An Dawo Da Wutar Lantarki A Dukkan Kauyukan Da Aka Tafka Ruwa Da Iska A Beijing
Published: 2nd, August 2025 GMT
A yau Asabar, hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin Beijing ta sanar da cewa, an dawo da wutar lantarki da ayyukan sadarwa a dukkan kauyukan da ibtila’i ya shafa a fadin birnin na Beijing, biyo bayan mamakon ruwan sama da iska mai karfi da aka tafka, yayin da kuma ake ci gaba da aikin ceto wadanda suka bace.
Ruwan sama da iska mai karfi da aka yi fama da shi daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Yuli ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da mutane tara suka bace, a babban birnin kasar, kamar yadda aka sanar a wani taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis da ta gabata.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin ta ce, zuwa safiyar yau Asabar, an magance matsalar samar da ruwan sha a yankunan da bala’in ya shafa.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka tafka a yankunan tsaunuka na arewaci, ya haifar da lalacewar kayayyakin more rayuwa a garuruwa 40 da kauyuka 312, lamarin da ya shafi fiye da mazauna yankunan 300,000 tare da lalata gidaje kusan 24,000. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
Jamus ta shiga sahun ƙasashen duniya da ke kiran a gaggauta tsagaita wuta a yaƙin da ke ci gaba da salwantar rayuka a ƙasar Sudan.
Sama da shekaru biyu ke nan Sudan na fama da yaƙin da ya ɗaiɗaita fararen hula baya ga asarar rayuka.
Rikicin PDP: Tsagin Wike ya dakatar da Damagum Kisan Kiristoci: Za mu kai hari Najeriya — TrumpMinistan Harkokin Wajen Jamus, Johann Wadephul, ya bayyana halin da Sudan ke ciki a matsayin “mummunan bala’i,” yana mai cewa babbar matsalar jinkai ta duniya a yanzu ta tattara ne a Sudan ɗin.
A taron da aka gudanar a Bahrain, ƙasashen Birtaniya da Jordan su ma sun yi magana kan rikicin, suna kiran da a kawo ƙarshen tashin hankalin.
A ƙarshen makon da ya gabata, RSF ta kori rundunar soji daga sansanin ta na ƙarshe a yammacin Darfur.
Rahotanni daga garin El-Fasher sun bayyana cewa ana samun kashe-kashe ba tare da shari’a ba, da fyaɗe da fashi har ma da hare-hare kan ma’aikatan agaji.
Wata Kungiyar Likitoci ta MSF a ranar Asabar ta ce ana fargabar dubban fararen hula sun maƙale sannan suna cikin mummunan haɗari a birnin Al Fasher wanda ya koma hannun dakarun RSF.
Rikicin Sudan ya fara ne a watan Afrilun 2023, bayan taƙaddama ta siyasa tsakanin Janar Abdel Fattah al-Burhan, shugaban sojin ƙasar, da Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti), Kwamandan RSF.
Bayanai sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani kan yadda za a haɗa rundunar RSF da sojojin ƙasar bayan juyin mulkin 2021 da ya hamɓarar da gwamnatin farar hula.
Tun daga lokacin, yaƙin ya zama wani mummunan bala’i na jin kai, inda Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ce fiye da mutane miliyan bakwai sun tsere daga gidajensu, yayin da dubbai ke buƙatar taimakon gaggawa.