E3 sun gindaya sharudda 3 kan dakatar da dawo da takunkuman MDD a kan Iran
Published: 30th, August 2025 GMT
A ranar Juma’a ne Birtaniya da Faransa da Jamus suka gindaya wasu sharudda guda uku ga Iran game da batun dage mayar da takunkumin Majalisar Dinkin Duniya a kanta,a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka fitar gabanin wani taron sirri na kwamitin sulhu na MDD.
Kasashen uku da aka fi sani da E3 sun ce a shirye suke su dage mayar da takunkumin har na tsawon watanni shida idan Tehran ta amince da sake baiwa masu binciken nukiliya na Majalisar Dinkin Duniya damar shiga cibiyoyinta na nukiliya, tare da magance abin da suka kira damuwar da suke da ita game da yawan tataccen sinadarin uranium da ta ke da shi, da kuma shiga tattaunawa da Amurka.
Sabanin haka, jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya yi watsi da tayin na Turai, yana mai bayyana shi a matsayin “mai cike da sharuddan da ba su da ma’ana,” ya kara da cewa “wadannan bukatu kamata ya yi su zama sakamakon shawarwari, ba sharuddan fara shawarwari ba.”
Iravani ya yi nuni da cewa, abin da ake bukata a halin yanzu shi ne goyon baya ga “wani takaitaccen bayani ba tare da wani sharadi ba na tsawaita kudiri mai lamba 2231,” wanda ya kafa harsashin yarjejeniyar nukiliyar ta shekarar 2015, wadda ta tanadi dage takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya da kasashen yamma suka kakabawa Iran.
A daya bangaren kuma, Rasha da China sun gabatar da daftarin kudiri ga kwamitin sulhun, inda suka bukaci da a tsawaita wa’adin kudirin har na tsawon watanni shida, inda suka bukaci dukkanin bangarorin da su koma tattaunawa cikin gaggawa. Sai dai har yanzu kasashen biyu ba su nemi a kada kuri’a a kai ba.
Jakadan na Iran ya bayyana daftarin kudurin na Rasha da China a matsayin wani mataki mai amfani na baiwa diflomasiyya karin lokaci, yana mai cewa zartar da kudurin na bukatar a kalla kuri’u tara, muddin babu daya daga cikin kasashe biyar din din din din din (Birtaniya, Faransa, Amurka, China, da Rasha) da ya yi amfani da hakkin hawa kujerar naki.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka ta hana izinin shiga kasarta ga shugaban Falastinawa don halartar taron MDD August 30, 2025 Rwanda ta dauki bakin haure kashi na farko da aka kora daga Amurka August 30, 2025 Jami’in Sojin Isra’ila: Masu Tunanin Hizbullah Ta Yi Rauni Suna Mafarki Ne August 30, 2025 Mali: Kungiyar Al-Qaeda ta kwace iko da garin Farabougou da ke tsakiyar kasar August 30, 2025 Mutum Guda Ya Yi Shahada Sanadiyar Harin Isra’ila A Kudancin Lebanon August 29, 2025 Malasiya Ta Bukaci A Kori Isara’ila (HKI) Daga MDD August 29, 2025 Iran: China Ta Zuba Jari A Aikin Samar Da Wutar Lantarki Ta Hasken Rana A Bushar August 29, 2025 MDD Ta Yi Tir Da Dirar Mikiyan Da Jamus Takewa Masu Goyon Bayan Falasdinawa August 29, 2025 Majalisar dokokin Iran ta gabatar da kudirin ficewa daga NPT August 29, 2025 Guterres: Dole ne a kawo karshen halin da ake ciki a Gaza August 29, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
HKI Na Ci Gaba Keta Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta A Gaza Inda Take Kashe Falasdinawa
Rahotanni sun bayyana cewa Isra’ila ta kashe wasu falasdinawa guda 5 yankin gaza a ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da suka cimma tsakaninta da kungiyar Hamas a farkon watan oktoba,
A yau juma’a kafar yada labarai ta falasdinu ta bayyana cewa sojojin Isra’ila sun harbe wani bafalasdine a yankin jabaliya dake arewacin yankin Gaza, haka zalika wani bafalasdine mai suna Mahmud suleman al- wadiya sojojin isaraila sun kashe shi a gabashin shuja’iyya dake makwabtaka da gabashin gaza, gari mafi girma a gaza kuma an jikkata wani dan uwansa,
Har ila yau hamdi al-barim da mohamma salem qadi sun ji mummunan rauni sakamakon harin da sojojin Isra’ila suka kai musu a khan yunus dake yammacin gaza a yan kwanakin nan,
Tun daga lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a yankin Gaza zuwa yanzu a shekara ta 2023 sojojin Isra’ila na ci gaba da kai hare – hare a yankuna daban – daban inda akalla sun kashe mutane 1062 tare da jikkata wasu dubbai fiye da 20,000 kuma da suka hada da yara kana 1600 an cafkesu ana tsare da su .
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Tube Yarima Mai Jiran Gado Na Birtaniya Bayan Da Aka Tabbatar Da Laifinsa October 31, 2025 Kasashen Pakistan Da Afghanistan Sun Tsawaita Yarjejeniyar Dakatar Da Bude Wuta October 31, 2025 M D Duniya Tayi Gargadi Game Da Gwajin Nukiliya Da Amurka Ta Sanar Za ta yi October 31, 2025 Sudan Ta Yi Kira Ga Kwamitin Tsaro Da Ya Ayyana RSF A Matsayin Kungiyar ‘Yan Ta’adda October 31, 2025 Araqchi: Gwajin Makaman Nukiliya Na Amurka Babbar Barazana Ce Ga Duniya October 31, 2025 Masar da Eritrea Sun Tattauna Bukatar Tallafawa Kasar Sudan October 31, 2025 Shugaban Lebanon Ya Umarci Sojoji Da Su Fuskanci Kutsen Na Isra’ila A Kudancin Kasar October 31, 2025 Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa October 31, 2025 Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci