Borrell: Rashin tabuka komai daga Turai ya karfafa gwiwar Isr’ila wajen aikata laifuka
Published: 5th, August 2025 GMT
Tsohon jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Joesp Borrell, ya yi gargadi game da ci gaba da rashin taka rawar gani daga bangaren kasashen Turai dangane da ayyukan cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi, yana mai cewa irin wannan rashin hankali ya sa kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta zama abokiyar tarayya a cikin laifukan da Isra’ila ke aikatawa.
Joesp Borrell ya bayyana hakan ne a cikin wani fashin baki wanda aka buga a cikin jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya.
“Wadanda ba su yi aiki ba don dakatar da wannan kisan kiyashi da kuma keta dokokin kasa da kasa, duk da cewa suna da ikon yin wani abu kan hakan, to tabbas suna da hannu a cikin wadannan laifuka,” in ji shi.
Borrell ya ba da misali da yakin kisan kiyashi da gwamnatin kasar Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta kaddamar tun daga watan Oktoban 2023 a kan zirin Gaza wanda ya zuwa yanzu ya lakume rayukan Falasdinawa akalla 60,332, galibi mata da kananan yara, a matsayin babban misali.
Tsohon jami’in ya kuma yi tsokaci game da harin da ake kaiwa a matsugunan Falastinawa wa a kullum a yammacin gabar kogin Jordan.
EU, ta sha tabbatar da cewa ita ce babbar abokiyar kasuwanci ta gwamnatin Isra’ila, kuma babban mai saka hannun jari, kuma babban mai samar da makamai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka UNICEF: Akalla yara 28 ne ke mutuwa a kowace rana a Gaza sakamakon harin Isra’ila da yunwa August 5, 2025 Baghaei : Ziyarar Pezeshkian a Pakistan ta bude wani sabon Shafin alaka August 5, 2025 Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump August 5, 2025 Hamas ta musanta kalaman Witkoff game da batun mika makamanta August 5, 2025 Araqchi: Namijin kokarin al’ummar Iran abin yabawa ne August 4, 2025 Khatibzadeh: Iran ba za ta amince da saryar da hakkokinta ba a duk wata tattaunawa da Amurka August 4, 2025 Rahotonni: Agajin Jin kai Da Ake Jefawa Ta Sama A Gaza Ba Shi Da Tasiri August 4, 2025 Wa’adin Da Shugaban Amurka Ya Gindaya Na Kawo Karshen Yaki A Ukraine Ya Karato Ba Tare Da Alamun Karewarsa Ba August 4, 2025 Sojojin Somaliya Sun halaka Mayakan Kungiyar Al-Shabab Fiye Da Hamsin A Kudu Maso Yammacin Mogadishu August 4, 2025 Pakisatan: Iran Ce Madogara Ga Al-ummar Musulmi August 4, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
ICC : Rikicin Sudan kan Iya kasancewa Laifukan yaki da cin Zarafin dan Adam
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) ta nuna damuwa kan rahotannin baya-bayan nan na “kasha kashe, fyade, da sauran laifuka” da Rundunar Taimakon Gaggawa (RSF) ta aikata a yankin El-Fasher, na Sudan, tana gargadin cewa wadannan ayyukan na iya zama “laifukan yaki da cin zarafin bil’adama.”
“Irin wadannan ayyuka, idan aka tabbatar da su, na iya zama laifukan yaki da cin zarafin bil’adama a karkashin yarjejeniyar Roma,” in ji sanarwar da Ofishin Mai Gabatar da Kara na ICC, ya fitar.
A cewar sanarwar, wadannan ayyukan sun lalata dukkan yankin Darfur tun daga watan Afrilun 2023,” ranar da aka fara yaki tsakanin sojojin Sudan da Rundunar Taimakon Gaggawa.
A cikin sanarwar, Ofishin Mai Gabatar da Kara ya tuna cewa, a karkashin kuduri na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 1593 (2005), Kotun hukuntan manyan laifuka ta Duniya (ICC) tana da hurumin gurfanar da masu hannu a laifukan da aka aikata a rikicin da ke ci gaba da faruwa a Darfur.
Ta kuma bayyana cewa Ofishin yana binciken laifukan da aka aikata a Darfur tun bayan barkewar rikici a watan Afrilun 2023.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne, Rundunar (RSF) ta kwace iko da garin El-Fasher tare da aikata kisan gilla ga fararen hula, a cewar kungiyoyin cikin gida da na kasa da kasa.
Rikicin da barke a ranar 15 ga Afrilu, 2023, tsakanin sojojin Sudan da RSF ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin 20,000 tare da raba mutane sama da miliyan 15 da muhallansu, a cewar Majalisar Dinkin Duniya da majiyoyin cikin gida.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya saboda Dalilan Tsaro November 4, 2025 Hizbullah Ta yi Gargadin Mayar Da Martani Idan isra’ila Tayi Kokarin Kai Samame Ta Kasa November 4, 2025 Iran Tayi Maraba Da Kalaman Da Hukumar IAEA Kan Shirinta Na Nukuliya November 4, 2025 Prime Ministan Sudan Yayi Gargadi Game Da Aikewa Da Dakarun Tabbatar Da Zaman Lafiya Kasar November 4, 2025 Ribadu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya kan barazanar Trump November 4, 2025 Mutum Daya Ya Yi Shahada Sanadiyyar Harin Sojojin HKI A Kudancin Lebanon November 3, 2025 Kungiyar Likitocin Kasar Sudan: Rundunar RSF Tana Garkuwa Da Dubban Fararen Hula A Al-Fasha November 3, 2025 An Sami Tsaikon Sauka Da Tashin Jiragen Sama A Tanzania Saboda Rikicin Zabe November 3, 2025 Falasdinawa Biyu Sun Yi Shahada A Nablus Da Khalil November 3, 2025 Jagora: Sabanin Jamhuriyar Musulunci Da Amurka Daga Tushen Manufa Ne Ba Sama-sama Ba November 3, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci