ke ci wa al’ummar yankinsa tuwo a kwarya.

 

Sojoji Ba Su Da Kayan Aikin Yakar Ta’addanci – Sanata Ndume

Hare- haren ta’addancin mayakan Boko- Haram a Arewa- Maso- Gabas wanda rahotanni a baya suka nuna cewar ya yi sauki sosai, a yanzu ya sake dawowa da karfi wanda hakan ya sanya al’umma a cikin tsoro da zullumi.

Dan Majalisar Dattawa da ke wakiltar Kuduncin Borno, Sanata Muhammad Ali Ndume ya nuna damuwa da fargabar yadda maharan ke gallazawa al’umma tare da hana su zuwa gona.

A tattanawar Sanata Ndume da BBC Hausa ya ce a baya hankalin al’ummar yankin ya dawo jikin su, suna murnar an samu kwanciyar hankali har jama’a na zuwa gona amma sai kwatsam hare- haren suka dawo murna ta koma ciki. Ya ce maharan sun kashe masu mutum biyar a ranar Asabar.

Ya ce ya wajaba Gwamnatin Tarayya da rundunar soji ta kara tashi tsaye wajen daukar matakan da suka wajaba domin shawo kan kalubalen matsalar tsaro.

Sanatan ya ce duk da cewar matsalar ta yi sauki a baya, amma ya jaddada cewar sojojin Nijeriya ba su da isassun kayan aikin da za su yaki gagarumar matsalar wadda ya ce ya kamata gwamnati ta bayar da fifiko ga tsaron al’umma da kula da walwalar su.

 

Dawowar Hare-hare A Arewa- Maso – Yamma

Jihohin Katsina, Sakkwato da Zamfara na fuskantar tsananin hare- haren ta’addanci daga barayin daji a yankin Arewa tare da rasa rayuka da tilastawa al’umma gudun hijira

A kwanan nan ‘yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a kauyen Unguwan Mantau da ke karamar hukumar Malumfashi da ke jihar Katsina a inda suka kashe masallata, harin da al’ummar gari suka bayyana da ramuwar gayya.

Tuni gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasa rayukan mutane 32 a harin masallacin. Rahotanni sun bayyana cewar ‘yan bindigar sun kai harin ramuwar gayya ne saboda al’ummar garin sun yi masu kwanton bauna sun kashe ‘yan ta’adda da dama kwanaki biyu gabani, kamar yadda Nasir Mu’azu, wani jami’in gwamnati a Katsina ya bayyana.

Malam Ali Isa Pantami, fitaccen malamin addinin musulunci kuma tsohon Ministan Sadarwa ya yi Allah- wadai da harin tare da kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar sun kama ‘yan ta’addar tare da hukunta su tare da kawo karshen aikin asshar mafi muni.

Malamin wanda ya bayyana hakan a shafinsa na soshiyal midiya ya ce makasan na al’ummar da ba su ji ba ba su gani ba, marasa imani ne da suka fi dabbobi barna.

A kwanan nan masu garkuwa da mutane a Zamfara suka yi garkuwa da mutane 35 tare da kashe su duk da biyan kudin fansa kamar yadda wani dan yankin ya bayyanawa BBC.

A Sakkwato baya ga gabascin Sakkwato da ke zaman hedikwatar barayin daji, yankin da gawurtaccen dan ta’adda Bello Turji da mayakansa suka mayar waje mafi hadarin kisa a Arewa, a yanzu haka ayyukan ta’addancin sun ta’azzara a kananan hukumomi da dama a Kuduncin jihar.

Kananan Hukumomin Kebbe, Tambuwal, Shagari da Tureta na cikin wadanda lamarin tsaron ya ta’azara a yankin musamman karamar hukumar Kebbe wadda barayin daji suka kwashe tsayin shekaru suna cin karensu ba babbaka.

 

Zanga- Zanga A Sakkwato

Daruruwan al’umma ne a garuruwa kusan 10 da ‘yan ta’adda suka tarwatsa a Karamar hukumar Shagari suka mamaye titi suka rufe babbar hanyar Shagari, Sakkwato, Birnin Kebbi zuwa Neja suna zanga- zangar neman agajin gaggawa daga gwamnati.

Dimbin mutanen maza da mata a ranar Litinin sun taru a hedikwatar karamar hukumar Shagari suna bayyana halin rai- kwakwai- mutu- kwakwai da suke ciki a hannun ‘yan bindigar da ke yawan kai masu hare- haren da rashin daukar mataki ya tilasta masu fitowa zanga-zangar lumana.

Rahotanni sun tabbatar da harin ‘yan bindiga a kauyukan Asake, Dodo, Tungar Barke, Lungu, Tungar Doruwa, Zango, ‘Yan Yandu, Tungar Na’anza, Jandutse da Ila tare da kashe mutane biyu da garkuwa da mutane 15 lamarin da yasa mutane da yawa suka kauracewa garuruwan.

A hare- haren mayakan sun yi garkuwa da mai garin Rinaye da wasu mutanen da ba a tantance adadin su ba ciki har da Limamai, bayan sun kashe mutane uku a karshen mako

Wata mata, Malama Tumba wadda ta samu tsira daga kauyen Jandutse ta bayyana cewar ta kasa gano ‘ya’yan ta biyar mata uku da maza biyu tun bayan da suka gudu a yayin harin, ta ce suna cikin mawuyacin hali, kuma ba su da abinci, suna son komawa gidajen su amma ba tsaro.

Masu zanga- zangar da suka yi gudun hijira daga garuruwan su sun bukaci gwamnati ta kawo masu agajin gaggawa domin magance matsalar da suke ciki.

Shugaban Karamar Hukumar Shagari, Honarabul Maidawa Kajiji a tattaunawarsa da manema labarai ya bayyana cewar sun fara daukar mataki domin ganin ‘yan gudun hijirar sun koma garuruwan su. Ya ce gwamnati za ta yi iyakar kokari domin samar masu da tsaro.

Haka ma duka a makon jiya ‘yan bindiga sun kai farmaki a garin Jabo da ke karamar hukumar Tambuwal a inda suka kashe mutane biyu suka yi garkuwa da mutane da dama a masarautar wadda ta kwashe tsayin shekaru ta na fama da gawurtacciyar matsalar tsaro, hasalima bayanai sun tabbatar da cewar a yanzu haka akwai sama da mutane dubu daya da ke zaman gudun hjira a Jabo.

Haka ma a karamar hukumar Kebbe, wadda ke kan gaba wajen fsukantar matsalar tsaro a Kudancin Sakkwato, matsalar wadda ta yi sauki a baya a yanzu ta dawo sabuwa. Mafi munin harin da suka kai kwanan nan shine a garin Fakku, inda suka kashe mutane hudu, suka yi garkuwa da wasu.

 

Gwamnati Ke Karfafawa ‘Yan Ta’adda- El- Rufai’i

A kan yadda matsalar tsaro ta ke kwan- gaba kwan- baya, tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El- Rufa’i ya soki Gwamnati da laifin baiwa ‘yan ta’adda damar ci- gaba da aikata ta’asa a sassan kasar nan.

Jigon na jam’iyyar hadaka ta ADC ya ce gwamnati na karfafawa ‘yan ta’adda ta hanyar biyan su alawus a kowane wata, ba su abinci a matsayin wata hanya ta shawo kan matsalar ba tare da makami ba wanda ya ce hakan bai dace ba domin karfafa masu ne matakin da ba zai taba daukar irinsa ba.

El- Rufa’i wanda ya bayyana hakan a shirin Siyasa A Yau na gidan talabishin na Channels ya ce babban matakin shawo kan matsalar tsaro shine a yi wa ‘yan ta’adda magana da yaren da suke ganewa maimakon karfafa masu wanda ya ce shine dalilin da yasa matsalar ta kasa zuwa karshe.

Ya ce matsayarsa ita ce, dan ta’addan da ya tuba shine kawai wanda ba ya raye, don haka kashe su ne kawai mafita, a kone su har sai sun zama babu su, idan ya so kaso biyar din da ake son su tuba za a iya karban tuban su.

Jigon dan adawar ya bayyana cewar ba a karfafawa makiyi, ba a ba shi kudin da zai je ya sayi manyan makamai wanda shine dalilin da ya sa matsalar tsaron ta kasa karewa kuma ba za ta kare ba matukar wannan tsarin ake kai.

Tsohon Gwamnan ya ce gwamnati ba za ta yaudari jama’a ba, iyaka su yi farfaganda, amma wadanda ke rayuwa a Katsina da Zamfara da Kaduna sun san halin da suke ciki.

 

Babu Gaskiya A Kalaman El- Rufai’i – Gwamnatin Tarayya

To sai dai jim kadan da fitar kalaman na El- Rufai’i, Gwamnatin Tarayya ta mayar masa da martani tana cewar ta yi watsi da zargin da ya yi a matsayin maras tushe ballantana makama.

A jawabin da Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara Kan Lamurran Tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya fitar wanda Kakakinsa Zakari Mijinyawa ya saka wa hannu, gwamnatin ta bayyana cewar babu kamshin gaskiya a tattaunawar da El- Rufa’i ya yi na cewar ta na da tsarin biyan kudin fansa tare da tallafi ga ‘yan ta’adda.

Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa ya bayyana cewar zargin ba gaskiya ba ne, domin babu lokacin da ofishin ko gwamnatin Tinubu ta bayar da kudin fansa ko bayar da tallafi ga ‘yan ta’adda, hasalima maimakon hakan sun sha gargadin ‘yan Nijeriya kan illar biyan kudin fansa.

Jawabin ya ce tun kafuwar wannan gwamnatin ta fito da dabarun kawo karshen matsalar ba tare da amfani da makami ba da sanya al’umma a ciki domin kawar da matsalolin da ke faruwa a cikin al’umma.

Gwamnatin ta ce an samu sakamako a wurare kamar Igabi, Birnin-Gwari, Giwa da wani bangare na Kaduna wadanda a baya suka fuskanci ukubar ta’addanci amma yanzu sun samu zaman lafiya.

A cewar gwamnatin kafafen yada labarai suna yada kokarin da jajirtattun jami’an tsaro ke yi domin kamawa da kisan gawurtaccin ‘yan ta’addan. A cewar ta kwanan nan sun samu nasarar kama jagororin kungiyar Ansaru wadanda a baya suka kafa sansani a Kaduna.

Gwamnatin ta ce ba daidai ba ne kuma batanci ne tsohon Gwamnan ya yi ga kokarin da jami’an soji ke yi kan kasa yabawa sadaukar da kai da aiki tukuru da suke yi domin aikin wanzar da zaman lafiya a fadin kasa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: garkuwa da mutane ya bayyana cewar karamar hukumar matsalar tsaro yi garkuwa da yan Nijeriya A yanzu haka gwamnatin ta A kwanan nan Gwamnatin ta barayin daji a yanzu haka yan ta adda

এছাড়াও পড়ুন:

Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda

Sudan ta yi kira ga Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya  da ya sanya rundunar  Rapid Support Forces (RSF) a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda bisa ga ka’idojin yaki da ta’addanci na duniya, sannan ya dauki mataki a kan duk wanda ya yi mu’amala da ita, ko ya samar mata da makamai da sojojin haya, ko jiragen sama marasa matuki, ko kuma kasar da ta bar ta ta tsallaka iyakokinta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a lokacin zaman gaggawa na Kwamitin Tsaro don tattauna yanayin da ake ciki a Sudan, Wakilin dindindin na Sudan a Majalisar Dinkin Duniya, Al-Harith Idris, ya bukaci Majalisar da ta yi Allah wadai da kisan kiyashin da ‘yan bindigar RSF, sojojin haya na kasashen waje, da masu goyon bayanta na yankin suka aikata a El Fasher da kuma sauran wurare a cikin Sudan.

Idris ya yi kira ga Kwamitin Tsaro da ya sanya takunkumi mai tsauri ga dukkan kasashe  da daidaikun mutane da Majalisar ta sani wadanda ke bayar da kudi ga  RSF, samar mata da makamai, ko samar mata da mafaka, sannan a fara bincike kan kisan kiyashin da ake yi wa mazauna El Fasher don ci gaba da kokarin daukar mataki. Ya kara da cewa “‘yan bindiga suna yin barazanar kashe mutane a kullum rana ta Allah.”

Wakilin na Sudan ya yi kira da a tabbatar da an aiwatar da kudurorin Majalisar Tsaro na 2736 da 1591, “kamar yadda shaidu a Darfur suka tabbatar da cewa wasu ƙasashe maƙwabta sun shiga cikin kisan fararen hula don tallafawa ‘yan bindiga.”

Bugu da ƙari, Al-Harith ya yi kira da a goyi bayan taswirar da gwamnatin Sudan ta gabatar wa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta dogara ne akan dakatar da yaƙi na dindindin da kuma kwance damarar makamai na ‘yan bindiga, sannan kuma su mika wuya.

Idris ya fayyace cewa ba za a yi tattaunawa da RSF ba har sai sun ajiye makamansu su kuma sun daina kai hari kan al’ummar Sudan.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu
  • Tinubu Ya Yi Wa Shugabannin Tsaro Ado Da Sabbin Muƙamai
  • Zargin Kisan Kiristoci: ’Yan majalisar Amurka sun yi amfani da bayanai marasa tushe — Gwamnati