Aminiya:
2025-08-03@21:16:53 GMT

An yi wa Jalo Daudu sarautar Tafarkin Gombe

Published: 3rd, August 2025 GMT

Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu sarautar Tafarkin Gombe.

Dakta Daudu, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Sakatare na Tarayya da Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe.

Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5 Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai 

Daga baya ya zama Shugaban Ma’aikata a Gwamnatin Jihar Gombe, sannan ya riƙe wasu manyan muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa.

Yanzu haka, shi ne Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikata na Ƙasa, inda yake wakiltar Jihohin Adamawa, Gombe da Taraba.

Dakta Daudu ya fito ne daga gidan sarauta a Gombe, kuma kakansa shi ne Hakimin Gombe na farko bayan masarautar ta koma zuwa birnin Gombe a yanzu.

Har ila yau, shi ne Ɗan Masanin Funakaye.

Sarautar Tafarki na ɗaya daga cikin manyan sarautun gargajiya a ƙasar Hausa.

Ana bai wa ɗan Sarki ko babban ɗan uwansa sarautar, kuma zai dinga bai wa Sarki shawara ko gyara idan ya zama dole.

Mai riƙe da wannan sarauta yana da damar shiga fada kai-tsaye da bai wa Sarki da masarauta shawara.

Asalin sarautar Tafarki ta samo asali ne tun zamanin Hausa Bakwai, kuma an ce mutum na farko da aka bai wa wannan sarauta shi ne Musa, a lokacin Sarkin Katsina Umaru Dallaje.

Yayin da yake sanar da naɗin, Sarkin Gombe, ya bayyana Dakta Daudu a matsayin mutum mai ƙwarewa, kuma wannan ne ya sa ya dace da wannan matsayi domin bai wa masarautar shawara.

Dakta Daudu, ya nuna farin ciki da godiyarsa ga Sarkin Gombe da majalisarsa, inda ya ce zai yi amfani da wannan dama wajen yi wa al’umma hidima cikin gaskiya da riƙon amana.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Naɗi Sarauta sarki Tafarkin Gombe

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa Kwanturola Janar na Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Kasa, Bashir Adewale Adeniyi na ta shan suka daga mutane daban-daban.

Yayin da wasu ke ganin abin da shugaban ya yi da cewa ya dace, wasu kuwa na ganin hakan ya yi hannun riga ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa.

Shin ko me dokar kasa ta ce game da wannan karin wa’adi da shugaban kasan ya yi?

NAJERIYA A YAU: Tinubu ya yi wa Arewa adalci a ayyuka da mukamai — Bayo Onanuga DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure

Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5
  • Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai 
  • Mai Martaba Sarkin Dutse Ya Kaddamar Da Rabon Zakka Ta Shekarar 1446
  • Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi
  • Etsu Nupe Ya Jaddada Buƙatar Sama Wa Sarakunan Gargajiya Gurbi A Tsarin Mulki
  • HOTUNA: Yadda aka yi Jana’izar Sarkin Gudi na Yobe bayan rasuwarsa a Abuja
  • Hanyar Da Matasa Za Su Bi Don Ceto Dimokuraɗiyyar Nijeriya Daga Rugujewa
  • NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?