Kashi 40 Na Ƙananan Yara A Nijeriya Ke Fuskantar Barazanar Yunwa — Rahoto
Published: 2nd, August 2025 GMT
A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira).
Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da bai kamata a ce mai shekaru irinta na ciki ba.
Aisha Abdullahi ba ta iya yin kuka ba, domin babu ƙarfin halin yin hakan Mahaifiyarta, Maryam Abdullahi, tana girgiza ta a hankali a cinyarta, ta hada man gero mai ruwa da dakakken ganye a cikin wani ƙaramar roba. Abincin da suke ci a cikin kwana biyu.
Ta shaida wa LEAɗERSHIP Weekend cewa, “wani lokaci ta ci abinci, wani lokacin kuma sai dai ta yi ta kuka, a gaskiya babu isasshen abinci, babu kuɗi, babu taimako.”
An ba da rahoton cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na yara ƴan ƙasa da shekaru biyar a cikin al’ummomin da ke fama da talauci suna takure, girma da ci gaban ƙwaƙwalwarsu na lalacewa a koda yaushe saboda rashin abinci mai gina jiki. Wannan yana nufin miliyoyin yaran da aka hana su damarsu, na fama da ƙanƙancewar a jiki, a hankali, kuma su ne mafiya saurin kamuwa da cuta da kusanci da mutuwa.
A cewar masana, kalmar “rashin abinci” ba lallai ba ne yana nufin cewa yara ba sa cin abinci
Yana nufin ba sa cin abinci daidai gwargwado da ake buƙata don ci gaban da ya dace.
LEAɗERSHIP Weekend ta ruwaito cewa, shekarar 2023 zuwa 2024, Hukumar Kiwon Lafiya Ta ƙasa (NɗHS) ta bayyana cewa huɗu daga cikin yara goma ƴan Nijeriya ƴan ƙasa da shekara biyar (kashi 40) na fama da matsalar tsangwama, wanda ya ƙaru daga kashi 37 cikin 100 a shekarar 2018.
Bugu da ƙari, kashi 8 cikin 100 na yara a yanzu suna fama da rashin kulawa, kusan daya cikin kowane goma, idan aka kwatanta da kashi 7 cikin 100 a shekarar 2018.
A cewar binciken daya daga cikin kashi 22 cikin 100 na yara ƴan ƙasa da shekara biyar ba su da ƙiba tun a shekarar 2018, adadin da ya ƙaru zuwa kashi 25 cikin 100 a bayanan 2023/2024.
ƙididdiga mai ban tsoro
A duk faɗin ƙasar nan, yara, mata masu juna biyu, har ma da manya na fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki, kuma babu wani yanki da ya tsira.
A cewar wani rahoto daga Shirin Buƙatun Jin ƙai da Bayar da Agajin Gaggawa da OCHA ta shirya, kimanin yara ƴan ƙasa da shekaru biyar miliyan 2.55 na iya fuskantar matsalar rashin abinci mai gina jiki a bana.
daga cikin wadannan, ana sa ran miliyan daya za su fuskanci matsanancin rashin abinci mai gina jiki. Bugu da ƙari, kimanin mata da ƴammata masu juna biyu da masu shayarwa (PBWG) kusan 309,000 ne kuma ake hasashen za su fuskanci matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Masu ruwa da tsakin sun bayyana damuwarsu kan yadda ƙarancin abinci da tsadar kayan masarufi ke ƙara ta’azzara matsalar rashin abinci mai gina jiki a Nijeriya.
dangane da bayanan 2025 daga Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS), hauhawar farashin abinci a watan Mayu ya tsaya da kashi 21.4 bisa dari a duk shekara, ya ragu da kashi 19.52 cikin dari daga kashi 40.66 da aka samu a watan Mayun 2024.
Yayin da raguwar hauhawar farashin kayan abinci ta shekara ta bayyana, al’amura na rashin araha da wadatarsu sun zama manyan cikas ga gidaje da yawa.
A ƙoƙarinta na shawo kan matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shirin Nutrition-774 Initiatiɓe, da nufin farfaɗo da ayyukan cikin gida don inganta samar da abinci, lafiya, da abinci mai gina jiki a faɗin Nijeriya. An tabbatar da tsarin sadarwa na ƙasa akan ingantaccen abinci mai gina jiki don tallafa wa manufofin da suka dace da ƙoƙarin majalisu.
A baya-bayan nan, kwamitin kula abinci na majalisar ya kira taron ƙasa kan abinci da samar da abincin kansa. Taron ya tattaro masu ruwa da tsaki da dama, da suka hada da ƙwararru daga muhimman sassa, ma’aikatu, sassa, da hukumomi da rundunonin soji, da hukumomin tsaro, da sarakunan gargajiya, da ƴan majalisar wakilai, da ƴan majalisar dokokin jiha, da kuma abokan ci gaba.
da yake bayyana buɗe taron, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, ya yi kira da a samar da tsarin yaƙi da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki a ɓangarori da dama da kuma ƙarfafa abinci da tsaron ƙasa a faɗin ƙasar.
da yake jawabi a madadin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, mataimakin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa (Ofishin mataimakin shugaban kasa), Sanata Ibrahim Hadejia ya bayyana cewa sabon shirin N-774 da aka ƙaddamar an yi shi ne musamman domin samar da tasiri kai tsaye a sassan ƙasar nan da ba a yi wa hidima ba kuma ba a mantawa da su ba.
“Mun shaida yadda aka kafa ƙungiyar ƴan majalisu ta ƙasa kan samar da abinci, tare da kwafin takardar zaman wannan kwamiti a dukkanin majalisun dokokin jihohi 36. Wannan ya nuna wani gagarumin ci gaba da ba a taɓa ganin irinsa ba a cikin ayyukanmu na majalisar, amma dole ne mu gane cewa dalilin da ya sa muka taru a yau ba wai don murna ba ne,” in ji shi.
A jawabinsa na maraba, shugaban kwamitin kula da abinci na majalisar, Hon. Chike Okafor, ya bayyana cewa majalisar na yin tarukan gina dabaru don ƙara fahimtar asalin lamarin da yanayin ƙalubalen abinci mai gina jiki da abinci da ke fuskantar Nijeriya.
Ya bayyana cewa, “Wannan zai ba mu damar ci gaba da sa ido kan duk abubuwan da suka shafi abinci da abokan aiki, amma ba’a iyakance ga tsarin Majalisar ɗinkin ɗuniya, Bankin ɗuniya, ƙungiyoyi masu zaman kansu na ƙasa da ƙasa da na ƙasa ba, kuma, haka abin yake a gwamnati matakin tarayya, jihohi, da ƙananan hukumomi.
Okafor ya ƙara jaddada cewa aikin farko na gwamnati shi ne tabbatar da tsaro, musamman a yankunan da ke da matuƙar muhimmanci wajen samar da abinci. Ya ƙara da cewa, “ɗole ne mu tabbatar da wuraren da suka hada da Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Arewa ta Tsakiya, da ma Kudu maso Gabas, wadanda duk suna da matuƙar muhimmanci ga samar da abinci a Nijeriya.”
da yake wakiltar gidauniyar Gates, Ekenem Isichie, ya yi kira ga Majalisar ɗokoki ta ƙasa da ta himmatu wajen yin amfani da aikin sa ido na doka don tabbatar da cewa cibiyoyin kula da lafiya a matakin farko a faɗin ƙasar nan suna isar da sahihan bayanai da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga iyaye mata da yara.
Ya kuma jaddada cewa dole ne Nijeriya ta jagoranci nahiyar Afirka wajen rage mace-macen jarirai da mata masu juna biyu, da kawo ƙarshen rashin abinci mai gina jiki, da inganta samar da abinci.
A nasa jawabin, daraktan ƙungiyar Global Alliance for Improɓed Nutrition (GAIN), ɗr. Michael Ojo, ya bayyana sauyin yanayi, rashin tsaro da yunwa, da ƙaruwar al’ummar Nijeriya ya zarce samar da abinci a matsayin manyan matsalolin rashin abinci mai gina jiki.
Ya bayyana cewa, “Muna samar da abinci da yawa, amma adadin mutanenmu na ƙaruwa da sauri fiye da yadda ake noman abinci, wannan yana haifar da matsin lamba ga wadatar abincin da ake samu, abin takaici, a cikin ƴan shekarun nan, ƙarfin samar da kayayyaki ya ragu saboda rashin tsaro da kuma dalilai kamar sauyin yanayi.”
ɗokta Ojo ya jaddada cewa samar da abinci ƙalubale ne, amma samar da abinci mai gina jiki wani abu ne. “Lokacin da muka tattauna matsalar rashin abinci mai gina jiki, dole ne mu yi la’akari da rashin abinci da abinci mai gina jiki.
da gaske muna fuskantar ƙalubale biyu. ɗon haka ne wannan shiri na kwamitin kula da abinci mai gina jiki da samar da abinci na majalisar wakilai ke da matuƙar muhimmanci. Wannan batu ba alhakin gwamnatin tarayya kadai ba ne; yana buƙatar yunƙurin haɗin gwiwa a dukkan matakai uku na gwamnati.”
A cewar dakta Ojo, yayin da gwamnatin tarayya za ta iya tsara manufofi, ainihin tasirin yana faruwa a matakin jihohi da ƙananan hukumomi.
“Akwai matsaloli da yawa da ke buƙatar mafita da yawa, amma haɗin gwiwa yana da mahimmanci don samar da wadannan hanyoyin ingantattu, wasu sun ce manoma ba sa amfani da hanyoyin noma yadda ya kamata, amma yawancin noman mu har yanzu ya dogara da ruwan sama, tare da yawancin gonaki ba sa ban ruwa.
Wannan wani ɓangare ne na ƙalubale, amma kuma dama. Misali, ƙarfafa wa mata, wadanda ke samar da wani kaso mai tsoka na al’ummar noma, ta hanyar samar musu da filayen noma don ƙananan sana’o’i na iya kawo canji,” in ji shi.
A halin da ake ciki kuma, daraktan Cibiyar Samar da Abinci Mai Gina Jiki ta ƙasa da ƙasa, ɗrakta Osita Okonkwo, ya jaddada cewa samar da abinci mai gina jiki ya kasance mai matuƙar muhimmanci ga lafiyar al’umma a Nijeriya.
Ya ƙara da cewa, Nijeriya kamar ƙasashe da dama, na fuskantar ƙalubalen rashin abinci mai gina jiki da ba wai kawai ya shafi lafiya da walwalar al’ummarta ba, har ma da hana ci gaban tattalin arziki, ci gaban al’umma, ci gaban kyawawan halaye, da kuma ci gaban ƙasa baki daya.
A cewar dakta Okonkwo, sanya hannun jari a fannin abinci mai gina jiki, saka hannun jari ne ga walwala da ci gaban al’umma, saboda rashin abinci mai gina jiki ya kasance babban ƙalubalen kiwon lafiyar al’umma a Nijeriya. Ya kuma buƙaci masu ruwa da tsaki da su hada kai wajen gina Nijeriya mai cike da ƙoshin lafiya, da wadata, ƙasar da kowane dan kasa zai samu ci gaba, ya kai ga ga cimma burinsa, da rayuwa cikin walwala da abinci mai gina jiki.
Ya ƙara da cewa “ɗole ne mu ƙarfafa haɗin gwiwa da kuma ware isassun kasafin kuɗi a sassa daban-daban kamar aikin gona, kiwon lafiya, ilimi, da kuma kare zamantakewar al’umma don samar da cikakkiyar hanya ta abinci mai gina jiki,” in ji shi.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin kiwon lafiyar jama’a da mai kula da harkokin abinci na ofishin mataimakiyar shugaban ƙasa, Uju Rochas Awuka, ta jaddada buƙatar gaggauta inganta harkokin kiwon lafiya, da kiyaye abinci mai gina jiki a kan manufofin siyasa, da ba da damar shiga tsakani a kan lokaci. Ta bayyana ƙwarin gwiwar cewa kowane ƙalubale na samar da mafita.
Uwargida Awuka ta bayyana shirin Nutrition 774 Initiatiɓe da hukumar kula da abinci ta ƙasa (NCN) ta ƙaddamar kwanan nan a matsayin shirin da aka tsara domin hada kan manyan masu ruwa da tsaki, da ƙarfafa haɗin kai a ɓangarori da dama, da inganta kudaɗe da tabbatar da gaskiya, da kuma magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a ƙasar nan yadda ya kamata.
da aka tambaye shi yadda za a sauya yanayin rashin abinci mai gina jiki, Hon. Chike Okafor, shugaban kwamitin majalisar kan harkokin abinci ya bayyana cewa:
“Abu ne mai sauƙi ƙwarai. A yi duk abin da zai yiwu don tabbatar da samun abinci da araha. Wadannan biyun, samuwa da araha, suna da mahimmanci.”
“Yaya za mu yi magana game da abinci mai gina jiki yayin da abinci ba zai iya isa ba? Abinci mai gina jiki da samar da abinci su ne ɓangarori biyu na tsabar kuɗin. Ba za mu iya magance daya ba tare da dayan ba,” in ji shi.
LEAɗERSHIP Weekend ta nanata tambayar cewa: Me ya sa rashin abinci mai gina jiki ke ci gaba da kasancewa cikin kashi 40 cikin 100? Wane ne ke da alhakin kasafin kuɗin da ba a kashe ba, da wuraren da ba su da kayan aiki, da kuma iyaye mata da ba a sani ba?
Wani lamarin gaggawa, yara nawa irin Aisha Nijeriya za ta yi asara kafin ta dauki mataki na hakika, ba wai kawai daukar alƙawura ne abin nufi ba, a samar da canji mai ma’ana.
A cikin al’ummar da ke cike da hazaƙa, babu wani yaro da za a yanke masa hukuncin girma da yunwa kuma a ce zai ci gaba. Yanzu ne lokacin yin aikin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Yara Yunwa matsalar rashin abinci mai gina jiki matuƙar muhimmanci ya bayyana cewa Ya bayyana cewa samar da abinci na majalisar jaddada cewa kiwon lafiya masu ruwa da tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
GORON JUMA’A 01-07-2025
Tarihin dan’adam ya nuna yadda ƙabilu daban-daban, ke nuna ƙin amincewa da auratayya ta haɗin gambiza a tsakanin ƴaƴansu da wasu ƴan ƙabilar da ba tasu ba. Hatta a cikin ƙabila daya ana samun wannan nuna wariya, tsakanin dangi, ko masu hali da talakawa. Hatta a tsakanin addini daya, bambancin aƙida ko fahimta na sa a hana masoya aure, ko da kuwa sun cancanci kasancewa tare.
Kodayake zamani na sauyawa, ilimi na ƙara yawa, mutane na dada samun wayewa kan ƴancin su, amma a wurare da dama aure daga wata ƙabila zuwa wata, abin kyama ne. Wasu na son ko da za a auro daga wata ƙabila to, ya kasance ba auren fari ba ne. Ko kuma ya kasance mai bin addini daya da su ne. Mutane suna son ƙabilar su ta ƙara yawa, al’adarsu da tarbiyyar su ta cigaba da wanzuwa, don kada tarihin su da harshen su na gado ya ɓace. Sai dai hakan na nuna ƙuntatawa ga matasa da wadanda suke son juna, yana tauye musu ƴanci da haƙƙoainsu.
Sunana Haj. Binta Umar Ahmad, daga Limawa:
Gaskiya ne cewa wasu ƙabilu ko al’ummomi, na iya samun abubuwan da suka fi so ko al’adu da ke tasiri a kan yadda ake gudanar da aure. Wadannan na iya kasancewa daga ƙarfafa aure a cikin ƙabilar zuwa samun takamaiman al’adu ko tsammanin al’adu. Wadannan al’adu sau da yawa suna fitowa daga sha’awar kiyaye gadon al’adu, kula da haɗin kan al’umma, ko kuma tsayawa kan imanin addini. ɗuk da haka, yana da muhimmanci a tuna cewa zaɓuɓɓuka da ra’ayoyi na mutum na iya bambanta sosai a cikin kowace ƙungiya.
Amfanin su ne; yin aure a cikin ƙabila daya yana taimakawa wajen kiyaye al’adu, harsuna, da ayyuka, tabbatar da isar da su ga tsararraki masu zuwa. Yana iya ƙarfafa haɗin gwiwar al’umma da haifar da jin daɗin zama a tsakanin ƴan ƙabila daya. Ma’aurata daga ƙabila daya sau da yawa suna da dabi’u, da al’adu iri daya, wanda hakan zai iya haifar da raguwar rikice-rikice a cikin aure. Iyalai da al’ummomi na iya samar da hanyoyin sadarwa masu ƙarfi ga ma’aurata, tare da taimaka musu su magance ƙalubale tare.
Kuma matsalolin sune ƙuntata aure zuwa cikin rukuni na iya iyakance zaɓi na sirri da damar soyayya da abota. Wannan al’ada na iya haɓaka tunanin ‘mu da su’, wanda zai haifar da wariya ko kyama ga wadanda suka fito daga wurare daban-daban. Sannan yana kawo rigingimun Al’adu, aure tsakanin ƙabilu na iya haifar da rashin fahimta a wasu lokuta ko rigima saboda bambancin al’adu da abin da ake tsammani.
Mutanen da suka yi aure a wajen ƙungiyarsu na iya fuskantar kyama ko rashin yarda daga al’ummarsu. Wadannan abubuwan na iya bambanta sosai dangane da ƙayyadaddun ƙabila da mahallin da suke rayuwa.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To, haƙiƙa yin hakan kuskure ne domin shi arziƙi nufi ne na Allah, kuma wasu sai bayan auren ma suke samun arziƙin, amma ba laifi bane don iyaye sun zaɓawa ƴaƴan su mata miji domin hakan zai taimaka wajen samun nagari. To, batun ƙabilanci sam-sam bai dace ba, domin ba a duban ƙabila wajen bada aure ko neman aure, ana duba addini ne, dabi’a dama nasaba.
Amma ba laifi bane iyaye su taya ƴaƴan su, zaban mijin nagari. Eh tabbas akwai hakan yana haifar kiyayya a tsakanin al’umma ko ƙabila, wanda ka iya jawo zaman doya da manja, a ɓangaren zaɓan mijin mai hali kuma irin wannan dabi’a tana rage darajar iyaye dama gidan a idon duniya. To, shawara ta a nan ita ce wajen zaɓen mijin a fifita zaɓen mai addini, dabi’a mai kyau dama nasaba akan ƙabilanci ko mai abun hannu, su kuma su dage wajen yi wa ƴaƴan su addu’ar samun mazaje nagari ba wai masu dukiya kadai ba, domin bawa Allah zaɓi zai taimaka wajen samun nagari.
Sunana Rahma Adamu Ahmad, daga Jihar Kaduna:
Hakan yana nuna wariya da rashin adalci. Auren soyayya da fahimta ya fi inganci fiye da wanda aka gina kan ƙabilanci ko dukiya. Amfani. A wasu lokuta iyaye na kallon tsaron ƴaƴansu ne da bin wannan hanya, musamman ta fuskar kuɗi. Rashin amfani: Yana hana soyayya ta gaskiya, yana hana haɗin kai da gina al’umma mai ƙarko. Kiyayya da rashin jituwa tsakanin ƙabilu,
Hana cigaban al’umma ta hanyar hada jini, Tilasta wa yara auren da ba sa so, wanda ke janyo matsaloli cikin gida, Rasa damar dogaro da kai idan an hana matasa fita neman arziƙi. A bawa yara ƴanci wajen zaɓen abokin rayuwa, matuƙar yana da tarbiyya da nagarta. A riƙa duba halayya da imani, ba ƙabila ko dukiya ba. Kuma a koya wa yara darajar aiki da nemowa da kansu.
Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk:
dalilin da ya sa wasu ƙabilun ba sa barin auratayya a tsakankaninsu da wasu ƙabilun shi ne; mafi akasari saboda bambamce-bambamce na addini da al’ada da kuma yare tare da riƙe sirrin junansu, haka kuma sun zaɓawa yaransu masu kuɗi ne domin kaucewa talauci ga yaran nasu mata dama jikokinsu, hakan tasa ba sa yadda yaransu mata su auri talakawan cikinsu.
Sannan ba sa barin talakawan cikin nasu su auri wasu matan da ba ƙabilinsu bane ba. Sannan sukan alaƙanta hakan da sabo ko sabawa al’ada da kuma tarihi ta yadda talakawan cikinsu za su kasance masu yi wa dokokin ƙabilar su biyayya don auren mata ƴaƴan talakawa dake a cikin ƙabilarsu.
Amfanin yin hakan zai haifar da danƙon zumunci da kuma ɗorewar al’ada ta ƙabilancinsu. Sannan sai tabbatar da ɗorewar cigaban ƙabila, haka ma rashin amfanin hakan zai sa talakawan ƙabilar su cigaba da kasancewa cikin talauci sannan hakan zai iya haifar da rashin jituwa, rashin zaman lafiya da haɗin kai tare da rashin fahimta a tsakanin ƙabilu daban-daban. Matsalolin da ka iya samuwa sun hada da; rashin samun cigaba, rashin chanzawar matsayi, rashin tsaro, rashin zaman lafiya, rikicin ƙabilanci, cin amanar juna, rashin aikin yi, talauci da fadawa cikin mawuyacin hali tare da sarewa rayuwa ko fadawa amfani da miyagun kwayoyi da safararsu.
Shawarar ta hada da su tuna cewa babu abin da hakan zai haifar face rashin zaman lafiya da cigaba sannan su kasance masu tunanin cewa duka mutanen duniya daya ne babu wanda ya fi wani sai mafi tsoran Allah da kuma mafi yin biyayya a gare shi da kuma dokokinsa, su kuma sani cewa Allah ne mai bada arziƙi da talauci kasancewar mutum a cikin daya jarabawar sa ce, kuma ni’imar sa ce don zai iya bawa mutum arziƙi ya kuma kwace ya bawa mutum talauci. Haka kuma zai iya bawa mutum talauci, ya kuma kwace ya bashi arziƙi, duk hakan cikin ni’imominsane.
Sunana Princess Fatima daga Gomben Najeria:
Abin sai godiya wanda abu ne ada ana yin shi dan gudun rasa yayaye, da kuma gaba tsakanin ƙabilu. Amma a yanzu ya zamo, kamar kyama ma ake yi wanda sam bai dace ba. Iyaye suna da damar zaɓawa yaransu mata ko mazaje, amma ba ta hanyar tilastawa ba, su kafe lallai sai mai kuɗi zai auri ƴar su ko sarauta ko dai abu madangancin dukiya, wasu sun kyamaci talauci duk da talauci kam wallahi abun gudu ne shi talakan ma ya yi arziƙi aka kira talauci sai ya juya dan tsoron kar ta sake biyo shi, yawanci zuriya in dai an ga wani ya yi dukiya to, fa! fatansu kawai kar ya auro wata a waje wai da na waje ya ci gwara na ciki ya ci ko cikin ɓacin rai, Allah ya kyauta.
Abu ne mara kyau abar kowa ya zaɓi rabonshi aure na Allah ne mai kuɗi da talaka duk bayin Allah ne, haka za ka iya aurawa ƴar ka mai kuɗin ya talauce ko ka aura mata talaka ya yi arziƙi. Amfaninshi kam shi ne haɗin zumunci kawai bayan shi komai sai kwadayi da burin komai su kar ya fita ya ƙare a cikin gida su ya su. Matsaloli kam ai barkatai ne sai dai a faɗi kadan, kamar zaman dole da-na-sani da tsayiwar zuci kar arziƙin ya mulmulce. Haka auren ƙabilu wani lokacin da-na-sani ne dan al’ada ba ta zo daya ba ra’ayi ba dole ya zamo daya ba, wani lokacin kuma haɗin auren tsakani kan iya kawo ƙarin zaman lafiya ga a’lumma da haɗin kai. ɓangaren auren masu kuɗi buri da kwadayi, ta auratayya tsakanin ƙabilu kuma zaman lafiya ko akasinsa.
Shawara kowa ya san daidai a bita kawai a zauna lafiya, a kuma daina kyamatar talaka, dan shi kan shi talaka ba ya son talauci, sunanan kyamatar ƙabila ko jahiltarsu ba kyau indai akwai fahimtar juna to, magana ta ƙare.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), JIhar Kano:
Son kai ne kawai. Rashin amfanin hakan yana rage ƙaruwar zumunci da kawo haɗin kai cikin al umma. Amfanin hakan kuma zai ƙara yawan dangi cikin al’umma. Kadan daga cikin irin matsalolin akwai haddasa gaba da kin yarda da juna da kuma haddasa fadace-fadace. Shawarata a nan ita ce su daina, domin ko irin taken da ake wa nahiyar mu ta Africa da kuma ita kanta ƙasata wato Nigeria shi ne ‘Uwa daya Uba daya’ mu daure mu cire son zuciya da son kai musamman mu ƴan yankin arewa mafiya yawanmu Hausa Fulani ne kuma musulmi. Allah kasa mudace.
Sunana Hafsat Sa’eed daga Jihar Naija:
Shawarata a nan ita ce, yin magana tare da abokin tarayya game da bambance-bambancen al’adu, gudun tsammanin rikice-rikice masu yuwuwa. Su kasance da sha’awar al’adun abokin tarayya da al’adunsu. Yin tambayoyi ko karanta littattafai ko kallon shirye-shiryen bidiyo, da ƙoƙarin koyo gwargwadon iyawa domin samun zaman lafiya da juna. Wannan yana taimakawa wajen cike giɓin al’adu, ƙarfafawa iyalansu gwiwa don sanin juna, wannan yana taimakawa wajen haɓaka fahimta da yarda. Su yi haƙuri da junansu ya yin da suke da bambancin al’adu, dabi’u, da sauran abubuwa daban-daban.
Sunana Hassana Yahaya Iyayi (Maman Noor) daga kano:
Allah daya, gari bamban.
Gaskiya wannan abin na su sai addu’a, ko da yake al’adar su ce ko to ai zabin Allah dai shi ne gaba da komai da fatan samun nagari ba kuɗin ba. Ai babu wani amfanin bin wannan tsarin nasu sam ai bin su sai su kam wallahi. Matsaloli sosai za su sa yaransu fadawa kungiyoyin asiri da fashi da makami, garkuwa da mutane da sauransu, Allah ya kyauta amin. Su yi haƙuri da abin da Allah ya ba su mai kuɗin ko talaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp