Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule
Published: 4th, August 2025 GMT
Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haɗin kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki.
“Wannan aiki wani ɓangare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more rayuwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da ganin cigaba ya kai kowane yanki,” in ji Gwamna.
Da yake kaddamar da aikin, Gwamna Sule ya sake jaddada kudirin Gwamnatinsa na kada a bar ko wata al’umma a baya wajen kawo ci gaba, domin samar da jihar Nasarawa da tabbatar da lafiya da haɗin kan ‘yan jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamna Abdulrazaq Ya Duba Titi Mai Tsawo Kilomita 49
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa.
Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji a misalin hadakar kamfanin BUA.
Gwamna AbdulRazaq ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da aiwatar da ayyukan karbar haraji da kuma sauran dimbin tallafin da yake baiwa jihar.
“Muna duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da na Jihohi, wannan sabon titin Ilorin/Offa ne, kuma za ku ga yadda yake da inganci, dole ne mu gode wa Shugaba Bola Tinubu kan wannan aikin hanyar, babban nasara ne kamar yadda kuke gani,” in ji shi.
A cewarsa aikin zai takaita lokacin balaguro tsakanin Ilorin, Offa da kuma makwabta. Lokacin da aka kammala hanyar, lura cewa lokacin tafiya zuwa Offa daga Ilorin zai kasance mintuna 30.
Gwamna AbdulRazaq ya ci gaba da cewa, wannan wani kyakkyawan jari ne kuma wani samfuri ne na ajandar sabunta fata, wanda ke nuna cewa manufofin suna aiki kuma akwai ƙarin kuɗi don samar da ababen more rayuwa.
A nasa jawabin injiniyan kamfanin dake aikin, Abdulsalam Onaolapo, ya ce suna aiki ba dare ba rana domin kamala aikin akan lokaci.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU