Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki
Published: 11th, September 2025 GMT
Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Sanin Makamar Aiki ta Najeriya (NARD), ta bai wa Gwamnatin Tarayya sa’o’i 24 don ɗaukar mataki game da buƙatunsu, ko kuma su tsunduma yajin aiki.
Wannan matakin ya biyo bayan cikar wa’adin gargaɗin kwanaki 10 da suka bayar a baya.
Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da shugabannin Ansaru 2 a kotu Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinciTuni wasu likitoci a Abuja da Jihar Oyo suka tsunduma yajin aiki.
Likitocin, waɗanda yawancinsu ke aiki a Asibitocin Koyarwa da na Ƙwararru, suna yawan tafiya yajin aiki saboda rashin biyan wasu haƙƙoƙinsu.
A halin yanzu, suna neman a biya su kuɗin horon 2025 da bashin albashin da suka bi, sannan sun buƙaci a hanzarta biyansu wani kuɗaɗen alawus-alawus.
Hakazalika, sun buƙaci gwamnati ta amince da takardar shaidar digiri ta ‘West African postgraduate’, sannan a magance matsalolin da suka shafi walwalarsu a Jihar Kaduna da kuma Asibitin Koyarwa na LAUTECH, da ke Ogbomoso.
Shugaban NARD, Dokta Tope Osundara, ya ce wannan mataki da suka ɗauka ya biyo bayan taron awanni shida na kwamitin gudanarwa na ƙasa da suka gudanar ta Intanet.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta yi alƙawarin ɗaukar mataki game da buƙatunsu amma dole ne a hanzarta aiwatar da su.
Ya yi gargaɗin cewa idan gwamnati ba ta yi wani abu a kan buƙatun nasu ba, za su fara yajin aiki a ranar Juma’a.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya wa adi Yajin aiki
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
A daidaikun kasuwannin Abuja da wasu manyan birane na ƙasar nan, an bayyana yadda farashin doya ke ƙara hawa fiye da yadda ake tsammani.
Wannan na faruwa ne duk da cewa yanzu sabuwar doya ta fara shigowa kasuwa, bisa al’ada, a duk shekara fitowar sabuwar doya kan karya farashin wanda yake kasuwa. Sai dai a bana, wasu daililai na sa farashin doya kara hawa.
NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Ukuwannan shine batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba akai.
Domin sauke shirin, latsa nan