Jaridar Isra’ila Ta Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Sha Kashi A Yakin Gaza
Published: 2nd, August 2025 GMT
Jaridar Ma’arif ta Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fuskantar daya daga cikin manyan shan kashi a tarihinta
Masanin harkokin soji na jaridar Ma’ariv ta Isra’ila Avi Ashkenazi ya amince da cewa: Isra’ila na fuskantar matsala ta gaske bayan shafe kusan watanni 22 ana yakin Gaza, yana mai cewa gazawar tsarin siyasar Isra’ila na yanke kwakkwarar shawara da kuduri da suka kamata ya sa Isra’ila ta kai ga daya daga cikin manyan shan kaye a tarihinta, na siyasa da kuma dabaru.
Avi Ashkenazi, wani manazarcin harkokin soji na jaridar Ma’ariv, ya amince cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fuskantar “matsala ta gaske” bayan shafe kusan watanni 22 na yakin Gaza. Ya kara da cewa, “Rashin iyawar tsarin siyasar Isra’ila na yanke shawara da balagagge da sanin ya kamata, shi ne ya sa Isra’ila ta kai ga daya daga cikin babbar kaye a tarihinta, a siyasance da kuma dabaru.”
Ashkenazi ya jaddada cewa: Babban muhimmin wannan shan kashi shi ne gazawar gwamnatin mamayar Isra’ila wajen cimma manufofin da ta ayyana tun daga ranar farko ta yakin, musamman kwato wadanda aka yi garkuwa da su. Ya kara da cewa; Hakikanin abin da ke faruwa a kasa ya tabbatar da cewa; Har yanzu ‘yan gwagwarmaya suna nan da karfinsu yayin da shugabannin gwamnatin mamayar Isra’ila ke ta yawo a shawarwarin da suke yi da kuma trsanantan sabani a cikin gida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dakarun Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 2, 2025 Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Afirka August 2, 2025 Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Juyayin Shahadar Haniya Bayan Shekara Guda Da Shahada August 2, 2025 MDD: HKI Ta Kashe Falasdinawa 1 Fiye Da 100 A Cikin Kwanaki 2 A Lokacinda Suka Karban Abinci August 2, 2025 Mutanen Kasar Siriya Sun Fito Zanga-Zanga Yin Allawadai Da Kissan Alawiyya A Kasar August 2, 2025 Shugaban Ansarullah: Amurka Tana Da Hannu A Ta’asar Da HKI Take Aikatawa A Gaza August 2, 2025 Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere August 2, 2025 Iran ta yi gargadi game da makircin Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin August 2, 2025 Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar August 2, 2025 Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: mamayar Isra ila Isra ila ta Isra ila na
এছাড়াও পড়ুন:
Duniya na tir da sabon farmakin Isra’ila kan Gaza
Kasashen duniya na ci gaba da yin tir da sabon farmakin soji da Isra’ila ta kaddamar kan Gaza.
Kasashen Biritaniya, Faransa, Italiya, Masar, Jordan, Qatar, Spain, duk sun yi tir da farmakin kan Gaza suna masu cewa zai kara dagula halin kunci da ake ciki.
Kungiyar tarayyar Turai, ta bakin Jami’ar kula da harkokin wajen ta, Kaja Kalas, ta yi kira da a sanyawa Isra’ila takunkumi domin matsa wa gwamnatin lamba ta kawo karshen hare-haren da take kaiwa Gaza, tana mai gargadin cewa al’amuran jin kai na kara ta’azzara.
“Hare-haren da Isra’ila ta kai a Gaza zasu haifar da mummunan sakamako game da halin da ake ciki da karin hasarar rayuka, da barna & hijira na jama’a,” in ji Kalas a kan X.
A jiya ne Sojojin Isra’ila suka kaddamar da sabon farmakin ta kasa mai manufar mamaye birnin Gaza bayan shafe makwanni ana kai hare-haren bama-bamai ba kakkautawa ba a kan wasu manyan gine-gine domin tilastawa Falasdinawa kauracewa gidajensu.
Farmakin ya zo ne jim kadan bayan da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya gana da firaminista Benjamin Netanyahu a kusa da masallacin Al Aqsa da ke gabashin birnin Kudus da aka mamaye.
Tun da farko dai, wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan yankunan Falasdinawa da ke mamaye, Francesca Albanese ta yi Allah wadai da hare-haren da Isra’ila ke kai wa birnin Gaza, tana mai cewa wani bangare ne na shirin Isra’ila na shafe Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Saudiyya sun bukaci hadin Musulmi game da halin da ake ci a yankin September 17, 2025 Akalla Falasdinawa 78 ne sukayi shahada a hare-haren Isra’ila a Gaza September 17, 2025 Akalla Falsdinawa 78 Ne Suka Yi Shahada A Yau A Gaza. September 16, 2025 Isra’ila Ta Kai Hari A Tashar Jirgin Ruwan Hudaida Dake Yamen September 16, 2025 Iran Ta Gabatar Da Sabbin Kayayyaki 5 A Wajen Taron kere-kere . September 16, 2025 Iran Ta Bukaci IAEA Tayi Tir Da Harin Da Isra’ila Ta Kai A Tashoshin Nukiyarta. September 16, 2025 Jonathan Zai Jagoranci Taron Tattaunawa Kan Dimokuraɗiyya A Ghana September 16, 2025 Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi September 16, 2025 Pezeshkian: Ta’addancin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Kan Kasar Qatar Zalunci Ne Ga Diflomasiyya September 16, 2025 Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya September 16, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci