Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami
Published: 5th, August 2025 GMT
Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON.
Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci musamman zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a karrama su saboda yadda suka ɗaga sunan Najeriya a idon duniya a fannin ilimi.
“Ina kira da babbar murya cewa a a ba wa Nafisa kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa daga Gwamnatin Tarayya.”
A cikin saƙon da ya wallafa a safiyar Talata, Pantami ya ƙara da cewa malaman Nafisa sun cancanci irin kyautar da aka yi wa tawagar masu horas da ’yan wasan Najeriya ta lambar OON da tsabar kuɗi Dala 50,0000 da kuma gida ga kowannensu, musamman ma tun da nasarar da suka samu a fannin ilimi ne.
’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje“Su ma malananta a ba su kyauta irin wadda aka yi wa masu horas da ’yan wasan ƙwallon Najeriya. Wajibi ne mu ba wa ilimi muhimmancin da ya dace tare da karrama ƙwazon ’yan kasarmu,” in ji Pantami.
Bayanin na zuwa ne washegarin da Gwamnatin Tarayya ta yi irin wannan kyauta ga kowacce daga ’yan wasan ƙwallon kwandon Najeriya na D’Tigress kan lashe gasar Kaifin Nahiyar Afirka ta shekarar 2025.
Ƙasa da mako guda ke nan kuma bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi irin wannan kyauta ga ’yan wasan ƙwallon ƙafan mata ta Super Falcons bayan sun lashe gasar Kofin Nahiyar Afirka ta bana.
Aminiya ta ruwaito cewar Nafisa Abdullah Aminu ta lashe Gasar Turanci ta Duniya ta Teen Eagle da aka gudanar a ƙasar Birtaniya.
Nafisa daga Kwalejin Nigeria Tulip International (NTIC) da ke Jihar Yobe ta doke abokan fafatawarta daga ƙasashe 69 domin zama Gwarzuwar Shekarar 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gasar Turanci kyautar Dala 100 yan wasan ƙwallon
এছাড়াও পড়ুন:
Karamar Hukumar Malam Madori Ta Horar Da Mata Kare Kai Daga Cututtukan Mahaifa
A ƙoƙarinta na ƙara wayar da kan jama’a game da harkokin lafiya a birane da karkara na Malam Madori, majalisar ƙaramar hukumar ta horar da mata da ‘yan mata 50 kan tsafta a lokutan al’ada domin kare kansu daga cututtukan mahaifa.
Jami’in shirin, Malam Ali Haruna, ya ce an zaɓi mahalarta horon ne daga kowace gunduma ta yankin
A cewarsa, manufar horon ita ce koyar da mahalarta yadda za su samar da kariya yayin al’ada da kansu domin rage kashe kuɗi da kuma kare kansu daga kamuwa da cututtukan mahaifa.
Shi ma shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Shehu Sani Gwadayi, ya bayyana cewa tsafta na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar ɗan adam domin inganta rayuwa da ƙarfafa garkuwar jiki.
A nasa jawabin, mataimakin shugaban sashen ruwa da tsafta, Malam Muhammad Abdullahi, ya yi wa mahalarta horon bayani kan muhimmancin tsafta yayin al’ada domin gujewa kamuwa da cututtuka.
Shugaban ƙaramar hukumar Malam Madori, Alhaji Salisu Sani Garun Gabas, ya shawarci mahalarta da su mai da hankali ga sashen aikace-aikace na yadda ake sarrafa audugar mata a gida yayin horon.
Usman Muhammad Zaria