An Zargin Akantan jihar Nasarawa Da Shiga Harkokin Siyasa
Published: 5th, August 2025 GMT
Kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa reshen jihar Nasarawa ta kalubalanci kungiyar tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari (NS-TA&G), da su tabbatar da zargin nuna son kai wajen sauke nauyin da babban Akanta Janar na jihar, Ahmed Musa Mohammed ke yi.
Ko’odinetan kungiyar na jiha Abimiku Dangana Solomon ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wani jawabi da Mista Lazarus Salaki, ko’odinetan kungiyar NS-TA&G2 na jihar ya yi a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Lafia babban birnin jihar.
Mista Abimiku Dangana ya ce, hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan bai hana masu rike da mukaman gwamnati da ma’aikatan gwamnati shiga harkokin siyasa da shiga jam’iyyun siyasa ba.
Kungiyar ta kuma bayyana cewa, shari’ar INEC da Ahmed Musa inda mai shari’a Ayoola da Justice Mohammad Uwais suka jaddada cewa dokokin ma’aikatan ba za su iya maye gurbin tanadin tsarin mulki ba.
“Muna kalubalantar Hukumar NS-TA&G2 da ta ba da shaidar nuna fifiko na musamman da ake zargin an yi mata ko kuma an yi kasa a gwiwa wajen sauke nauyin da Akanta Janar na Jiha ke yi.
Idan za a iya tunawa wata kungiyar da abin ya shafa a karkashin Mista Lazarus Salaki, ta yi kira ga Mista Musa Ahmed Mohammed, Akanta Janar na Jihar Nasarawa ya yi murabus, bisa zarginsa da hannu a harkokin siyasa yayin da yake rike da wani mukami mai muhimmanci.
Kungiyar ta kuma bayar da misali da umarnin da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Mohammed Uban-doma Aliyu ya bayar a ranar 16 ga Afrilu, 2024, inda ya umurci duk masu rike da mukaman siyasa masu burin shiga zabe da su yi murabus ko kuma su dakatar da harkokin siyasa har sai Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa INEC ta bayyana matsayarta.
Mista Lazarus Salaki ya yi zargin cewa, duk da wannan umarnin, wasu da aka nada sun ci gaba da yakin neman zabe da kuma gudanar da taron siyasa yayin da suke kan mukamansu.
COV/Aliyu Muraki/Lafia.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: nasarawa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama mutum 9 kan yin garkuwa da kansu
Rundunar ’yan sandan Jihar Neja ta kama wasu mutane tara da ake zargi da shirin yin garkuwa da kansu tare da neman kuɗin fansa Naira miliyan 7.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, inda ya ce waɗanda ake zargin na da hannu a cikin shirin zamba na Ponzi, kuma ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya samu kuɗin fansa daga abokan aikinsu.
An kama sojan bogi da ɓarayin mota 2 a Jigawa Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin ministaAn kama ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin mai suna Suleiman Dauda a Minna babban birnin jihar, inda daga bisani ya ambaci wasu mutum takwas da ake zargin yayin da ’yan sanda ke yi musu tambayoyi.
“A ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 10 na dare, an samu rahoto a yankin Tudun-Wada na wani da ake zargi da yin garkuwa da mutane a kusa da unguwar Mandela da ke Minna, sannan kuma an kira shi ta wata baƙuwar lambar wayar salula ana neman kuɗin fansa Naira miliyan 7.
“A cikin binciken da ake yi, a ranar 3 ga Satumba 2025, an kama wani wanda ake zargi mai suna Suleiman Dauda da laifin aikata laifin, kuma bisa ga tambayoyi, an kama wasu mutum takwas a unguwar Mandela.
“A binciken da aka yi, an ƙwato katin wayar salula SIM guda 21 da satifiket 29 a hannun Suleiman, bisa zargin cewa yana yin rijistar katin SIM ne, ya kuma yarda cewa lambar waya salula da ake neman kuɗin fansa ya ba wanda aka aka yi garkuwan da shi.”
Duk da haka ya bayyana cewa, “Binciken da aka yi ya nuna cewa, waɗanda ake zargin sun fito ne daga wurare daban-daban a ciki da wajen jihar suna gudanar da shirin zamba na Ponzi, kuma an gano cewa ɗaya daga cikin tawagarsu ya shirya da wanda ake zargin ya karɓi kuɗin fansa daga abokan aikinsu.
Abiodun ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike da nufin ganowa tare da cafke wasu, yana mai cewa waɗanda ake zargin an gurfanar da su a gaban kotu.