Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje
Published: 5th, August 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata D’Tigress kyautar Dala dubu 100 da gidaje da lambar girmamawa ta OON, a matsayin karramawa bayan lashe kofin gasar ta bana.
Shugaban ya kuma ba masu horar da ’yan wasan dala 50,000 kowannensu.
Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ’yan wasan ƙwallon ƙafa mata wata Super Falcons makamanciyar wannan kyautar ta dala 100,000 da lambar girma.
A wannan Litinin din ce tawagar ’yan wasan ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka, wato Afrobasket.
Tawagar ta D’Tigress ta samu gagarumar tarba daga masoya ƙwallon kwando a Nijeriya, lokacin da suka sauka a filin jirgin sama na Abuja.
Ministar Mata Iman Sulaiman Ibrahim da takwararta ta al’adu, Hannatu Musawa ne suka yi wa tagawar rakiya tun daga birnin Abidjan zuwa Abuja.
A ranar Lahadi ne tawagar D’Tigress ta lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka, bayan doke Mali da ci 78-64 da aka fafata a Ivory Coast.
Wannan ne karo na bakwai da tawagar Nijeriya ta lashe kofin gasar a tarihi, wanda kuma shi ne na biyar a jere da ta ɗauka.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ƙwallon kwando yan wasan ƙwallon ƙwallon kwando
এছাড়াও পড়ুন:
NECO Ta Saki Sakamakon Jarrabawar 2025
A cewarsa, ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajistar jarrabawar; maza 685,514 da mata 681,696.
Daga cikinsu, ɗalibai 1,358,339 ne suka rubuta jarrabawar, waɗanda suka haɗa da maza 680,292 da mata 678,047.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp