Larijani: Iran za ta katse hadin gwiwa da IAEA idan aka dawo mata da takunkuman MDD
Published: 26th, September 2025 GMT
Sakataren Majalisar Koli ta Tsaron kasar Iran ya bayyana cewa, Tehran za ta katse yarjejeniyarta da take yi da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA, tare da daina bada hadin kai ga binciken makamai na kasa da kasa, idan har aka aiwatar da tsarin “sake dawo mata da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya.
Sakataren Majalisar ta Iran Ali Larijani ya sake nanata kudurin Iran na cewa ba da ta niyyar yin amfani da makamin nukiliya – ko dai a yanzu ko a nan gaba.
Ya kuma ce ayyukan wuce gona da iri da Amurka da Isra’ila suka yi kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku a watan Yuni ya sanya tattaunawar ta zama “bazara”.
Yau Juma’a ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke zama domin kada kuri’a kan kudurin da Rasha da China suka gabatar na dage batun sake kakaba takunkuman na MDD kan Iran.
Idan kwamitin ya gaza amincewa da kudurin, Majalisar Dinkin Duniya za ta kakabawa Iran takunkumi a gobe Asabar.
A cikin tattaunawar da akayi da shi, Larijani ya ce, “Mun bi duk wata hanya da hanyoyin da aka tanada domin magance wannan rikici cikin lumana.”
Ya kuma gargadi shugaba Donald Trump na Amurka cewa Iran ba za ta taba mika wuya ba idan har aka kai wasu sabbin hare-hare.
Dama kafin hakan Ministan harkokin wajen Iran Abbas Agarachi ya yi gargadin cewa Iran za ta yi watsi da yarjejeniyar da ta kulla ta barin jami’an MDD masu sanya ido kan nukiliya su duba cibiyoyinta, matukar kasashen Yamma suka sake kakaba mata takunkumi.
Hukumar kula da makamashin nukiliya ta Duniya na ta kokarin ganin ta gyara alakarta da Iran domin komawa kan aikin sanya ido kan shirin nukiliya na kasar, tun bayan harin da Isra’ila da Amurka suka kai kan cibiyoyin sarrafa makamashin nukiliyarta a watan Yuli.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyar $ biliyan 25 don gina tashoshin makamashin nukiliya September 26, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci ya Jaddada Cewa: Mallakar Makamashin Nukiliya Hakkin Iran September 26, 2025 Pezeshkian: Martanin Iran Zai Yi Daidai Da Sabon Halin Da Ake Ciki Kan Shirinta Na Makamashin Nukiliya September 26, 2025 Kasashen Rasha Da China Sun Bukaci A Jinkirta Batun Maido Da Takunkumi Kan Kasar Iran September 26, 2025 Magajin Garin Landan Ya Yi Dirar Mikiya Kan Shugaban Kasar Amurka Donald Trump September 26, 2025 Sojojin Yemen Sun Kai Wani Gagarumin Hari Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila September 26, 2025 Iran ta yi Allah wadai da yunkurin E3 na neman sake dawo mata da takunkumi September 26, 2025 Maduro jaddada hadin kai tsakanin al’ummomin Venezuela da Colombia September 26, 2025 UNRWA: Halin da ake ciki a Gaza ya yi muni matuka September 26, 2025 Sojojin Yaman: Mun kai hari kan sojojin mamaya a Jaffa September 26, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta
Kasar Yemen ta gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan fuskantar hare-hare masu zafi idan har ta karya yarjejeniyar Gaza
A ranar Lahadin da ta gabata, Hazam al-Assad, mamba a ofishin siyasa na kungiyar Ansarullahi ta Yemen, ya gargadi gwamnatin mamayar Isra’ila kan karin fuskantar hare-hare masu zafi idan ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza.
A wata sanarwa da ya fitar ta hanyar gidan radiyo Sputnik ta kasar Rasha, Hazam al-Assad ya tabbatar da cewa: Yemen za ta dakatar da kai hare-hare kan gwamnatin mamayar Isra’ila, idan har ta yi aiki da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza.
Tun da farko dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila da kungiyar Hamas sun rattaba hannu kan matakin farko na shirinsa na zaman lafiya.
A nata bangaren, Kungiyar Hamas ta sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta a zirin Gaza, wadda ta hada da shigar da kayan agaji da musayar fursunoni. Ta yi kira ga shugaban kasar Amurka Donald Trump da kasashen da suka amince da yarjejeniyar, da kuma kasashen Larabawa, da na Musulunci, da na kasa da kasa, da su tilastawa haramtacciyar kasar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar gaba daya.
A yau litinin ne za a gudanar da shawarwarin a Sharm el-Sheikh a birnin Alkahira, tare da halartar shugaban Amurka Donald Trump da kasashe masu shiga tsakani, domin kafa dukkanin sharuddan da suka dace domin samun nasara da kuma ci gaba da aiwatar da shirin, wanda bangarorin Falasdinu da gwamnatin mamayar Isra’ila suka amince da shi.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 An Gudanar Da Taron ‘Farkawar Musulmi’ A Nan Tahren Inda Aka Tattauna Batun Falasdinu October 12, 2025 Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci