Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza.

Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”.

“Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta.

Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza yayin da tattaunawar tsagaita wuta da Hamas ke fuskantar cikas.

Isra’ila ta ƙaddamar da mummuman yaƙi a Gaza sakamakon hare-haren Hamas a Kudancin Isra’ila ranar 7 ga Oktoban 2023 inda aka kashe kusan mutum 1,200 sannan aka yi garkuwa da mutum 251 a Gaza.

Fiye da mutum 60,000 aka kashe sakamakon yaƙin da Isra’ila ta ƙaddamar a Gaza tun lokacin, kamar yadda ma’aikatar lafiyar Hamas ta shaida.

‘Ƙawayen Isra’ila sun fara ƙaurace mata’: Ƙasashen duniya sun fara juya wa Netanyahu baya Yadda Birtaniya da ƙasashen duniya 28 suka caccaki Isra’ila kan yaƙin Gaza

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas

Ƙungiyar Hamas ta sake jadadda matakinta na cewa ba za ta taɓa ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu a yankin Gabas ta Tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin ƙullawa baya.

A halin da ake ciki yanzu haka ana wata tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba tsakanin Isra’ila da Hamas don ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60, da kuma sakin mutanen da ke riƙe a hannun ɓangarorin biyu.

A Talatar da ta gabata ne ƙasahen Qatar da Masar suka sanar da matakin ƙasashen Saudi Arabiya da Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasdinu, don tabbatar da dawamammen zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

To amma ƙasashen sun ce hakan za ta yiwu ne kawai idan har Hamas ta amince da ajiye makamai ga mahukuntan Faladinu da ke Ramallah.

A wata sanarwa da Hamas ɗin ta fitar ta ce bazata taɓa ajiye makamai ba, har sai ta tabbatar da samun ƴancin kan Falasɗinawa, da kuma ayyana birnin Ƙudus a matsayin babban birni.

Wannan ba shi ne karon farko da Hamas ke bayyana hakan a matsayin hanya ɗaya tilo ta ajiye makami ba, yayin da ita kuma Isra’ila ke cewa zata yi kowacce irin tattaunawa da Hamas ne bayan sun amince da ajiye makami.

A makon da ya gabata Firaministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya ce ba shakka samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu, shimfida hanya ne na rusa Isra’ila don haka ba zai taɓa aminta da hakan ba, kuma dole ne sha’anin tsaron yankunan Falasɗinu ya kasance ƙarƙashin ikon ƙasar sa.

Da yake caccakar matakin ƙasashen Birtaniya, Canada da kuma Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasɗinu biyo bayan halin da Isra’ila ta jefa al’ummar Gaza, ya ce wannan abu ne da Hamas ta janyo.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Kafa Kwamitin Tsaron Kasa Wanda Zai Kula Da Sabbin Matsalolin Tsaro
  • Gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Tana Kokarin Boye Barnarta A Zirin Gaza
  • Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba
  • Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas
  • Jamus ta soma jefa kayan agaji a Zirin Gaza
  • Jaridar Isra’ila Ta Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Sha Kashi A Yakin Gaza  
  • Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya
  • An Sake Kashe Wata Ɗalibar Jami’ar Ondo
  • Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa