Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa
Published: 4th, August 2025 GMT
Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An yi wa Jalo Daudu a sarautar Tafarkin Gombe
Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu sarautar Tafarkin Gombe.
Dakta Daudu, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Sakatare na Tarayya da Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe.
Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5 Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-RufaiDaga baya ya zama Shugaban Ma’aikata a Gwamnatin Jihar Gombe, sannan ya riƙe wasu manyan muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa.
Yanzu haka, shi ne Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikata na Ƙasa, inda yake wakiltar Jihohin Adamawa, Gombe da Taraba.
Dakta Daudu ya fito ne daga gidan sarauta a Gombe, kuma kakansa shi ne Hakimin Gombe na farko bayan masarautar ta koma zuwa birnin Gombe a yanzu.
Har ila yau, shi ne Ɗan Masanin Funakaye.
Sarautar Tafarki na ɗaya daga cikin manyan sarautun gargajiya a ƙasar Hausa.
Ana bai wa ɗan Sarki ko babban ɗan uwansa sarautar, kuma zai dinga bai wa Sarki shawara ko gyara idan ya zama dole.
Mai riƙe da wannan sarauta yana da damar shiga fada kai-tsaye da bai wa Sarki da masarauta shawara.
Asalin sarautar Tafarki ta samo asali ne tun zamanin Hausa Bakwai, kuma an ce mutum na farko da aka bai wa wannan sarauta shi ne Musa, a lokacin Sarkin Katsina Umaru Dallaje.
Yayin da yake sanar da naɗin, Sarkin Gombe, ya bayyana Dakta Daudu a matsayin mutum mai ƙwarewa, kuma wannan ne ya sa ya dace da wannan matsayi domin bai wa masarautar shawara.
Dakta Daudu, ya nuna farin ciki da godiyarsa ga Sarkin Gombe da majalisarsa, inda ya ce zai yi amfani da wannan dama wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.