Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai
Published: 3rd, August 2025 GMT
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya.
El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya.
Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a TarabaYa ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Najeriya sun sauke APC daga kan mulki.
“Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya zai lalace.
“Ƙasar na iya fuskantar barazana,” in ji shi.
“Wannan dai ta zama gwagwarmaya don ceto rayuwarmu.”
El-Rufai, ya ce dawowarsa siyasa ba don wata riba ko matsayi ba ne, sai don yana ganin gwamnatin yanzu ta gaza.
“Ba don ƙashin kaina nake wannan ba. Na dawo siyasa ne domin na yi wa al’umma hidima. Idan gwamnati ba ta cika alƙawari ba, dole ne na fito na faɗi gaskiya kuma na ɗauki mataki,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa haɗakar ADC an kafa ta ne domin yaƙar manufofin APC.
Ya ce gangamin da aka yi a Sakkwato shi ne farkon matakin neman goyon bayan jama’a a faɗin ƙasar nan.
El-Rufai, wanda ya ɗaya ne daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC, ya fice daga jam’iyyar a watan Maris, 2025.
Ya koma jam’iyyar SDP, saboda rashin jin daɗin yadda ake tafiyar da mulki a Najeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan siyasa Sakkwato jam iyyar a
এছাড়াও পড়ুন:
Arewa Ba Zata Ƙarɓi Mulki A 2027 Ba, Gwamna Bago
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp