Aminiya:
2025-07-11@08:54:52 GMT

An kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da mayaƙa 100 a Katsina

Published: 12th, April 2025 GMT

Jami’an tsaro sun samu nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ake kira Gwaska Ɗan Ƙarami da wasu mayaƙa 100 a Jihar Katsina.

Kwamishinan Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Dokta Nasir Mu’azu ya bayyana matakin a matsayin wata gagarumar nasara a yaƙi da ’yan bindiga ake yi a jihar.

An kama mutum 8 kan faɗan daba a Kano Ziyarar da Atiku ya kai wa Buhari ba ta dami APC ba — Ganduje

“Abin farin ciki ne ga jihar, domin wannan nasara ta taimaka wajen wargaza ayyukan ’yan bindigar da ke addabar garuruwa da ƙauyukan da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur,” in ji Kwamishinan.

Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin Nijeriya tare da ɓangaren sojin saman ƙasar ne suka ƙaddamar da hare-haren a ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025 a dabar ɓarayin daji a Mununu Bakai da Zango da Jeka Arera da Malali, da kuma Ruwan Godiya duka a cikin ƙananan hukumomin Kankara da Faskari.

Haɗin gwiwar jami’an tsaron ƙasar ne suka ƙaddamar da harin a ranar Juma’a wanda ya yi sanadin kisan Gwaska — wanda ya kasance mataimakin shahararren ɗan bindiga Malan, shugaban ISWAP a yankin Arewa Maso Yamma.

“Hare-haren da suka yi daidai kan ɓarayin, bisa bayanan sirrin da aka samu, sun yi silar kashe wani wanda ake nema ruwa-a-jallo da aka fi sani da Gwaska, wanda mataimaki ne ga wani shugaban ’yan bindiga mai alaƙa da ISWAP,” in ji shi.

“Bayanan sirri sun tabbatar da cewa kwanan nan ne Gwaska ya yi ƙaura daga Ƙaramar Hukumar Danmusa zuwa dajin Munumu.

Rahotonni sun ce sojojin sun lalata maɓoyar ’yan bindigar da dama a sassan jihar a lokacin harin, tare da ƙwato da kuma lalata wasu manyan bindigogi masu jigida da waɗanda aka ƙera a cikin gida.

Harin na zuwa ne bayan da a farkon mako ’yan bindigar suka yi garkuwa da mutum 43 mazauna ƙauyukan Maigora da ke yankin Ƙaramar Hukumar Dandume.

Kazalika, dakarun tsaro sun ƙaddamar da wani aiki da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025, a hanyar da ɓarayin daji ke bi a Dutsen Wori gefen hanyar Dandume zuwa Kandamba, da ke wajen garin Dandume a kan iyaka da ƙananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Aikin da aka aiwatar da misalin ƙarfe 3:45 na dare ya yi silar kashe ɓarayi shida ciki har da shugabansu, yayin da sauran ɓarayin suka tsere da raunukan bindiga.

Bayanai sun nuna cewa dakarun sun ƙwace mashina bakwai yayin da saura huɗu suka tsere cikin daji.

An bi sawun ɓarayin ne daga dabarsu da ke Maigora/Doroyi cikin Ƙaramar Hukumar Faskari.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Jihar Katsina yan bindiga

এছাড়াও পড়ুন:

Babu Wanda Ya Buƙaci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC

Jam’iyyar ADC ta musanta labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa wasu shugabanni daga yankin Kudu sun buƙaci Atiku Abubakar, da ka da ya fito takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, ta ce wannan labari ƙarya ne, wanda aka ƙirƙira don haddasa rikici , musamman a wannan lokaci da ake ƙoƙarin haɗa kan ‘yan adawa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a Nijeriya.

Amurka Ta Tsaurara Matakan Bai Wa ‘Yan Nijeriya Biza Kofin Duniya: Chelsea Ta Kai Wasan Ƙarshe Bayan Ta Doke Fluminense

Jam’iyyar ta ce: “Ba mu taɓa zama da wasu wakilai daga Kudu domin yin irin wannan magana ba.

“Wannan rahoto ba kawai ƙarya ba ne, yana kuma iya haddasa rikici da rashin fahimta tsakanin ‘yan Nijeriya.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sojoji sun kashe ’yan fashin daji masu yawan gaske a Zamfara
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 13 a ƙauyukan Neja
  • Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 30 a Katsina
  • Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 13 A Neja
  • Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 30 A Katsina
  • Babu Wanda Ya Buƙaci Atiku Ka Da Ya Yi Takara A 2027 – ADC
  • Kaso 90 na ’yan bindigar da suka addabi Katsina ’yan asalin jihar ne – Radda
  • An kama ɓarayin babura a Gombe
  •  Wani Fim Din Iran Mai Ya Sami Kyauta A Baje-Kolin Fina-finai Na Shanghai
  • Kakakin Rundunar Izzuddeen Qassam ya Bayyana Yadda Suka Yi Kofar Rago Ga Sojojin Mamayar Isra’ila