Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar suka kan hare-haren wuce gona da iri da Amurka ke kaiwa kan kasar Yemen

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan ci gaba da kai hare-haren da sojojin Amurka suka kai cikin sa’o’i 24 da suka gabata kan yankuna daban-daban na lardin Sana’a, da Sa’ada da Al-Jawf na kasar Yemen, inda suka lalata  kayayyakin more rayuwa da kuma muhallin al’ummar kasar.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya bayyana hare-haren da sojojin Amurka suke kaiwa Yemen a matsayin cin zarafi ga ‘yancin kan kasar, da kuma keta ka’idojin yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya da kuma dokokin kasa da kasa. Ya jaddada cewa wadannan hare-haren da ke kaiwa kan gidajen jama’a da kuma ababen more rayuwar al’umma, suna daga cikin laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana cewa: Babu wata tattaunawa da zata yi da Amurka a halin da take ciki na kare kanta

A yayin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare kan yankunan kasar Iran, a hukumance Iran ta bayyana rashin yiwuwar ci gaba da zaman tattaunawa da Amurka kan batun shirinta na makamshin nukuliya, tare da dora wa Amurka alhakin abin da ke faruwa kai tsaye.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Akwai hadin kai tsakanin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka wajen kai hare-hare kan kasar Iran domin rusa zaman tattaunawar nukiliya da haka ke bayyana kawar da duk wata magana ta hakikanin aniyar Amurka na samar da hanyar warware takaddamar Shirin Iran ta hanyar lumana.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa ci gaba da tattaunawa da Amurka a yayin da ake ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri yana gwada tsarin tattaunawar ba shi da ma’ana. Ya yi kakkausar suka ga matakin da hukumar ta IAEA ta dauka, inda ya yi la’akari da hakan a matsayin wani dalili na halasta cin zarafi a kan cibiyoyin nukiliyar Iran.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya bayar da umarnin binciken hare-haren Benuwe
  • Tinubu ya bayar umarnin binciken hare-haren Benuwe
  • Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Sun Kai Hare-Hare Kan Cibiyoyin Leken Asirin Isra’ila
  • Jami’an Tsaron Kan Iyakar Iran Sun Harbo Jiragen Masara Matuka 44 Na Sojojin H.K.Isra’ila
  • Iran Ta Cilla Makamai Kan HKI Da Rana A Karon Farko A Yau Lahadi
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Ce Ba’a Rufe Kofar Diblomasiyya Ba, Matukar HKI Ta Dakatar Da Kaiwa Kasar HKI
  • Martanin Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Kan Ta’addancin ‘Yan Sahayoniyya ya Shiga Rana Ta Biyu
  • Iran Ta Sanar Da Dakatar Da Tattaunawa Da Amurka A Wannan Lokaci Da Take Fuskantar Yaki Daga Isra’ila
  • Kungiyar Abokan Yarjejeniyar M.D.D Ta Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Da Isra’ila Ke Kai Wa Kan Iran
  • Iran ta sake kai hare-haren martani kan Isra’ila