Ya ci gaba da cewa, tuni aka fara gudanar da wasu manyan ayyukan a Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, musamman a ta Lekki da ta Tin Can Island.

Shugaban ya bayyana cewa, an kuma samar da kafar sadarwa ta zamani ga masu ruwa da tsaki a daukacin Tashoshin Jiragen Ruwan Kasar, domin a rinka yin musayar Data, har da lokacin da ya dace, a fara gudanar da aiki.

Ya sanar da cewa, idan an kammala wannan aikin, za su kara taimaka wa wajen kara inganta ayyukan Hukumar, na tsawon sa’oi 24.

Dantosho wanda Manajan Sashen Tashar da ke a jihar Legas Lawal Ibrahim ya wakilce shi a wajen taron ya bayyana cewa, Hukumar ta kuma yi hadaka da Rundunar Sojin Ruwa, Rundunar ‘Yansanda ta kasa da kuma Hukumar Kula da Tsaro da sufurin jiragen Ruwa ta Kasa NIMASA musamman domin a kara karfafa samar da tsaro da kuma bai wa ma’aikatan Hukumar kariya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban.

Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na ganin hakan ya yi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.

Shin ko me dokar kasa ta ce game da wannan karin wa’adi da shugaban kasan ya yi?

NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta
  • Abin Da Ya Sa NPA Da Kwalejin MAN Oron Suka Yi Haɗin Gwiwa
  • Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansaninta a Kebbi
  • An Zaɓi Saidu Yahya A Matsayin Shugaban Hukumar Yaƙi Da Cin Hanci Ta Kano
  • NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?
  • INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
  • Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin aikin shugaban hukumar Kwastam
  • Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
  • Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo