Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-08-04@12:56:09 GMT

Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Shirin Dashen Bishiyoyi

Published: 4th, August 2025 GMT

Gwamnan Kano Ya Kaddamar da Shirin Dashen Bishiyoyi

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da gurbacewar kasa, zaizayar kasa da sauran kalubalen muhalli.

 

 

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren shirin dashen itatuwa, inda za a dasa itatuwa miliyan 5 da rabi a fadin jihar, wanda aka gudanar a karamar hukumar Makoda.

 

 

 

Ya ce babban makasudin wannan shirin shi ne a magance dimbin kalubalen muhalli da ke addabar al’ummar jihar Kano.

 

 

Gwamna Yusuf ya jadadda cewa wadannan kalubalen na haifar da babbar matsala ga al’umma.

 

 

Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta bayar da duk wani tallafin da ya dace don shayar da ‘ya’yan itatuwan, ta yadda za su yi girma da kuma cim ma burin da aka yi niyya. Wannan tallafi yana da mahimmanci don nasarar shirin.

 

 

Ya bukaci dukkan shugabannin kananan hukumomi 44, shugabannin gargajiya, da jami’an ci gaban al’umma (CDOs) da su sanya hannu a cikin wannan shirin, inda ya ce shigar su na da matukar muhimmanci wajen cimma manufofin shirin.

 

“Idan aka kula da kyau itatuwan da aka dasa ta wannan shiri za su taka rawar gani wajen magance sauyin yanayi da batutuwan da ke da alaka da hakan. Hakan ya yi dai-dai da manyan manufofin jihar Kano.”

 

Kwamishinan Muhalli, Dr. Dahiru Mohammad Hashim, ya yaba da kudurin Gwamna Yusuf na tallafawa kokarin ma’aikatar wajen dakile matsalolin muhalli.

 

Sarkin Dawakin Mai Tuta Alhaji Mohammad Bello Abubakar, wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammad Sanusi II ya jaddada goyon bayan Masarautar kan shirin dashen itatuwa.

 

 

Taron ya gabatar da bayar da kyautuka ga mutanen da suka bayar da gudunmawa sosai wajen tallafawa al’ummarsu.

 

 

Wannan amincewa yana aiki azaman abin ƙarfafawa ga wasu don shiga cikin ayyukan muhalli.

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Itatuwa

এছাড়াও পড়ুন:

Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar

Firayim Ministan Senegal Ousmane Sonko ya sanar da wani sabon shirin farfado da tattalin arzikin kasar, inda ya yi alkawarin samar da kudi “90% na aiwatar da wanann shirin ta hanyar albarkatun cikin gida da kuma kauce wa karbar bashi.

Sonko ya bayyana haka ne a lokacin da ake gabatar da wannan shiri a Dakar babban birnin kasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito. Ya ce: “Za mu nemi haɗin kan abokan hulɗa na waje ne kawai a ɓangaren sake amfani da kadarorinmu na cikin gida.”

Ya kara da cewa “dole ne a yi amfani da kuma tattara albarkatun cikin gida don samar da mafi yawan kudaden da kasa take bukata.”

Shirin wanda ke da nufin daidaita harkokin kudi na kasar da ke yammacin Afirka, wadda ta fara hako mai da iskar gas a bara, ya zo ne a daidai lokacin da Senegal ke fuskantar kalubalen kudi da kuma tarin basusuka.

Kasar Senegal dai na fama da boyayyen bashi na biliyoyin daloli daga gwamnatin da ta shude, lamarin da ya sanya hukumar lamuni ta duniya IMF ta dakatar da shirinta na lamuni ga Senegal.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Gaza: Witfkoff ya yi rangadi a wuraren da Amurka ta kafa domin tallafi August 2, 2025 ‘Yan Sudan dama na komawa gida bayan gudun hijira na tsawon shekaru a Masar August 2, 2025 Iran Ta Ce Batun Neman Dakatar Da Tace Uranium Zai Rusa Duk Wata Jarjejeniya Da Ake Son Cimmawa August 1, 2025 Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Duk Wani Zarge-Zargen Neman Bata Mata Suna August 1, 2025 Limamin Sallar Juma’a Ya Ce; Iran Zata Mayar Da Isra’ila Kufai Idan Ta Sake Kai Hari Kan Kasarta August 1, 2025 Kasar Slovenia Da Haramta Tura Makamai Zuwa Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 1, 2025 Kasar Spain Ta Bayyana Abin Da Ke Faruwa A Gaza A Matsayin Abin Kunya Ga Bil’Adama August 1, 2025 Iran ta yi watsi da zargin gwamnatocin turai na yunkurin kashe wasu mutane a kasashensu August 1, 2025 Mali da Rasha sun tattauna kan hadin gwiwar makamashi August 1, 2025 Afirka ta Kudu na shirin daukar matakan kauce wa tasirin harajin Amurka August 1, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Yusuf Ya Kaddamar da Shirin Dashe Itatuwa Don Yaki da Matsalolin Muhalli
  • Gwamnan Jihar Kwara Ya Hori Sabbin Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima Akan Kishin Kasa
  • Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura
  • Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5
  • Shirin ACRESAL Zai Samar Da Injinan Ban Ruwa Masu Amfani Da Hasken Rana A Jigawa
  • Mai Martaba Sarkin Dutse Ya Kaddamar Da Rabon Zakka Ta Shekarar 1446
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji
  • Sabon Shugaban Matatar Dangote Ya Bayyana Shirin Faɗaɗa Ayyukanta
  • Firayim Ministan Senegal Ya Bayyana Sabon Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Kasar