Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabino
Published: 4th, August 2025 GMT
Gwamnatin Najeriya ta ce tana sa ran samun kimanin Naira biliyan 300 a duk shekara daga noman dabino a ƙasar.
Ta ce tana fatan samun wannan kuɗaɗen shiga ne daga rabon irin dabino guda miliyan biyar da ta samar ga manoma a wannan shekara ta 2025.
Darakta-Janar na Hukumar Yaƙi da Kwararowar Hamada (NAGGW), Alhaji Saleh Abubakar, ya ce, “Kowane iri ƙwaya ɗaya na iya samar da miliyan 100 na dabino, wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan ɗaya.
“Muna hasashen manoma za su samar da Naira biliyan 300, wanda tabbas zai bunƙasa tattalin arzikin Najeriya,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta raba irin dabino miliyan biyar da ta samar ga jihohi 11 da ke maƙwabtaka da saharar hamada domin su ci gajiyar tattalin arzikin noman dabino.
Ya sanar da haka ne a yayin taron ƙaddamar sashen itatuwa a ƙauyen Maimalari da ke Ƙaramar Hukumar Yusufari ta Jihar Yobe.
A cewarsa, manufar shirin ita ce bunƙasa tattalin da ke cikin ɓangaren gandun daji wajen samar da ƙarin kuɗaɗen shiga da harkokin kasuwanci a jihohi takwas da ke gaɓar hamada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: kwararowar hamada Saharar Hamada
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Buba Ya ƙaryata Jita-jitar Cewa Majalisa Ta Amince da ƙirƙiro Sabbin Jihohi 12
Sai dai tuni masu sanatoci da dama, kamar Sanata Shehu Buba, da Sanata Abdul Ahmad Ningi da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya suka ƙaryata labarin da cewa babu gaskiya a cikinsa tare da neman jama’a da su yi watsi da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp