An kama dilallan ƙwaya 28 a cikin barikin sojoji a Kaduna
Published: 4th, August 2025 GMT
Sojoji sun kama wani gungun dillalan miyagun ƙwayoyi 28 a cikin Babban Barikin Sojoji na Jaji da ke Jihar Kaduna.
Dilolin ƙwayar da aka kama sun haɗa da mata 11 da maza 18, lamarin da ya haifar da fargaba gane da yaɗuwar ɗabi’ar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyalan sojoji da fararen hula da ke makwabtaka da su.
Kakakin Cibiyar Horas da Mayaƙan Ƙasa da aka barikin, Kyaftin Olusegun Abioye, ya bayyana cewa sojoji sun gano cibiyar dilolin ƙwayar ne a unguwanni Railway da Unguwar Lauya da ke cikin harabar barikin na Jaji.
Ya ƙara da cewa an kama shugabannin masu fataucin miyagun ƙwayoyi guda aƙalla guda 15 a waɗannan unguwanni biyu, kuma an miƙa duk waɗanda aka kama ga Hukumar Yaƙi da Ta’ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA).
NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a TarabaYa bayyana haka ne a yayin rangadin da ya jagoranci manema labarai yana mai ƙaryata labaran da ke cewa sojoji sun rusa unguwannin biyu.
Kyaftin Olusegun Abioye ya ƙara da cewa duk da cewa yankunan irinsu Unguwar Alasan da Unguwar da Unguwar Alhaji da Unguwar Aboki, da ke cikin harabar barikin suna taimaka wa sojoji da wasu ayyuka; amma duk da haka suna addabar al’ummar barikin sojojin da wasu matsaloli.
Ya bayyana cewa unguwanni sun riga sun haɗe da barikin sojojin wanda babbar cibiyar horon soji ce, kuma kusancin nasu kan jefa mazaunansu cikin mummunan haɗari a lokacin da sojoji ke atisayen amfani manyan makamai.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Barikin sojoji Dillalan ƙwaya ƙwayoyi Unguwar Lauya barikin sojoji
এছাড়াও পড়ুন:
’Yansanda Sun Kama Mutane 9 Kan Yin Ƙaryar Sace Su A Jihar Neja
A lokacin gudanar da bincike, an samu layin waya guda 21 da takardun rijistar layi guda 29 a wajen Suleiman, wanda ya ce yana harkar rijistar layin ne.
Ya amsa cewa shi ne ya bai wa waɗanda “aka sace” waya da lambar da aka yi amfani da ita wajen neman kuɗin fansa.
Binciken ya nuna cewa waɗannan mutanen suna cikin wani tsari na zamba wanda ake kira da Ponzi.
An kuma gano cewa ɗaya daga cikinsu ya haɗa baki da wanda aka ce an yi garkuwa da shi don su karɓi kuɗi daga sauran abokan harkarsu.
SP Abiodun ya ce bincike ana ci gaba da bincike domin kama sauran waɗanda ke da hannu a lamarin, yayin da aka riga aka gurfanar da waɗanda aka kama a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp