Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Namijin Kokarinsu
Published: 4th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin ‘yan sahayoniyya a yakin kwanaki 12
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Al’ummar Iran sun dakile shirin yahudawan sahayoniyya a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa. A lokacin da yake halartar taron manema labarai da kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Ismail Baqa’i ya gudanar a yau Litinin, Araqchi ya ce: Na farko dai ya zama wajibi a gare shi ya girmama dukkanin shahidai: shahidan juyin juya halin Musulunci, shahidan tsaro mai alfarma (1980-1988), da dukkanin shahidan da suka sadaukar da rayuwarsu wajenkare kasa, tun farko-farko har zuwa yau, musamman ‘yan jaridu da shahida yakin matsorata masu wuce gona da iri na yakin kwanaki 12.
Ministan harkokin wajen kasar ya kara da cewa: Babu shakka wannan yaki zai kasance daya daga cikin abubuwan da ba za a taba mantawa da shi ba a tarihin Iran na yau da kullum, yakin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya masu laifi tare da goyon baya da hadin gwiwar manyan kasashen duniya da sauran su suka kaddamar na wuce gona da iri kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da fatan cimma munanan manufofinsu da wani harin ba-zata cikin kankanin lokaci, to sai dai al’ummar Iran sun sake tabbatar cewa sun yi tsayin daka tare da zage dantse babu abin da zai kawar da su kan azamarsu, saboda mutane suna ne da saiwoyinsu suka shimfiɗa a cikin kasa sama da dubban shekaru, saiwoyin suke kara karfi kowace rana, ƙasar da ta wanzu saboda sadaukarwa, da tsayin daka, da Imani.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasar Iran Ko Da Zata Sake Tattaunawa Da Amurka Zata Kasance Dauke Da Makamai Cikin Shirin August 4, 2025 Rahotonni Sun Bayyana Cewa; Agajin Jin kai Da Ake Wurga Ta Sama A Gaza Tamkar Digon Ruwa Ne August 4, 2025 Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba August 4, 2025 Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu August 4, 2025 Pakisatan: Iran Ce Madogara Ga Al-ummar Musulmi August 4, 2025 Wakilin Hukumar FAO A Iran Yace Sauyin Yanayi Ya shafi Dukkan Yankin August 4, 2025 Malamai A Najeriya Suna Goyon Bayan Iran A Yadda Take Fuskantar HKI August 4, 2025 Shugaban Kasar Lebanon Ya Yi Alkawalin Adalci Ga Wadanda Feshewar Beirut Ta Shafa August 4, 2025 Iran Ta Ce Ba Wani Ma’aikacin Hukumar IAEA A Kasar A Halin Yanzu August 4, 2025 Pezeshkian ya yaba da irin goyon bayan da Pakistan ta baiwa Iran a lokacin yaki August 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Ministan harkokin wajen kasar Al ummar Iran
এছাড়াও পড়ুন:
Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
A ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da HKI ke yi a kasar labanon a jiya ma ta kai hari a kudancin kasar kuma ta yi sanadiyar mutuwar mauta 4 tare da jikkata wasu guda 3,
Isra’ila ta kai hari da jirgin sama mara matuki kan wata mota a kauyen kafr rumman , kana kuma ta sake kai wani harin a garin kafr sir kamar yadda rahotanni suka bayyana, kuma wadannan hare haren suna zuwa ne kwanaki 3 bayan da sojojin israila suka kai samame ta kasa a kudancin labanon a yankin Nabatiya inda suka kai hari a jiya,
A ranar jumaa da ta gabata ne shugaban kasar ta labanon joseph Aun ya nuna damuwarsa game da ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Isra’ila ke yi, inda yayi tir da tel aviv game da irin mataken da take dauka na karya yarjejeniyar.
A yan kwanankin nan sakatare janar din kungiyar hizbullah na kasar labanon shaikh Naim Qassem ya jaddada cewa tsayin daka ne karfin labanon, don haka Amurka na matsin lamba ne don ganin an danneta an tauye mata yanci da raunata ta don biyan muradun gwamnati.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya November 2, 2025 Shugaban AmurkaTrump ya yi barazanar daukar matakin soji kan Najeriya November 2, 2025 Kamaru: Jagroan ‘Yan Hamayya Ya Yi Kira Da A Tsayar Da Harkoki A Fadin kasar November 1, 2025 MDD Tana Sa Ido Akan Kashe-kashen Da Ake Yi A Zaben Kasar Tanzania November 1, 2025 Gaza: Daga Tsagaita Wuta Zuwa Yanzu Fiye Da Mutane 200 Ne Su Ka Yi Shahada November 1, 2025 Shugaban Najeriya Ya Mayar Da Martani Ga Takwaransa Na Amurka Akan Rikicin Addini November 1, 2025 Iran ta damu da halin da ake ciki a yankin El Fasher na Sudan November 1, 2025 Kwamitin Tsaron MDD ya goyi bayan shirin Morocco game da yankin Yammacin Sahara November 1, 2025 Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben shugaban kasa a Tanzaniya November 1, 2025 Najeriya ta musanta ikirarin Trump, na cewa Kristoci na fuskantar babbar barazana a kasar November 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci