Leadership News Hausa:
2025-09-18@00:39:13 GMT

“Hadin Kan Kasashen BRICS” Ya Karfafa Shawo Kan Kalubale

Published: 10th, September 2025 GMT

“Hadin Kan Kasashen BRICS” Ya Karfafa Shawo Kan Kalubale

A halin yanzu, sauye-sauyen da ba a taba ganin irinsu ba a cikin karni guda suna ci gaba da habaka cikin sauri, yayin da mulkin kama-karya, son kai, da kuma kariyar tattalin arziki suka kara yawaita. A wannan yanayi, a wajen taron yanar gizo na shugabannin kasashen BRICS da aka gudanar a ran 8 ga watan nan da muka ciki, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da shawarwari uku don karfafa “hadin kan kasashen BRICS” da kuma kafa kyakkyawar makomar bil’adama ta bai daya.

Wato na farko nacewa ga kasancewar mabambantan bangarori a duniya. Bugu da kari, a kare adalcin duniya domin ci gaba da bude kasuwanci don samun nasara ga kowa, da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya. Sannan a karfafa hadin kai don habaka ci gaban juna.

Wadannan shawarwari uku ba kawai sun nuna sabbin ayyuka da aikin da ke gaban kasashen BRICS ba, har ma sun ba da hanyoyin habaka ingancin hadin kan BRICS, ta yadda za ta zama karfi na farko a cikin sauye-sauyen tsarin daidaita harkokin duniya. A matsayin babbar kungiyar kasashe masu tasowa, tsarin hadin gwiwar BRICS tun daga shekarar 2006 ya ba da fa’ida ga kasashe masu tasowa, kuma ya zama karfi mai kwazo, daidaito, da kyautatawa a harkokin duniya.

Kasancewar mabambantan bangarori a duniya shi ne tushen zaman lafiya da ci gaba. Game da wasu kasashe dake amfani da kasuwanci a matsayin makamin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu, Sin ta ba da shawarar ci gaba da bude kofa da cin moriya tare da kuma kiyaye tsarin tattalin arzikin duniya. Wannan ya sami amincewar shugabannin da suka halarci taron, kuma ya ba da karin tabbaci ga al’ummar duniya. Daga taron tattaunawa kan zuba jari na kasa da kasa na Sin (CIFIT) da taron hada-hadar ba da hidima (CIFTIS), har zuwa bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin daga ketare (CIIE) da za a gudanar a watan Nuwamba, Sin ta dauki hakikanin matakai don raba damammaki da samun nasara ta hanyar bude kofarta ga kasashen BRICS, da kuma inganta tattalin arzikin duniya mai bude kofa, don bai wa kasashe masu tasowa karin damammaki shiga cikin hadin gwiwar duniya da raba sakamakon ci gaba yadda ya kamata.

Dabara ta rage ga mai shiga rijiya, dole ne a inganta harkokin cikin gida ta yadda za a iya shawo kan kalubalen waje da kyau. A nan gaba, hadin gwiwar BRICS zai samar da karin sakamako a fannonin kasuwanci, kudi, da fasaha, don kara karfafa tushen “hadin kan kasashen BRICS,” da kara karfi da tasirinsa baki daya. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya

Babban sakataren MDD António Guterres, ya bayyana a jiya Talata cewa, jerin shawarwarin da Sin ta gabatar wato shawarar raya duniya, shawarar tabbatar da tsaron duniya, shawarar raya wayewar kan al’ummun duniya, da kuma jagorantar harkokin duniya, sun dace da ka’idar kundin tsarin MDD.

Guterres ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a wani taron manema labarai da aka yi a ranar. Ya ce shawarwarin da Sin ta gabatar sun mutunta manufar kasancewar bangarori da dama, kuma sun goyi bayan MDD a matsayin cibiyar hadin gwiwar kasa da kasa, tare da dukufa kan inganta hadin gwiwa tsakanin kasashe daban daban da warware rikice-rikice cikin lumana.

Guterres ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar rarrabuwar kawuna a fagen siyasa ta duniya da kuma karuwar yaduwar rikice-rikice, da ma rashin hukunta masu laifi. Bugu da kari, sabbin fasahohi suna ci gaba da bullowa “ba tare da bin wani tsari ba”, yayin da rashin daidaito ke kara tsananta. A wannan yanayi, babban taro karo na 80 na MDD mai tsawon mako guda da za a fara a mako mai zuwa, zai ba da duk wata dama ga tattaunawa da shiga tsakani.(Amina Xu)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Guterres: Jerin Shawarwarin Da Sin Ta Gabatar Sun Cika Ka’idar Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya
  • Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza
  • Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
  • Shawarar Inganta Jagorancin Duniya Ta Haifar Da Damar Wanzar Da Daidaito Da Adalci
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya tare da kiyaye hadin kai
  • Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Yanke Hutu, Zai Dawo Abuja Gobe Talata
  • Sabunta Cinikin Ba Da Hidima, Masu Zuba Jari Na Waje Suna Ganin “Damar Da Kowa Ke Bukata A Kowane Lungu Na Sin”
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
  • Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar