Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun ci gaba.

Tun daga wannan lokacin, kasar Sin ta ci gaba da yin sauye-sauye masu kiyaye muhalli, inda ta zama kasa mafi girma a duniya wajen kera batir na lithium da motocin masu amfani da lantarki.

Game da hakan, a yayin da ake tattaunawa da Jorge Moreira da Silvas, babban darektan ofishin kula da ayyuka na MDD, a wani shiri mai suna “Leaders Talk” da babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya gabatar a birnin Beijing, ya bayyana cewa, kokarin da kasar Sin ta yi da kuma sakamakon da ta samu wajen samar da makamashin da ake sabuntawa, da samun ci gaba mai dorewa, sun nuna wata alama mai kyau kuma mai inganci. Kuma wannan na da matukar alfanu ga batun dakile sauyin yanayin duniya.

Bugu da kari, Jorge Moreira da Silvas ya ce, ya yaba da hangen nesa da aniyar aiwatarwar da shugaba Xi Jinping ya nuna a fannin dakile sauyin yanayi da samun ci gaba mai dorewa. Gagarumin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arzikin mai kiyaye muhalli, musamman a fannin makamashin da ake sabuntawa da kuma sufurin ababen hawa masu amfani da wutar lantarki, ba wai kawai yana da muhimmanci sosai ga ita kanta kasar Sin ba ne, har ma ga duk fadin duniya.

A sa’i daya kuma, kasar Sin tana goyon bayan ra’ayin damawa da bangarori daban-daban, kuma tana taka rawa sosai a cikin ajandar samun ci gaba mai dorewa ta shekarar 2030, da kuma ajandar dakile sauyin yanayi ta duniya. Kazalika, ya ce ya yi imani da gaske cewa, kasar Sin za ta cimma burin samun daidaito tsakanin yawan hayakin da za ta fitar, da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin kafin shekarar 2060. (Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasar Sin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara

Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna

Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya

Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.

Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina

Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi October 31, 2025 Manyan Labarai Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai October 31, 2025 Manyan Labarai Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Isra’ila Tana Ci Gaba Da Hana Masu Jinya Zuwa Kasashen Waje Neman Magani Daga Gaza
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Za mu ci gaba da shirye-shiryen babban taronmu — PDP
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Bunkasar Fannin Kirkire-Kirkiren Fasahohi Na Sin Alheri Ne Ga Dukkanin Duniya Ba Barazana Ba