An sace jaririya sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti
Published: 4th, August 2025 GMT
An nemi wata jaririya saoi kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin.
Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin.
Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙuraLamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin.
Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da mai gadi da wasu da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
Aminiya ta ruwaito cewa wasu masu neman na abinci a kusa da asibitin sun shiga ɗimuwa matuƙa dangane da faruwar lamarin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda na jihar, SP Sunday Abutu, ya ce yanzu haka akwai mutum huɗu da ake zargi da suka shiga hannu, “kuma suna bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka a binciken.”
Abutu ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Joseph Eribo, ya umurci sashen bincike na musamman (CID) da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da dawo da jaririyar cikin ƙoshin lafiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.
“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.
“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.
Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa da ke a sassan kasar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA