Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 135
Published: 31st, August 2025 GMT
135-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma, ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin Dastane, Rastan na Aya. Shahid Murtada Muttahari, ko kuma cikin littafin Mathnawa na maulana jalaluddin Rumi.
////…Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Hassan Al-mujtapa (a) jikan manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmu da ya gabata, mun bayyana yadda aka yi yaki kan ruwan furat, bayanda sojojin mu’awiya ya hana sojojin Imam (a) shan ruwan Furat. Inda Ash’ash dan Kais Alkindi ya zu wajen Amirul muminina (a) ya fada masa cewa na hana mutane ruwan sha amma takubbammu na hannummu? Sai Imam ya bashi izini ya je ya bude hanyoyin isa zuwa ga ruwan Furat.
Sai aka kwana gari ya waye sai Ash’ash dan kais Al-kindi ya kira mutanen Iraki kimani 12 suka zu suka fafata da mutanen sham, bayan hasarorin da suka yi, na rayuka da dukiyoyi, mutanen sham sun kauce sun kuma barwa mutanen Iraki damar amfani da ruwan kogin furat. Sannan munji cewa Imam Ali (a) ya bar mutanen sham su sha ruwa bayanda suka kaudasu da karfi.
Daga nan Sai Imam (a) ya sake dawowa a kan abinda ya kawoshi siffin, inda ya aiki yan sakonni har biyar zuwa wajen Mu’awiya a lokacin gud don su gamsar da shi kan ya dawo kan hanyar da musulmi suke kai. Ya kuma dai taurine kai. Daga cikinsu akwai Adr dan Khatam Adda’ii, shibthu dan Ribii, da Yaziz dan Kais, Ziyad dab Khasfah.
Ko wannan daga cikin wadannan jakadun sun yi wa mu’awiya magana, inda suka bayyana masa gaskiyar matsayin sa a cikin wannan , al-ummar ta yadda babu ma yadda za’a kwatantanshi da Aliyu dan Abitaliba (a). Banda haka babau wanda bai masa bai’a ba sai mutanen sham.
Bayan da kowa yayi magana, sai ya basu amsa gaba daya, daga cikin maganarsa sai ya sake nanata cewa Aliyu (s) ya kashe Uthman, ko kuma ya tara wadanda suka kashe, uthman. Don haka Imam (a) ya basu wadanda suka kashe uthman su kashesu, sannan a yi maganar bai’a da kuma hada kan musulmi.
Sai daya daga cikinsu ya ce, yanzu idan an baga Ammar dan Yasir ka kashe shi, Mu’awiya zaka kashe shi.
Sai yace me zai hana, ai ba don Uthman ne zai kasheshi ba, zai kasheshi kan Na’ila yentaccen bawan Uthman. Sai suka ce masa ai baka isa ba mazaje suna nan. . sai magana ta kare.
Bayansa Imam Ali(a) ya bi dukkan hanyoyin da yakamata ya bi don kada a zubar da jinin musulmi sai ya shelanta yaki a kan su.
Kuma kamar yadda ya saba ya sheke fara masu dokokin yaki da wadanda suka ce lailaha illahu, na fako yace
{Kada ku fara yaki da su sai sun soma da kansu, dama, godiya ta ta tabbaga ga All..kuna kan Hujja, ku barsu su soma yakin don ku samu karin hujja a kansu, idan kun yakesu kuka sami nasara a kansu kada ku kashe wanda ya juya baya, kada ku karasa wanda aka jiwa rauni, kada ku kwaye al-aura, kada ku yi muthla da wadanda aka kashe masu, idan kun kai ga tentunan tafiyarsu kada ku yaye labulem kada ku shiga wani gida, sai tare da izini. Kada ku dauki wani abu daga cikin dukiyoyinsu sai abinda kuka sami na kayakin yaki, kada ku cutar da mata, ko da sun zageku, kuma sun zagi shuwagabanninku, ko bayin All..daga cikinku, saboda su masu rauni ne a karfi, da rayukansu da hankalinsu. } Wannan kamar yadda ya zo a cikin littafin Waki’atus Siffin SH 266.
Wannan itace Khudubar Imam Ali (a) kafin a fara yakin Siffin, kuma a fili tana nuna irin yadda yake da tausayi, da jinkai hatta ga wadanda suke adawa da shi ko makiyansa.
Daga nan sai ya daura tutoci ya rabasu ga kwamandojinta, sai ya sanya Ammar dan Yasir a matsayin kwamandan sojojinsa masu dawaki, sannan ya sanya Abdullahi dan Badil a matsayin kwamandan wadanda suke kan kafafuwansu. Sannan ya bada tuta ga Hashin Al-mirkal, ya sanya Ash’ash dan Kais Al-kindi kwamandan bangaren dama, sannan Abdullahi dan Abbas a matsayin kwamandan bangaren hagu. Sanna ya kulla tutocin kabilu ya bada su ga fitattu daga cikin su.
Mu’awiya kuma ya bada tukar masu dawaki ga Ubaidullahi dan Umar, sannan Muslimu dan Ukabah Al-murri , sannan ya santa Abdullahi dan Amru dan Assi kwamandan ta dama, sannan Habibu ibnu Muslimul Fakhri da hagu. Sannan ya bawa tuta ga Abdurrahman dan Khalid Dan Walid. Sannan ya santa Dhahhaak dan Kais Akan mutanen Dimask.
Sai wasu kananan rundunoni daga rundunan Imam (a) suna fita su je su sami wasu daga cikin sojojin Mu’awiya suna yakarsu a tsawon rana. Ko kuma bangarensa. Imam bayan son a fara yaki nag aba daya, saboda har zuwa lokacin yana fadar Mu’awiya zai yi nadama ya dawo kan hanyar gaskiya a daina yakin.
Don haka an fara yakin nan da can har zuwa wasu yan kwanaki , sai watan Muharram ya shigo. An haramta yaki a cikin watan a jahiliya da Musulunci. Don haka suka zauna wata guda babu yaki.
Sannan sun kiyaye mutuncin watan, har ya kai ga sukan chakudu da juna, mutanen sham suna tattaunawa da mutanen Iraki, su yi ta jayayya a tsakaninsu da musa, amma babu fada.
Mutanen Iraki suna fadawa mutanen sham kan cewa kuzo kuyi bai’a ga wisiyin manzon All..(s). su kuma mutanen sham su ce masu ku zo ko nemi fansar Uthman. Ana cikin wannan halin har watan ya wuce aka kuma sake dawowa yaki kamar da.
Sannan a wannan halin ne sai Malikul Ashtar Ankha’I, ya lura da tutocin bangarorin biyu, sai yaga cewa, da dama daga cikin tutocin Mu’awiya suna sutocin Mushrikai a zamanin manzon All…(s) sannan tutocin su kuma sune tutocin manzon All…(s). sai ya sakankance, da cewa gaskiya da bata ce a fili.
Don haka ya tashi cikin mutane Iraki yana cewa (( mafi yawan tutocin da suke wajenku sune tutocin da suke tare tare da manzon All..(s). sannan a wajen Mu’awiya kuma akwai turocin da suke tare da Mushrikai, a zamanin manzon All..(s). ba wanda zai yi shakkar yakar wadan nan mutane sai wanda zuciyarsa ta mutu).
Daga nan sai Ammar dan Yasir ya tashi yana bayyanawa musulmi, dangane da waye Mu’awiya. Da kuma hakikanins, (yace: Ya ku musulmi, shin kuna son ganin wanda yayi adawa da All..da manzonsa (s) ya kuma musantasu, sannan ya zalunci musulmi, ya kuma taimakawa mushrikai,? Sannan a lokacinda ya ga All…yake son ya bayyana addininsa ya kuma taimakawa manzonsa, sai ya zo wajen annabi (a) ya musulunta? Wallahi shi yana maraba da abinda yake gani amma ba mai sonshi ba, manzon All..(s) ya yi wafata, wallah mun san shi da adawarda ga musulmi, da kuma sonsa ga mujrimai, kuma ku saurari shi ne Mu’awiya ku la’anceshi All..ya la’ane shi. Ku yake shi, yana daga cikin wadanda suke dushe hasken All..kuma sune bayyananun makiyan All..).
Lalle shi mu’awiya kafin ya musulunta yayi adawa da All..da manzonsa (s). kuma ya zalunci musulmi. Bai musulunta ba sai don tsaron kaifin takubba. Wanda ya riki danginsa. Kuma hakika ya boye shirka da munafurci da kuma tsokanar musulunci da musulmi, a lokacinda ya sami mataimaka, ya yunkura don yakar dan uwan manzon All..(s) kuma kofar Ilminsa.
Ana cikin wannan halin sai Mu’awiya yana son wasa da Imam Hassan Almujtaba(a) sai ya aika masa Ubaidullahi dan Umar ya kwadaitar da shi Khalifanci. Ya yaudare shi ya bar mahaifinsa. Sai Ubaidullahi ya je wajen Imam Hassan (a).
Kafin haka waye Ubaidullahi dan Umar. An haife shi a zamanin manzon All..(s) bai ruwaito hadisi ko guda ba daga manzon All…(s). sannan bayan an kashe mahaifinsa Khalifa na biyu, ya je kashe Hurmuz da Jufaina yayan Abu lulu’a ya kashe babansa. Sai Khalifa Uthman yaki tsaida hakki a kan kashe, dai ai wanda ya kashe mahaifinsa yakamata ya kashe ba yayansa ba. Amma Khalifa Uthman ya kyale ya gabafarta ma, ko kuma yadda wadda wasu suka ce ya biyya diyyar kashesu daga kudansa. Amma Imam Ali (a) ya fada masa cewa a duk lokacinda ya sami iko a kansa sai ya zartar masa da haddin kissan wadanna farisawa yaran Abu lulu’a da ya kashe.
Don haka yaje siffin tare da Mu’awiya , sai wata ranan ya fito a cikin mutane yanan fada kafin a fara yakin, yana cewa Aliyu zai sani a gobe idan mun kara da shi, sao gashi da aka fara yaki a Siffin an kasheshi a yakin.
Don haka idan mun sake dawowa kan maganar inda mu’awiya ya aike shi, ya je ya yaudari Imam Hassan (a) ya fada masa cewa, Mu’awiya zai bashi Kha;ifanci don haka yana son ya bar babansa ya koma bangaren Mu’awiya.
Da ya zo wajen Imam Hassan (a) sai yace masa ina bukatar in yi magana da kai. Sai Imam yace masa, me kakeso?
Babanka ya kashewa quraishawa iyayensu daga farko har karshe, (ya maidasu marayayu).
Sai Imam (a): Haka ne, babane ya maida su marayu amma a kan tafarkin All…sun yi kokarin su sauke tutanta, sai Imam (a) ya fuskancesu ya kuma kashe jabbarai daga cikinsu, ya kawar girman kansu, ya wargaza taronsu, don wannan ne suke kinsa suke kuma adawa da shi. …
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatyhu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 137 August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 136 August 31, 2025 Iran Ta Sami Nasarar A Kan Amurka A Gasar Volleyball Na Kasa Da Kasa August 31, 2025 Rasha Tace: Masu Son Yaki A Turai Suna Zangon Kasa Ga Kokarin Trump Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine August 31, 2025 AU Da WHO Zasu Hada Kai Don Yakar Cutar Kolera A Nahiyar Afirka August 31, 2025 Almashat: Yemen Za Ta Dauki Fansar Jinin Shahidanta A Kan Sahyuniyawa August 31, 2025 Iran ta yi Allawadai da kisan jami’an gwamnatin Yemen da Isra’ila ta yi August 31, 2025 Yemen: Firayi Ministan da wasu ministoci sun yi shahada a wani harin Isra’ila August 31, 2025 Argentina: Lauyoyi sun bukaci a cafke Netanyahu a kan laifukan yaki August 31, 2025 Sudan: Hamedti ya yi rantsuwar shugabantar gwamnati mai kishiyantar gwamnatin kasar August 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mutanen Iraki wadanda suka masu sauraro a fara yaki
এছাড়াও পড়ুন:
Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar Sin ya gudanar da taron manema labarai da misalin karfe 10 na safiyar yau Litinin, inda kakakin hukumar kididdiga ta kasar, kuma babban masanin tattalin arziki, kana daraktan sashen kididdigar tattalin arziki na kasar, Fu Linghui ya yi karin haske kan ayyukan tattalin arzikin kasar cikin watan Agustan bana, tare da amsa tambayoyin manema labarai.
A cewar bayanan da aka gabatar a yayin taron, ayyukan tattalin arzikin kasar a watan Agusta sun samu ci gaba ba tare da tangarda ba. Kuma hakan ya bayyana ne ta hanyoyi daban-daban kamar haka: masana’antu sun habaka cikin sauri, masana’antar kera kayayyakin aiki da masana’antar fasaha sun samu ci gaba mai kyau. Kana ayyukan bayar da hidima su ma sun bunkasa cikin sauri. Baya ga haka, an samu ci gaba mai kyau a bangaren bayar da hidimomi na zamani. Harkokin kasuwanci sun samu ci gaba cikin natsuwa, inda harkokin sayar da kayayyaki ga masu sayayya suka kara habaka. Har ila yau, kadarorin jari sun ci gaba da karuwa, jarin masana’antu ya habaka cikin sauri, harkokin fice da shigen kayayyaki sun ci gaba da girma, tsarin kasuwanci ya ci gaba da ingantuwa, kana yanayin samar da guraben aikin yi, ya kasance kan wani mataki mai daidaito. Sai dai kuma saboda yanayin da ake ciki, adadin marasa aikin yi a birane ya karu, ma’aunin Core CPI ya ci gaba da hauhawa, kana faduwar farashin kayayyakin masana’antu ya ragu.
Bayanan sun kara da cewa, akwai bukatar lura da cewa, ana fuskantar yanayin rashin tabbas a waje, kuma tattalin arzikin kasar Sin yana fuskantar kalubale da hadari da yawa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp