Leadership News Hausa:
2025-11-04@06:46:11 GMT

LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya

Published: 5th, August 2025 GMT

LASTMA Ta Rufe Gidan Casu A Legas Saboda Karya Dokar Hanya

Hukumar Kula da Dokokin Hanya ta Jihar Legas (LASTMA) ta rufe wani gidan casu mai suna Vaniti Club House da ke kan titin Adeola Odeku a Victoria Island bisa laifin karya dokar harkokin sufuri ta shekarar 2018.

A cewar LASTMA, an rufe gidan casun ne saboda ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba a gefen titi da kuma toshe hanyoyi, lamarin da ke haddasa cunkoso da barazana ga lafiyar jama’a.

Wannan matakin ya samu jagorancin babban daraktan hukumar, Olalekan Bakare-Oki, tare da sashen ceto da tabbatar da doka.

Mutane 8 Sun Mutu A Wani Mummunan Hatsari A Hanyar Lagos Kwalara Ta Kashe Mutane 5 A Lagos, An Kai 60 Asibiti Ranga-Ranga

Hukumar ta ce wannan mataki na ɗaya daga cikin tsarin sabbin dabarun sa ido da aiwatar da doka a faɗin Legas, kuma gwamnatin jihar na da ƙudurin tabbatar da tsari, da tsaro, da ingantaccen tsarin zirga-zirga.

Shugaban LASTMA ya gargaɗi cibiyoyin nishaɗi, kamfanoni da jama’a da kada su yi katsalandan ga zirga-zirgar ababen hawa ko su haifar da haɗari ga lafiyar al’umma. Ya kuma buƙaci mazauna Legas su riƙa kai rahoto idan akwai cibiyar taro da ke hana zirga-zirga ta layukan gaggawa na LASTMA.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa

Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isa, ta ƙaryata labarin da wata jaridar intanet ta yaɗa cewa wai tana son ta auri shahararren dan TikTok, Ashiru Mai Wushirya, wanda ya yi tashe a kafafen sada zumunta a ’yan kwanakin nan.

A wani saƙo da ta wallafa, Mansurah ta ce labarin ƙarya ne kuma ya jefa ta da iyalinta cikin ruɗani da damuwa.

Ta ce, “Na shiga firgici bayan na ga wannan labarin. Ba ni da wata alaka da Mai Wushirya. Wannan sharri ne tsagwaron karya.”

Rahoton da aka yada a jaridar AMC Hausa ya yi iƙirarin cewa wai Mansurah ta ce ta shirya auren Mai Wushirya idan har yana son ta da gaske.

Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m An yi garkuwa da Mataimakin Shugaban Majalisar Dokokin Kebbi

Amma jarumar ta yi watsi da wannan iƙirarin, tana mai cewa jaridar ta ɓata mata suna kuma ta karya ƙa’idojin aikin jarida.

Ta ce, “Na kira su, na ba su awa 24 su sauke labarin, amma har yanzu ba su yi hakan ba. Sun kira ni sun ba ni hakuri a waya, amma labarin har yanzu yana nan. Wannan abu ya zubar min da mutunci kuma ya saka iyalina cikin tashin hankali,” ina ji ta.

Mansurah ta bayyana cewa yanzu tana cikin shirin ‘WalkAwayCancer’, wani gagarumin shiri na wayar da kan jama’a kan mcutar daji, amma wannan labarin karya ya yi ƙoƙarin karkatar da hankalin mutane daga ainihin aikinta.

“Kun hana ni barci da kwanciyar hankali saboda labarin da babu gaskiya a cikinsa. Amma in sha Allahu, za ku ji daga gare mu,” in ji ta cikin fushi.

Har zuwa lokacin da muka kammala wannan labarin dai, kamfanin AMC Hausa bai fitar da wata sanarwa ba dangane da ƙarar da Mansurah ke shirin kai musu bisa zargin yaɗa labarin ƙarya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Likitocin Gwamnati Sun Zargi Gwamnatin Tarayya Da Yaɗa Bayanai Na Karya
  • Gidan rediyo ya ɗauki nauyin sanya yara 40 a makaranta a Kano
  • Chadi Ta Rufe Iyakarta Da Nijeriya Bisa Dalilan Tsaro
  • ’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo
  • Uwargidan Gwamnan  Zamfara Ta Yaba Wa  Karamar Hukumar Gusau Bisa Shirin Tallafawa Jama’a
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Yabawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Hanyoyi A Fadin Jihar
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m