Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki.

 

Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano.

 

Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su yi wa jihar hidima cikin himma da gaskiya.

 

 

Ya ce matakin ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da jihar ke yi na inganta samar da abinci da kuma habaka arzikin iyali.

 

 

Gwamna Yusuf ya bayyana daukar ma’aikata a matsayin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma wani muhimmin mataki na cimma wadannan manufofin.

 

“Yau rana ce ta sabuwar dama da cika alkawarin da muka dauka a yakin neman zabe, wadannan ayyuka ba wai kawai za su tallafa wajen samar da abinci ba, har ma da samar da kudaden shiga ga dubban iyalan Kano.”

 

Gwamnan ya bayyana cewa, duk da cewa Kano ta riga ta jagoranci kasar nan wajen yawan ma’aikata, amma duk da haka jihar na bukatar karin biyan bukatun noma na zamani.

 

 

“Muna bukatar karin kwararrun ma’aikatan da za su yi wa al’ummominsu hidima, da tallafa wa manomanmu, da kuma taimakawa wajen kawo sauyi a fannin noma.”

 

Gwamna Yusuf ya gargadi sabbin ma’aikatan da su guji cin hanci da rashawa, rashin zuwa aiki, da rashin tausayi, yana mai jaddada cewa daukar ma’aikata ba wata hanya ce ta wawure dukiyar al’umma ba.

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga 19, Sun Ƙwato Makamai A Kano November 3, 2025 Manyan Labarai Mayar Da Martani Kan Barazanar Amurka Ga Nijeriya: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yaba Wa Kwankwaso  November 3, 2025 Manyan Labarai Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi November 3, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Namadi Ya Yaba Da Tasirin Shirin NG-CARES A Jihar Jigawa
  • Kwamishinan Ƴansanda Na Kano Ya Karrama Sabbin Jami’an Da Aka Ƙara Wa Matsayi
  • Isra’ila ta aikata laifuka 194 tun bayan tsagaita wuta a Gaza
  • NARD Ta Yi Fatali Da Iƙirarin Gwamnatin Tarayya Na Ba Ta ₦43bn, Kuma Yajin Aiki Na Nan
  • Kano Ta Amince Da Naira Biliyan 8.2 Don Ayyukan ilimi, Samar Da Ruwa, Da Makamashi
  • 2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su
  • Dalilin Gwamnatin Jihar Kuros Riba Na Raba Wa Manoma Taraktoci
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3