Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana.

Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana haka yayin da yake duba aikin jingar ruwan kogi da ya ratsa garuruwan Auyo da Tsidir da Agin da Matsa da Sorakin da Jiyan da Tage da Turabu da kuma Tandanu.

Alhaji Hamza Hadejia ya ce daga zuwan Gwamna Umar Namadi kan karagar mulkin Jihar, ya dauki kwararan matakai don kaucewa ambaliyar ruwa, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ya kuma bayyana cewar, Gwamna Namadi ya inganta harkar noma don tabbatar da isasshen abinci da samar da ayyukan yi ga al’ummar karkara.

A cewar sa, kwamitin fasaha na magance ambaliya ya zage damtse wajen sarrafa koguna da gina kwarya-kwaryar shinge a wuraren da ake sa ran ambaliya domin magance matsalar.

A don haka, Hamza Muhammad Hadejia, ya bukaci jama’a su ci gaba da bada hadin kai da goyon baya ga gwamnatin jihar domin a cimma wannan manufa domin kwalliya ta biya kudin sabulu.

ya kuma yabawa Gwamna Umar Namadi bisa hadin kai da goyon bayan da ya ke baiwa ayyukan kwamitin a kowane lokaci.

A jawaban su, Dagacin Turabu Malam Shu’aibu Saje da Shugaban ci gaban al’umma Sani Barde da tsohon kansila Umar Jiyan, sun jinjinawa Gwamna Umar Namadi da shugaban karamar hukumar Auyo da mai ba da shawara Hamza Hadejia bisa kokarin kare rayuka da dukiyoyin su, tare da tabbatar da gudunmawar su don cimma burin gwamnati kan magance ambaliya a yankin.

Sun kuma godewa gwamnatin jihar Jigawan da ta kananan hukumomi bisa samar da ababen more rayuwa da kuma bunkasa harkokin ilimi da lafiya da ruwa da wuta da hanyoyi da kuma bunkasa noma don samar da isasshen abinci da ayyykan yi a tsakanin al’ummomin karkara.

Usman Mohammed Zaria

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Ambaliya Jigawa Gwamna Umar Namadi

এছাড়াও পড়ুন:

Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya

Bankin Raya Ci-gaban Afirka (AfDB) ya amince da ba wa Gwamnatin Jihar Sakkwato bashin Naira biliyan 70.4 domin inganta fannin kiwon lafiya.

Wannan shiri na da nufin bunƙasa fannin kiwon lafiya da ingancinsa, da kuma cike giɓin da ake da shi a ɓangaren a Jihar Sakkwato, a cewar AfDB ta bayyana a cikin wata sanarwa ranar Juma’a.

Rahotanni na nuni da cewa, yaro ɗaya cikin kowane yara 20 ne akale yi wa allurar rigakafi cikakke a Jihar Sakkwato a, a yayin da adadin mutuwar jarirai ya kai 104 daga cikin 1,000 a Jihar.

Ƙasa da kashi 14 cikin 100 na cibiyoyin lafiya a jihar ne suke da kayan aiki masu aiki, kuma likita ɗaya ne kawai ke kula da mutum 8,285, wanda ya gaza abin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar na likita 1 ga 1,000 mutum.

Har yanzu ana fama da cutar kwalara a Najeriya – UNICEF PDP ta mutu murus a Kano — Shugaban NNPP

Kuɗaɗen da bankin ya ware za su tallafa wa samar kayan aikin kula da lafiya masu inganci a matakai uku na kula da lafiya a Jihar Sakkwato.

Wannan ya haɗa da gina sabon asibitin koyarwa mai gado 1,000, da manyan asibitoci na yankuna uku masu jimillar gadaje 450, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya guda shida da aka tsara a domin kuka da al’ummomin karkara.

Aikin ya kuma haɗa da gyaran cibiyoyin horar da ma’aikatan lafiya da ƙirƙirar sabon ma’ajiyar magunguna ta zamani.

Darakta-Janar na Ofishin AfDB a Najeriya, Abdul Kamara, ya ce, “Wannan rancen na nuna yadda muke jajircewa wajen aiki tare da gwamnati don magance giɓin kayan kiwon lafiya a Najeriya, tare da gina cibiyoyin kula da lafiya masu ƙarfi da suka dace da tsari na yanayi.

“Ta hanyar ƙarfafa kayan aikin lafiya a Jihar Sakkwato, muna gina fata da hanyoyin samun kyakkyawan sakamako ga miliyoyin ’yan Najeriya.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ana Gaggauta Ayyukan Gyara Tituna Da Gadojin Da Ambaliya Ta Lalata A Arewacin Kasar Sin
  • Shirin ACRESAL Zai Samar Da Injinan Ban Ruwa Masu Amfani Da Hasken Rana A Jigawa
  • Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare
  • Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA
  • Yadda Kwamishinan Kano Ya Karɓi Dala $30,000 Domin Yin Belin Dilan Ƙwaya A Kotu – Rahoto
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Sha Alwashin Inganta Kwazon Kananan Hukumomin Jihar
  • HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
  • Manyan Ƙalubale Takwas Da Ke Shafar Farashin Tumatir
  • Jihar Sakkwato ta ciyo bashin N70.4bn domin inganta kiwon lafiya