Aminiya:
2025-11-02@21:12:51 GMT

Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA

Published: 3rd, August 2025 GMT

Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta ce aƙalla mutane 165 ne suka rasu, sannan 82 suka ɓace sakamakon ambaliya a bana.

NEMA ta bayyana haka ne a ranar Juma’a a wata ƙididdiga da ta fitar, tana mai cewa ambaliyar ta shafi aƙalla mutum 119,791 a bana — kuma mafi akasari mata ne da yara.

Dadiyata: Buhari ya gaza nemo shi, Tinubu yana da lokaci — Amnesty Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a Abuja

Ta bayyana cewa mutane 138 sun samu raunuka iri-iri, 43,936 sun rasa matsugunansu, gidaje 8,594 da gonaki 8,278 ne ambaliya ta shafa a cikin ƙananan hukumomi 43 da ke jihohi 19.

Ta ce, “Yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304 da kuma mutane 1,863 masu nakasa ne ambaliya ta shafa a bana.”

Jihohin da suka fi yawan waɗanda ambaliya ta shafa sun haɗa da Imo, Ribas, Abia, Borno da Kaduna.

A halin yanzu, jihohi 19 da ambaliya ta shafa sun haɗa da: Abia, Abuja, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Ribas da Sakkwato.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ambaliya Nijeriya ambaliya ta shafa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya

Daga Ali Muhammad Rabi’u 

 

Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi  ritaya a matakin jiha da  kananan hukumomi.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.

A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.

Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da  biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.

Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.

 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba
  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  •  Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada
  • Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
  • An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
  • Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
  • An raba wa iyalan jami’an ’yan sandan da suka rasu a bakin aiki a Borno N63.4m