Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan Al-Mujtaba (a) 138
Published: 10th, September 2025 GMT
138- Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi.
////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka fara yakin gama gari a Siffin tsakanin rundunar Amirulmumina Aliyu dan Abitalib (a) da kuma rundunar Azzalumai kamar yadda manzon All..(s) ya kirasu, wato rundunar Mu’awiya dan Abusufyan.
Kuma muhimman abubuwan da suka faru a yakin sun hada da cewa, akwai wani lokacin da rundunar Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a) ta tarwatse har ya kaiga ya shiga yaki da kansa, tare da yayansa wadanda suke kareshi. Amma bayan da Malik dan Ashtar ya sami damar sake tattarasu da kuma karfafa giuwarsu da maganganu masu tada hamasa, sannan ya jagorancesu sai da suka dangana da Haimar Mu’awiya dan Abusufyan. Sai da mu’awiya ya fara shirin gudu dafa fagen fama.
Banda haka munji yadda Ammar dan Yasir (a) yayi shahada, inda kafin haka, ya fahinci cewa a wannan yakin ne manzon All..(s) yayi masa al-kawalin cewa zai yi shahada. A lokacin dai Ammar dan Yasir, ® yana dan shekara 90, sannan yaje wajen Imam (a) dan neman izini da kuma bankwana da shi. Imam (a), ya yi bakin ciki da rabuwa da Ammar wanda yake kamar hannun damarsa ne, amma ba makawa, bai da zabi, shiga yaki har zuwa lokacinda ya hadu da Abulghadiya wanda ya kashe shi ya kuma kaishi ga gurinsa na haduwarsa da Ubangijinsa, da kuma riskan yan uwansa wadanda suka rika shi komawa ga All..
Imam Ali (a) ya yi bakin ciki da shahadar Ammar dan Yasir, kuma a lokacinda ya tsaya kan gawarsa, ya bayyana falalolinsa, inda daga ciki ya cewa, ya ga lokacinda idan an ambaci sahabban manzon All..4, Amma shi ne hudunsu, ko an mabaci 5 to chi ne na biyar. A wani wuri ya bayyana cewa babu wani mumini wand aba zai yi bakinciki da shahadar Ammar ba.
Hakama dan Imam Al-Hassan (a) ya tsaya a kan gawarsa inda ya ambaci cewa: Yaji kakansa manzon All..(s) yana cewa, lalle Aljanna tana shaukin mutane uku, Aliyu da Ammar da Salman.
Sannan a lokacinda labarin shahadar Ammat ta yatsu mutanen sham suke rude don hadisin “Ammar, azzaluman kungiya ce zata kasheshi” ya nuna cewa su ne kungiyar, amma dan Ass yace masu ai Aliyu ne ya kashe shi, don shi ya kawo shi yaki.
Daga nan sai Imam (a) ya daga murya yana cewa: Ku ne shamaki na da mashi na! sai mayaka 12, 000 suka tsaya a bayansa da ya tunkari, sojojin Mu’awiya, sai da ya wargazasu gaba daya, sai gashi a gaban haimar Mu’awiya, sai yace masa: Kaiton ka! Ka taho mu yi baga da gaba tsakanimmu da All.., me yasa mutane suke mutuwa a tsakanimmu, ka zo duk wanda ya kashe wani, shugabanci nashi ne.
A lokacinda Amru dan Ass ya ji haka, sai ya tashi ya je wajen mu’awiya, yana ce masa, mutumin ya yi maka adalci, ka fito ku yi mubaraza, sai Mu’awiya ya ce mata, amma baka yi mani adalci ba, ka san cewa ba wanda zai yi mubaraza da shi sai ya kashe shi.
Sai dan Assi yace masa: Ba abinda yafi dacewa da kai sai, mubaraza. Sai yacewa Amr kanason ka shugabanci sham a bayana? Sojojin Iraki sun gama da dukkan rundunonin Mu’awiya ba abinda ya rage masa sai shirin gudu don kada ya shiga hannun Malikul Ashtar.
A nan sai mu’awiya ya kira ministan makircinsa Amru dan Asi, ya nemi shawararsa kan abinda za’a yi, don ga dukkan alamu rundunar Iraki ta fi karfinsu a yaki. Dana nan zuwa gobe zasu gama da su.
Sai Amru dan Assi ya ce masa: Ni ina ganin, mutanen suna yaki bisa wata manufa, wato neman mulki, a yayinda mutanensu na yaki domin neman yardar All…
Sannan mutanen Iraki sun jin tsoroka idan ka sami iko a kansu, amma mutanen sham basa jin tsorin Ali, idan ya sami nasara akanka don suna da labarin cewa bayan yakin Basra ya yi amfawa ga duk wadanda suka saba mashi ko suka yake shi).
Daga nan sai Amru dan Asi ya bashi shawara ya kirasu zuwa wani abu idan sun amince sabani zai shiga tsakaninsu, idan sun ki amincewa har yanzun sabani zai shiga cikinsu, kuma shi ne kirasu zuwa alkur’ani mai girma a matsayin hukunci a tsakaninsu.
Mu’awiya ya yi tunani, ya ga cewa dabarace mai kyau, sai ya amince da shi. Amru bin Asi yace wannan dabarar na ajiye maka shi ne don lokacin bukata a wannan. Daga nan sai mu’awiya ya bada unurni ga mayakansa su dauki mushafin alkur’ani su daga a saba sannan su fada da babban murya kan cewa wannan ya shiga tsakaninsun. Malaman tarihi sun bayyana cewa, mutum fiye da 500 suka daga mushafi suna fada da babban murya kan cewa shi ne zai shiga tsakaninsu.
Suna cewa da murya guda (ga wannan littafin All..tsakanimmu da ku, daga fatiharsa zuwa karshensa. Wa zai kula da kan iyakokin sham in banda mutanen sham,? Wa zai kula da kan iyakokin Iraki in ba mutanen Iraki ba. Wa zai yi jihadi da rumawa,? Wa zai yaki turkawa, wa zai yaki kafirai.
Hakika sun daga mushafi don makirce da kuma kubutar da kansu. Lalle, babu shakka basu yi Imani da mushafi ba. Sun dai yi amfani da shi don hana a zubar da jininsu a kuma sami nasara a kansu. Banda haka babu ruwansu da makoman musulunci da musulmi. Kama basa kaunar dauka darajar All.. da hakan. Abin za zai biyo baya zai tabbatar da hakan.
Lalle, babu wata musiba da fitina da tafi fitinar daga Mushafi a tarihin dana dam, don daga mushafi ya sauya hankalin mutanen kasar Iraki, jahilai, wadanda aka zubar da jininsu, mai yawa a siffin, kuma har suka ga kofar nasara, amma sai suka juya suna sabawa shugabansu a fila, suka daina biyayya a gareshi , banda haka suna maida shi makiyi, suna barazanar zasu kasheshi kamar yadda suka kashe Uthman.
Abin bakin ciki mata ta sami rinjaye a kan gaskiya da Kalmar gaskiya wacce ake nufin bata da ita.
Sai gashi dubban mutanen Iraki sun zagaye Imam Ali (a) suna daga murya suna maimaita bukatar Mu’awiya, (hakika mu’awiya ya kiraka zuwa gaskiya, ya na kiranka zuwa littafin All..ka karbi kirinsa, )
Abin mamaki, daga cikin wadan suke wannan kiran har da Ashash dan Kai Alkindi, daya daga cikin kwamandojin, Imam Ali (a) a wannan yakin kuma shugaban kabilar kinda da Rabee, wannan yana nuna cewa akwai makirci babba a cikinsa, (mai yuwa mu’awiya sun bashi cin hanci don yayi hakan, a matsayinda na shugaban mutane masu yawa a kasar ta Iraki.
A lokacinda Imam ya ga cewa shi ne ke jagorantarsu sai ya ce ya creshi daga shugabancin wadannan kabilu, ya mayarwa Hassan dan Mahduj, wasu sun yi magana da Imam kada ya cireshi, ko kuma ya maida shi, amma ya ki. Wannan ya kara fusata Kais wanda tun lokacin yake neman ya dauki fansa kan Imam (a).
Banda haka, ko way a sancewa Kais dan Ashash al-kindi ba wawa bane, ta yadda za’a ce Mu’awiya ya yaudare shi, sai dai idan abinda suka yi masa, na alkawali ko kudade ko dai wani abu dangane da matsayin da ya dauka na bayyana tawaye wa Imam Ali (a) a lokaci guda tare da mutanensa.
Sai Kais dan Ash’ash Alkindi yaje wajen Mu’awiya yana fada masa a gaban Jami’a .don me kuka daga wadan nan mushafi? Sai Mu’awiya y ace masa don ni da ku mu koma cikin abinda ya umurce mu da shi. Ku aiki mutum wanda kuka yarda da shi, a cikinku, mu ma mu zabi wani da muka amince da ci ya wakilcemu sais u yi huklunci da alkur’ani a tsakanimmu.
Sai ya dawo yana fadawa Imam Ali (a) da sauran mutane kan cewa, mu’awiya yana son hukunci da al-kur’ani . Mafi yawan malamai suna ganin Mu’awiya ya bashi kudade don yayi haka, kuma don ya gano cewa baya daswa da Imam Ali (a).
Don haka shi ne ya takurawa Imam Ali(a), Imam ya ki amincewa, ya dage kan hakan .
Daga nan sai Imam (a) ya gay a dace ya yi masu bayani kan cewa waye Mu’awiya, sai ya ce:
{Bayin All! Ni nafi cancanta a kirbi kirata zuwa littafin All.., Amma Mu’awiya da amru dan Assi da kuke gani, da kuma dan Abu Mu’eed, da Habibu dan Maslamah, da dan Abusarkh, ba mutanen addini bane, ko kuma alkur’ani ba, ni na fiku saninsu, na kasance tare su suna yara, da kuma bayan sun girma, sun kasashe mafi munin yara, kuma mafi munin mazaje, Lalle Kalmar gaskiya ce amma ana nufin bata da ita, lalle sun santa amma basa aiki da ita. Basu daga ta ba sai din yaudara da kuma kaidi, ku bani aron kunnuwanku da kwakwalenku na dan lokaci, gaskiya ta kai mayankarta, ba abinda ya rage in banda ya yanke wutsiyar wanda suka kasance azzalumai}.
Amma wadannan basu bashi aron kunnuwansu da hankalinsu kamar yadda ya fada ba, don haka, mutane kimani 12,000 daga cikinsu bayan wannan jawabin, sun bayyana masa cewa : Ya Aliyu, ka karbi kiran wadan nan mutane ga littafin All..idan kana kira zuwa gareshi, idan baka yi ba, zamu kasheka kamar yadda muka kashe uthman, wallah idan bakayi haka ba sai mun aikata
Sai ya amsa masu
{Kaitonku, ni ne na farko da yayi kira zuwa littafin All..kuma nine na farko da ya amsa kira zuwa gareshi, don haka baya halatta a gareni, kuma bai dace da ni ba, a kirani zuwa gareshi ban karba ba, Kuma lalle ni ina yakarsu ne don yi addini da hukuncin littafin All..kuma lalle su, sun sabawa All..a cikin abinda ya umurcesu, sun karya al-kawalinsa, sun yi watsi da littafin All..sai dai ni ina fada muku makirci suka yi maku. Lalle sub a aiki da al-kur’ani suke so ba}.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu, wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi Ya Isa Kasar Tunisiya A Wata Ziyarar Aiki Da Ya Kai. September 10, 2025 Babu Gaggawa Na Fara cire Haraji Kashi 5 Na Man Fetur A Nijeriya September 10, 2025 Da Alama Nijeriya Ta Rasa Tikitin Kai Tsaye Na Zuwa Gasar Kofin Duniya September 10, 2025 Iran Da Hukumar IAEA Sun Fahimci Juna Kan Shirinta Na Nukiliya . September 10, 2025 Harin Isra’ila A Qatar ya kalubalanci Grantin Tsaron Amurka September 10, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Bayar Da Izinin Aikewa Da Wani Kaso Na Khumusi Ga Falasdinawa September 10, 2025 Pezeshkian: Dole Kasashen Musulmi Da Na Larabawa Su Fito Fili Su Yi Allah Wadai Da Harin Isra’ila Kan Qatar September 10, 2025 Araqchi: Hanya Daya Tilo Ta Kalubalantar Isra’ila Ita Ce Hadin Kai Tsakanin Kasashen Musulmi September 10, 2025 Kasar Iran Ta Ce; Ta’addancin Isra’ila Kan Qatar Laifi Ne Da Ke Barazana Ga Tsaro Da Zaman Lafiya September 10, 2025 Farkon Martanin Gwamnatin Siriya Kan Tofin Allah Tsinen Harin Da Isra’ila Ta Kai Kan Yankunan Kasarta September 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sai mu awiya sai Mu awiya masu sauraro wadanda suka Sai Mu awiya kamar yadda Mu awiya ya mu awiya ya
এছাড়াও পড়ুন:
Peter Obi ya kai wa Obasanjo ziyara
Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027.
Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya.
An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wutaA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja, wanda aka naɗa a matsayin Olubadan, da kuma jaddada muhimmancin Ibadan a siyasa, zamantakewa, da tattalin arzikin ƙasar.
“Na kai ziyara don girmama sabon Olubadan, Rashidi Ladoja, wanda ƙwarewarsa a matsayin tsohon sanata, gwamna, kuma attajiri za ta taimaka wajen ɗaga martabar Ibadan,” in ji Obi.
Ya ƙara da cewa tattaunawarsa da Obasanjo da Ladoja na da nasaba da ci gaban Najeriya da kuma shugabanci da ke da burin sauya al’umma ta fuskar gaskiya da adalci.
Ziyarar Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da shirye-shiryen siyasa gabanin babban zaɓen shekarar 2027, inda ake hasashen zai sake tsayawa takarar shugaban ƙasa.