Pezeskkian Ya Ce: Suna Fatan Musayar Kasuwancin Tsakanin Iran Da Pakistan Ta Haura Dala Biliyan 10
Published: 2nd, August 2025 GMT
Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna fatan haɓakar musayar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ta haura dala biliyan 10
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bar birnin Tehran a wannan ranar Asabar din zuwa Islamabad na Pakistan a wata ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi masa.
Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya fitar kafin ya bar Tehran ya ce: “Zasu ziyarci Pakistan ne tare da tawaga bisa gayyatar da dan uwansu fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi musu.”
Ya kara da cewa: “Akwai kyakykyawar dangantaka, mai karfi da kuma zurfafa a tsakanin Iran da Pakistan. Wannan alakar ba ta shafi tattalin arziki, kimiyya, al’adu, masana’antu, da kan iyaka ba, akwai kuma alaka mai zurfi ta addini tsakanin Iran da Pakistan.”
Shugaban ya ci gaba da cewa: A yayin da ake ci gaba da tashe- tashen hankula a yankin da kuma cin zarafi na kafirci da zalunci kan kasar Ira da gwamnatin mamayar Isra’ila da Amurka suke yi, Pakistan na daga cikin kasashen da suka yi kakkausar suka ga wannan ta’addanci tare da bayyana cewa za ta ba da duk wani hadin kai da goyon baya don kiyaye yankin kasar Iran.
Pezeshkian ya kara da cewa: “Pakistan ta yi biye-biye a wannan fanni kuma ta gudanar da Sanya ido kan lamarin, abin da ake matukar yabawa.”
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba August 2, 2025 Jaridar Isra’ila Ta Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Sha Kashi A Yakin Gaza August 2, 2025 Dakarun Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 2, 2025 Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Afirka August 2, 2025 Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Juyayin Shahadar Haniya Bayan Shekara Guda Da Shahada August 2, 2025 MDD: HKI Ta Kashe Falasdinawa 1 Fiye Da 100 A Cikin Kwanaki 2 A Lokacinda Suka Karban Abinci August 2, 2025 Mutanen Kasar Siriya Sun Fito Zanga-Zanga Yin Allawadai Da Kissan Alawiyya A Kasar August 2, 2025 Shugaban Ansarullah: Amurka Tana Da Hannu A Ta’asar Da HKI Take Aikatawa A Gaza August 2, 2025 Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere August 2, 2025 Iran ta yi gargadi game da makircin Isra’ila na kawo cikas ga tsaron yankin August 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Iran da Pakistan
এছাড়াও পড়ুন:
Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi.
Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa.
Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya.
Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa.
Ya jaddada cewa gwamnati za ta tallafa musu da kayan noma na zamani da wuraran kasuwanci domin inganta tattalin arziki.
A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi na Jigawa ya yaba da samun Cibiyar Cigaban Karakara ta Pulse ta farko a Jigawa, yana mai cewa za ta kawo sauyi a harkar noma da rayuwar jama’ar karkara.
Haka zalika, shi ma Ministan Harkokin Waje, Yusuf Tuggar, ya ce haɗin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu zai taimaka wajen ci gaban tattalin arziki.
Shugaban ƙaramar hukumar Birnin Kudu, Alhaji Builder Muhammad Uba, ya jaddada goyon bayansa ga shirin Renewed Hope Agenda na Shugaba Tinubu tare da yabawa gwamnatin Namadi kan sauya fasalin noma a jihar.
Usman Muhammad Zaria