HausaTv:
2025-04-30@18:41:32 GMT

Najeriya Tana Fatan Samun Dalar Amurka Biliyan $200 A Ayyukan Sararin Samaniya

Published: 12th, April 2025 GMT

Gwamnatin tarayyar Najeriya tace tana fatan samun dalar Amurka billiyon $200 a ko wace shekara, a ko wace shekara daga ayyukan sararin samani.

Jaridar Premiun times ta Najeriya ta nakalto ministan kirkire-kirkira da fasahar sararin samaniya yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa kamfanonin sadarwan da suke cikin kasar kamar Starlink da DSTV.

Banda haka yace jiragen ruwa masu shigowa kasa ba zasu kaucewa biyan haraji ko kudin foto ba, saboda kayakin aiki na sararin samaniya wanda kasar take da su.

Ministan yace shugaba Tinubu ya bada umurni a yi amfani da fasahar sararin samaniya wajen ayyukan gas da man fetur.

Uche Nnaji ya ce gwamnati tana fatan samun karin dala biliyon 20 a wannan bangaren.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Fira Ministan Indiya Ya Bayyana Cewa: Iran Tana Kokari A Fagen Inganta Zaman Lafiya A Yanki Da Duniya Baki Daya

Fira ministan Indiya ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana kokari da zage dantse wajen taimakawa a fagen inganta zaman lafiyar yanki da na duniya baki daya

Fira ministan Indiya Narendra Modi ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya, yana mai cewa: Gwamnatin Indiya tana goyon bayan kokarin Iran na karfafa zaman lafiya a yankin da ma duniya baki daya, yana mai jaddada bukatar warware takaddama ta hanyar diflomasiyya, ciki har da na Iran da Amurka.

Har ila yau fira ministan na Indiya ya bayyana matukar bakin cikinsa dangane da abin da ya faru a tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’e da ke lardin Hormozgan a kudancin kasar Iran, ya kuma bayyana cewa kasarsa a shirye take ta ba da duk wani taimako ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Modi ya bayyana kyakkyawar fatansa na lafiya da burinsa ga shugaban kasar Iran da jagoran juyin juya halin Musulunci da kuma ci gaba da wadata ga al’ummar Iran masu girma.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Xi Ya Jaddada Muhimmancin Tsara Nagartaccen Shirin Raya Tattalin Arziki Da Zamantakewar Al’umma Tsakanin 2026-2030
  • Talauci Da Rashin Ilimi Ne Ya Sa Ayyukan Boko Haram Ke Dawowa – Gwamnan Yobe
  • Arsenal Da PSG: Wa Zai Yi Nasara A Gasar Zakarun Turai A Yau?
  • HKI Tana Amfani Yunwa A Matsayin Makamin Yaki  A Kan Falasdinawa A Gaza
  • Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Ayyukan Sadarwa
  • Makafi 37 Sun Zana Jarabawar JAMB A Bauchi
  • Sin Za Ta Aiwatar Da Matakan Daidaita Samar Da Guraben Ayyukan Yi Da Raya Tattalin Arziki
  • Ƴan Ta’adda Sun Kashe Maharba 10 A Adamawa
  • Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Wajabcin Kawo Karshen Ayyukan Ta’addanci A Kasashen Yanki
  • Fira Ministan Indiya Ya Bayyana Cewa: Iran Tana Kokari A Fagen Inganta Zaman Lafiya A Yanki Da Duniya Baki Daya