Ruwan Wuta Ne Kawai Maganin ‘Yan Ta’adda Ba Sasanci Ba – Mataimakin Gwamnan Zamfara
Published: 4th, August 2025 GMT
Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe.
Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.
Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare
Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji Al’ummomin da aka kudiri niyyar sake tsugunar da su sun hada da Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram da Darajamal. Zulum ya ce ana kafa matsugunan tanti na wucin gadi guda 1,000 a kowace al’umma, inda tuni aka kammala wacce ke Darajamal. “Mun himmatu wajen mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu na asali, a yanzu haka, ana ci gaba da gudanar da ayyukan a Mayanti, Goniri, Bula Kuriye da kuma Abbaram. “An kammala Darajamal. Ana haka gololo a kewayen wadannan al’ummomi don inganta tsaro,” in ji Zulum.Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp