Dakarun Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 2nd, August 2025 GMT
Dakarun sojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin Lod na Jaffa da makami mai linzami
Dakarun sojin Yemen sun sanar da aiwatar da wani zazzafan harin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye.
Dakarun kasar ta Yemen sun yi karin haske a cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin yau cewa: Dakarun sojin Yemen masu kula da harkar makamai masu linzami sun kai wani zazzafar harin soji kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye da makami mai linzami na “Palestine 2”.
Sanarwar ta tabbatar da cewa: Harin ya samu nasarar kai wa yadda aka saita shi, wanda ya sa sama da makiyaya yahudawan sahayoniyya miliyan hudu tserewa zuwa mafakar karkashin kasa tare da dakatar da ayyukan tashar jirgin sama.
Bayanin ya yi nuni da cewa: Dakarun kasar Yemen suna sa ido kan ayyukan makiya da kuma shirinsu na burin ganin sun dakatar da taimakon kasar Yemen na goyon bayan ‘yan uwansu Falasdinawa, yana mai jaddada cewa, Dukkanin ‘yantattun al’ummar kasar Yemen masu ‘yanci, suna cikin taka tsan-tsan da kuma shiri tsaf don tunkarar duk wani yunkuri na makiya har sai sun kai ga dakile shi, kamar yadda sauran tsare-tsaren makirci, suka ci tura a lokutan baya.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Afirka August 2, 2025 Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Juyayin Shahadar Haniya Bayan Shekara Guda Da Shahada August 2, 2025 MDD: HKI Ta Kashe Falasdinawa 1 Fiye Da 100 A Cikin Kwanaki 2 A Lokacinda Suka Karban Abinci August 2, 2025 Mutanen Kasar Siriya Sun Fito Zanga-Zanga Yin Allawadai Da Kissan Alawiyya A Kasar August 2, 2025 Shugaban Ansarullah: Amurka Tana Da Hannu A Ta’asar Da HKI Take Aikatawa A Gaza August 2, 2025 Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere August 2, 2025 Iran ta yi gargadi game da makircin Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin August 2, 2025 Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar August 2, 2025 Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas Ta Karyata Gwamnatin Mamayar Isra’ila Kan Shirga Karya Don Kare Muggan Manufofinta
Kungyar Hamas ta bayyana cewa: Gmanatin mamayar Isra’ila ta ƙirƙiri ƙarya don kare kisan gillar da ta yi a Gaza
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta tabbatar da cewa: Zargin da kakakin rundunar sojin mamayar Isra’ila ya gabatar dangane da yin amfani da hasumiyai a birnin Gaza domin aikin soji ba komai ba ne illa karairayi na zahiri da suke nufin kare laifukan da ake aikatawa da kuma boye barnar da ake yi a birnin Gaza, kamar yadda a baya sojojin mamaya suka lalata garuruwan Rafah, Khan Younis, Jabaliya, Beit Hanoun, da Beit Lahiya.
A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, zargin mamaya na cewa kungiyar Hamas na amfani da fararen hula a matsayin garkuwar dan adam tare da hana su ficewa daga Gaza, yaudara ce karara da ke nuna rashin mutunta ra’ayin al’ummar kasa da kasa tare da tabbatar da dagewar da take yi na ci gaba da kisan kiyashi kan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da kuma raba su da muhallinsu da karfi da nufin korar su daga zirin Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Bayyana Abubuwan Da Bata Amince Da Su Ba A Jawabin Bayan Taro Na Kungiyar OIC A Birnin Doha September 17, 2025 Chadi: Majalisa ta amince a baiwa shugaban kasa damar ci gaba da Mulki har karshen rayuwa September 17, 2025 Iran Ta Bukaci Musulmi Su Goyi Bayan Yunkurin Kasa da Ka Na Kauracewa Isra’ila September 17, 2025 Kwamitin bincike na MDD ya zargi Isra’ila da aikata “kisan kare dangi” a Gaza September 17, 2025 Iran da Saudiyya sun bukaci hadin kan Musulmi game da halin da ake a yankin September 17, 2025 Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci