Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 130
Published: 13th, August 2025 GMT
130-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shirin wanda yake kawo maku kissoshi wadanda suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafai wadanda suka hada da littafin Dastane Rastantan na Aya. Shaheed Murtadan Muttahary ko kuma cikin littafin mathnawi na Maulana Jalaluddeen Rumi ko kuma cikin wasu littafan, da fatan masu sauraro za su kasashence tare da mu a cikin shirimmu na yau.
///… Madallah, masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata a kuma cikin sirar Imam Al-Hassan Al-Mutaba, (a) dan Fatima (s) diyar manzon All..(s) da muke kawo maku, a cikin shirimmun da ya gabata mun bayyana yadda Amirulmuminina Aliyu dan Abitalib (a) ya maida Aisha matar manzon All..(s) daga Basra zuwa madina a cikin mutunci da daukaka, sannan ko ita bata san wadanda suke tare da ita a ayarin ba, sai da suka isa Madina. Wannan bayan nasaranda ya samu a kanta a yakin da ita da zubaira da Talha suna jagoranta. Da kuma kariyar da suka kaga, suka kuma dora masa na cewa shi ya kashe Khalifa Uthman. Sun yi sanadiyyar kissan musulmi kimani 10,000 a kan karya. Banda haka sun budewa wasu shaidanun hanya ta yakar Amirul muminina (a) da wannan dalilin na wai shi ya kashe Khalifa Uthman.
Wanda kamar yadda zamu gani, wannan kofar da suka bude sai da ta zama kofar musibu ga al-ummar musulmi har zuwa yau fiye da shekaru 1,400 da faruwar musibar, ya haddasa rarraba tsakanin musulmi. Sune suka sabbaba zuwan Banu umayya kan kujerar Khalifanci, sannan abbasiyawa daga baya, sannan daga karshe kujerar khalifanci ta fice daga hannun larabawa gaba daya ta koma hannan turkawa. Sai kuma daga karshe, kafirai suka mamayesu suka yiwa mafi yawan kasashen duniya mulkin mallaka, kafirai suka yi watanda da kasashen musulmi a tsakaninsu, wanda har yau sun kasa kwato knasu daga wadannan kafifirai. Sun zama kaskastattu a duniya suna daukan umurni daga kafirai, ba abinda suka iya. Duk wannan sakamakon yakin Jamal da siffin da zamu fara maganarsa a yau.
Daga karshen mun bayyana cewa malaman addinin sunna da shi’a sun gamu a kan cewa dukkanin yake, yaken Aliyu da Abitalib (a), bayan manzon All..(s) shi ne gaskiya.
Yakin siffin shi ne yaki na biyu wanda Amirul muminina (a) Aliyu dan Abitalib (a) ya shiga tare da Mu’awiyya dan abisufyan. Shi ma da sunan yana neman fansar jin Khalifa Uthman kan Aliyu dan Abitalib ko kan wadanda suke tare da shi.
Don haka da farko bayan anyiwa Imam Aliyu (a) bai’a, ya fitar da umurninsa na sauke dukkan gwamnonin Khalifa Uthman a sauran birane da yankunan musulmi, daga cikin har da Mu’awiya dan Abusufyan a sham. Sannan mu’awiya ya san cewa Imam ba zai barshi kan kujerar gwamnan a sham yayi ta kashe dukiyoyin mutane kamar yadda yaga dama ba, ya kuma san ba zai bar mashi dukiyoyin da ya tare da kimani shekaru 20 da yayi yana kan wannan kujerar. Don haka ya zabi yin tawaye, amma da wani hujja, shi ne ba abinda yafi sauki kamar ya fadawa mutanen sham, Aliyu (a) ne ya kashe Khalifa Uthman, kamar yadda su Aisha da Talha da Zubair suka yi.
Don abinda ya faru shi ne, wani wanda ake kiransa Numan dan Bashir ya dauki rugar da aka kashe Khalifa Uthman a cikinta, ya kaita sham, inda Mu’awiya ya sami kan mutanen sham da ganinta. Sun kewayeta suna kuka.
Amma kafin ya shrya ya fita zuwa sham, dan karamin wuri, idan an kwatanta da fadin kasar yake iko da shi, wato daga wasu yankunan kasar Iran har zuwa Yemen a kudu Kenan, sannan ta yamma kuma har zuwa kasar Masar.
Don haka kasar sham karamar kasashe, a lokaci guda zai gama ta ita, amma ana cikin wannan halin sai ya ji su Aisha sun kwace Basra, shi ne sai ya maida hankalisa zuwa Basra har ya sami nasara a kansu.
Don haka ya sake komawa kan Sham, inda mu’awiya ya tare mutane da dama, don yakar Imam (a).
Kafin haka a lokacinda Imam ya bayyana tube shi daga kan kujerar shugabancin sham, ya rubuta masa wasika inda ya bukaci, ya barshi kan kujerarsa, ko kuma ya sauya masa wuri zuwa Masar. Imam yaki amincewa. Don yana son tabbatar da adalci ne, wanda aka rasa a baya, don haka ba zai nemi taimakon azzalumi don kawo adalci ba.
Don haka ne suka shelanta yaki kan Imam Aliyu (A) don masalaharsu ta kansu. Kafin haka a cikin shekaru kimani 20 da yayi yana iko da sham , mu’awiya ya fara tanadin zama a kasar Sham, zaman a din-din din, saboda ya tara kudi yana kuma baje ikonsa yadda ya ga dama a zamanin khalifofin da suka gabata, Ya sayi flaye da gidaje da dukiyoyi masu yawa. Sannan ya sayi mataimakansa da dimbin kudaden da suke hannunsa. Harma yana ganin cewa zai mutu ya gadadar da mulkin sham zuwa yayansa.
Sannan a wani bangare kuma, fitar Aisha kan Amirul muminina (a) ya karfafa Mu’awiya wajen fita don yakar Amirul muminina (a). Sun bude masa kofar fita kan sa, (a) saboda yakarsa da suka yi a Basra. Don haka yakin siffin ci gaba ne da yakin Jamal, don suma sun fita da shi’arin neman jinin Khalifa Uthman, al-hali su suka kashe shi.
Har’ila yau muna iya cewa, wasikar da muhammada dan Abubakar ya rubutawa mu’awiya dan Abusufyan, da kuma maida martanin da yayi masa a wata wasikar sun kara karfafashi na yakar Imam (a). Inda ya ci mu’awiya yana fada masa cewa (Babankan da farukunsa ne suka fara kwacewa Aliyu(a) hakkinsa, suka kuma saba masa a cikin al-amarinsa kan wannan suka hadu suka kuma gamu, sannan suka kirashi zuwa bai’a garesu, sai ya ki zuwa, ya yi baya daga karesu, sun kuma kudurin abubuwa da ama a kansa, kuma sun su yi masa wani abu babban, sannan aga baya, yai masu bai’a ya kuma sallama masau), a cikin shirye-shiryemmu na baya mun bayyana cewa wasu malamai suna ganin bai yi wa Abubakar bai’a ba,-amma duk da haka basu bashi wani aiki ko kuma sanyasu a cikin al-amuransu ba, basa bayyana masa sirrinsu har zuwa lokacinda All..ya dauki rayukansu……).
A wani wuri yana cewa (..idan abinda muke kai a yau dai-dai ne, babanka ne ya zalunce shi mu dai mun bishi ne daga baya, idan ba don abinda babanka ya yi tun farko ba, da bamu sabawa dan Abitalib ba, da mun sallama masa, sai dai munga babanka, ya yi haka da shi, sai muka karba daga wajensa..) Muruju Azzahab. 3/12.
A cikin wannan wasikar ya bayyana, al-amura masu muhimmancin gaskiye, na cewa idan ba don Abinda Khalifa na farko da kuma khalifa na biyu suka yi da Aliyu )a) ba da Mu’awiya bai isa ya yake shi ba. Sai dai ya bi sawunsu ne. Ya bi hanyarsu ne, ya zalunci Aliyu dan Abitalib (a). a kafin da kuma bayan yaki a rikita masa sojojinsa ya barshi da bakinciki har ya kaiga yana burun mutuwa a kan rayuwa cikinsu.
Sannan mun yi maganar cewa dalilin da Mu’awiya yake kawowa na yakar Imam Ali (a) sun hada da cewa yana neman fansar jinin Khalifa Uthman. Mu’awiya yayi amfani da neman jinin Khalifa Uthman don jawo hankalin mutanen sham su goya masa baya, sannan yayi amfani da shi don cusa kiyayyar Aliyu (a) a cikin zukatan mutanen sham, wadanda basu taba sanin matsayinsa ba. Don dukkan khalifofin da suka zo gabaninsa sukan boye falalan iyalan gidan manzon All..(S) ta hanyar kona hisansa, da hana sahabbai ruwaito hadisi sai wanda ya watsu.
Kariyar da mu’awiya ya yada cikin mutanen sham dangane da Aliyu dan Abitalib (a) ya kai ga a lokacinda labara ya zo masu kan cewa an kashe shi a masallaci, sai suka ce yana sallah ne?.
Don haka yayi amfani da kissan Uthman don cimma manufarsa ta zama sarkin musulmi, don idan da za’a nemo wadanda suka ingiza mutane suka kashe Khalifa Uthman ko kuma suna da damar kareshi sannan suka ki, Mu’awiya na daga cikinsu.
Uthman ya aika masa dangane da halin da yake ciki tun kafin a kasheshi, sai mu’awiya ya aika da sojoji ya umurcesu su tsaya a kusa da Madina sai da aka kasheshi suka kama hanya suka dawo sham.
Abokinsa Amru dan Asi yana daga cikin wadanda suka ingiza mutane su kashe Khalifa Uthman, sannan suka mu’amala da Mu’awiya kan cewa idan taimaka masa kan Imam Ali(a) suka sami nasara a kansa, do zai bashi gwamnan masar, abinda kuma ya faru kenen.
Wannan kadan Kenan daga cikin dalilan da suka sa Mu’awiya ya yaki Imam Ali (a).
Dan haka bayan da Imam Ali (a) ya sami nasara a yakin siffin yayi afawar gama gari ga duk wadanda suka yake shi ko suka yi adawa shi, ya kuma maida Aisha madina, sai ya sanya ibni Abbas wali a Basra, bayan cira Uthman bin Hunaif Al-ansara.
Sai ya dawo Kufa , to amma mutanen garin suna son ya gaggauta fitowa zuwa sham don yakar mu’awiya dan Abisuyan. Sai yace, masu baya son haka. Yana son ya tafiyar da al-amarinsa da ka’ida. Don haka ya nemi wanda zai aika wajen Mu’awiya dan Abusufyan ya kai masa wasika tare da bukatar ya shiga cikin al-umma wanda ya fice daga cikinta bayan tawayen da ya shelanta.
A nane sai ya sami wani sahabanin manzon All..(s) wanda ake kira Jarir ko Jurair iban Abdullahil Bajali ya bashi wannan wasikar ya kaiwa mu’awiya. Zamu karanat wasikar a cikin shirimmu nag aba.K
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 129 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 128 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Imam Hassan (a) 127 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 126 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125 August 13, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 124 August 13, 2025 Iran: Babu Mika Kai Ga Takurawar kasashen Yamma har sai An Kawo Karshen Barazana August 13, 2025 Hukuma Mai Kula Da Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Paris Ya Dakatar Da Wani Ma’aikacinta August 13, 2025 Iraki Tace: Ita Yentacciyar Kasashe Ce Bayan da Amurka Ta Yi Korafi Kan Yarjeniyar tsaro da Iran August 13, 2025 Ministan Harkokin Wajen Masar Ya sake Ganawa da Aragchi Da Kuma Gorossy August 13, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: da mu awiya ya wadanda suka Mu awiya dan mu awiya dan awiya dan a da Mu awiya Don haka ya kan kujerar Mu awiya ya
এছাড়াও পড়ুন:
Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna
Yanzu haka mutane huɗu suna karɓar magani a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Shika, Zariya, bayan sun jikkata a wani mummunan haɗarin da ya haɗa da tankoki biyu a ƙauyen Kake, yankin Dan Magaji, kan hanyar Zariya–Kaduna. Haɗarin ya jawo mummunar gobara bayan haɗuwar motocin.
Kwamandan hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) reshen Zariya, Nasir Abdullahi Falgore, ya bayyana cewa ɗaya daga cikin tankokin na ɗauke da iskar gas (LNG), yayin da ɗayar kuma babu komai a cikinsa. Ya ce sakamakon binciken farko ya nuna tayar ɗaya daga cikin tankokin ce ta fashe, lamarin da ya sa tankar da ke biye ta bugi ta gaba, wanda ya haddasa fashewar gas da tayar da gobara.
Kwalejin Digiri Na Biyu Ta ABU Ta Ƙaddamar Da Sabbin Ɗalibai A Zariya Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na ƘasaKwamandan hukumar kashe gobara ta ƙasa a Zariya, Aminu Ahmadu Kiyawa, ya ce jami’ansa sun isa wurin cikin gaggawa bayan samun kiran wayar gaggawa. Ya tabbatar da cewa mutum uku sun jikkata sakamakon fashewar gas, yayin da aka ceto mutum guda daga ɗaya tankar, kuma duka huɗun an garzaya da su zuwa asibitin ABU domin samun kulawar likitoci.
Kiyawa ya ƙaryata jita-jitar da ake cewa haɗarin ya rutsa da ƙananan motoci irin su Gulf, yana mai cewa “Lokacin da muka isa wurin, tankoki biyu ne kawai muka gani. Babu wata ƙaramar mota da ta shiga hatsarin.” Shaidun gani da ido ma sun tabbatar da cewa tankoki biyu kacal ne suka shiga haɗarin, kuma babu wanda ya rasu a lokacin da ake haɗa wannan rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp