Aminiya:
2025-07-03@04:53:22 GMT

HOTUNA: Fashewar tankar gas ta kashe gomman mutane a Legas

Published: 12th, March 2025 GMT

Wata tanka ɗauke da gas ta yi bindiga a Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gomman mutane da jikkata da dama.

Lamarin ya faru ne a ranar Talata da dare a ƙarƙashin gadar mota ta Otedola, wadda tana daga cikin manyan hanyoyin da ke haɗe Legas da sauran sassan ƙasar.

HOTUNA: An hana Gwamna Fubara shiga Majalisar Dokokin Ribas Ukraine ta amince da ƙudurin tsagaita wuta a fafatawarta da Rasha

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a lokacin da tankar ke ƙoƙarin juyawa domin kai gas ɗin wani gidan mai, inda a nan ne ta faɗi ta yi bindiga.

Mutane da dama da suka shaida lamarin sun ce ya ƙazanta, sakamakon yadda wuta ta kama motoci da dama da kuma gidaje da ke kusa.

Wakilin kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya tattauna da wani mutum da ya tsira da ransa sakamakon lamarin.

“Tankar ta faɗo kan motata, inda ta tura ta gefen hanya. Sai na yi sauri na gudu bayan na gano cewa gas ne, sai tankar ta yi bindiga cikin ƙasa da minti uku,” in ji Ajayi Segun, wanda ya rasa motarsa ƙirar Sienna sakamakon faruwar lamarin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, a wani rahoto na wucin-gadi da ya fitar ya tabbatar da cewa lamarin ya rutsa da gidaje huɗu tare da haka kuma motoci 15 sun ƙone ƙurmus.

“Ana zargin hatsarin ya afku ne a lokacin da motar ke kokarin hawan hanyar Legas zuwa Ibadan ta gadar Otedola,” inji shi.

“Saboda haka, motar ta kife a kan hanya sannan ta yi bindiga nan take.”

“Har yanzu ana kididdige adadin rayukan mutanen da aka rasa, domin an gano gawawwaki biyu ne kawai.

“Lamarin ya kuma shafi wani asibiti mai zaman kansa, sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da halin da waɗanda lamarin ya shafa a can.

“Za a ci gaba da bayar da rahoto a yayin da ake ci gaba da aikin ceto,” kamar yadda ya bayyana.

Jami’in Hukumar Agajin Gaggawa na Kasa (NEMA) shiyyar Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinyole, ya tabbatar da faruwar lamarin da cewa suna ci gaba da ƙididdige asarar da aka yi.

A cewarsa, mutum daya ya mutu yayin da wasu hudu suka jikkata baya ga motoci 14 da shaguna hudu da suka ƙone ƙurmus.

A cikin ‘yan watannin nan, an samu fashewar tankokin mai dama a Nijeriya inda kusan mutum 300 suka rasu a ƙasar.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Jihar Legas Tankar Gas

এছাড়াও পড়ুন:

’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa

Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta cafke wani matashi mai shekaru 30 da ake zargin ya kashe mahaifiyarsa a Karamar Hukumar Gumel ta Jihar Jigawa.

Kakakin ’yan sandan Jigawa, SP Lawan Shi’isu, ya ce matashin mai suna Hussaini Abubakar ana zargin ya kashe mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75 da misalin karfe 8 na yammacin ranar 29 ga watan Yunin 2025.

Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU HOTUNA: An yi jana’izar Dantata a Madina

SP Shiisu ya ce matashin ya jikkata mahaifiyarsa da bulon ƙasa, kuma bayan an garzaya da ita asibiti ta mutu washegari.

Ya ce wannan lamari ya sanya rundunar ta gaggauta tura tawagar jami’ai kuma aka cafke matashi da a yanzu haka an soma gudanar da bincike a kan lamarin.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP AT Abdullahi, ya yi Allah-wadai da lamarin, yana mai bayyana shi a matsayin rashin imani na kololuwa.

Ya bai wa al’umma tabbacin cewa za su bi diddigin lamarin domin matashin ya girbi hukunci daidai da abin da ya aikata.

Rundunar ’yan sandan ta bukaci jama’a da su rika gaggauta mika rahoton duk wata alama ta tabin hankali ko cin zarafi domin kaucewa faruwar makamancin wannan lamarin.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Na Ci Gaba Da Cika Alkawarin Bude Kasuwarta Ga Duniya
  • Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Iran Ta Bayyana Lokacin Ci Gaba Da Ayyukan Cibiyoyinta Ta Nukiliya
  • ’Yan sanda sun kama wani mutum da jabun kuɗi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama matashin da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa
  • An Kashe Kusan Mutane 1500 Kan Sabanin Mazhaba A Kasar Siriya A Wata Guda
  • Togo: An Kashe Mutane 7 A Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati
  • Dalibai 29 Suka Rasu A Turmutsitsin Tserewa Ga Fashewar Taransifoma A Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya
  • Hare-haren Isra’ila sun kashe mana mutum 935 a yaƙin kwana 12 — Iran
  • ‘Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kan Al’ummar Benuwe, Sun Kashe ‘Yansanda 4
  •  Wani Dan Bindiga Dadi Ya Kashe Ma’aikatan Kashe Gobara 2 A Amurka