An sace jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta a asibitin Ekiti
Published: 4th, August 2025 GMT
An nemi wata jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin.
Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin.
Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙuraLamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin.
Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da mai gadi da wasu da ake zargi zuwa ofishin ’yan sanda domin ci gaba da bincike.
Aminiya ta ruwaito cewa wasu masu neman na abinci a kusa da asibitin sun shiga ɗimuwa matuƙa dangane da faruwar lamarin.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sanda na jihar, SP Sunday Abutu, ya ce yanzu haka akwai mutum huɗu da ake zargi da suka shiga hannu, “kuma suna bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka a binciken.”
Abutu ya ce Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Joseph Eribo, ya umurci sashen bincike na musamman (CID) da su gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da dawo da jaririyar cikin ƙoshin lafiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai kai jihar ga tudun mun tsira.
Lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Honorabul Aminu Sani Jaji, ya gode wa al’ummar Zamfara bisa nuna kauna da yarda da suka yi mishi, inda ya sha alwashin yi musu sakayya akan haka.
“Dukkanin abubuwan da muke yi muna yin su ne domin al’umma, kuma jama’ar nan ita taga dacewa ta da in tsaya mata takarar gwamna, babu shakka na amince zan amsa kiran da suka yi mini domin fitar da Jihar Zamfara daga mawuyacin halin da take ciki “ in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp