2025-09-24@17:21:07 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2233
«Yan Siyasa»:
’Yan bindiga sun kai hari garin Hunƙuyi da ke Ƙaramar Hukumar Kudan, a jihar Kaduna, inda suka kashe mutum ɗaya tare da sace wani ɗan kasuwa. Mutanen yankin sun ce maharan sun kai hari ne da misalin ƙarfe 12:30 na dare. ACReSAL ya tallafa wa manoma da buhunan iri 6,220 a Gombe Babu ɗaya daga...
Ministan harkokin wajen Iran ya ce: A shirye Iran take ta gudanar da shawarwari da Amurka, amma kan sharudda Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce; kasarsa a shirye take ta dawo da tattaunawar makamashin nukiliya da Amurka, amma tare da ba da tabbacin babu batun kai hari kan Iran. Ya bayyana cewa ba...
Maharan da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne a ranar Talata sun sace mata da miji tare da ’yarsu mai shekara ɗaya a cikin birnin Katsina. An dai kai harin ne a gidan ma’uratan, Anas Ahmadu, da matarsa Halimatu, da kuma ’yarsu Jiddah a Unguwar Kanada a yankin Ƙofar Ƙaura a Katsina. DAGA LARABA: Abin...
Haka kuma, a wani samame daban da rundunar ta kai a ranar 15 ga watan Agusta, 2025, ‘yansanda a ƙaramar hukumar Danko/Wasagu sun yi artabu da ‘yan bindiga a kusa da garin Dankade. Sun ceto mutum biyu da aka sace; Tukur Bello da Isyaka Abubakar, waɗanda aka sace a dajin Gairi na Jihar Zamfara a...
Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu...
Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana...
Fasinjoji na jirgin kasa wanda ya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya sauka kan layin dogo da misalign karfe 11:00 nan safe kusa da garin jere. Da dama daga cikin fasinjojin suna cikin tashin hankali saboda matsalolin tsaro da ake fama da shi a kan hanyar. Amma Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana...
Ribadu ya yaba da jajircewar sojoji da ‘yansanda da sauran jami’an tsaro da suka gudanar da aikin, yana mai cewa, wannan wata nasara ce da za a yi alfahari da ita a tarihin yaki da ta’addanci. A Guji Siyasantar da Tsaro Sai dai Ribadu ya gargadi shugabannin siyasa da masu rike da madafun iko...
Har yanzu babu tabbaci ko zai iya buga wasan. Arsenal na fatan cewa Saka da Odegaard ba za su daɗe suna jinya ba. A kakar da ta wuce, Saka ya sha fama da rauni har ya yi watanni uku ba ya wasa. Sai dai a bana Arsenal ta ƙara wasu sababbin ‘yan wassan gaba kamar...
Jirgin kasa dauke da fasinjoji a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya sauka daga kan titi. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin tarogon jirgin kasan sun mirgina a yayin da fasinjoji suka shiga tashin hankali.
A halin yanzu Sarkin Daura, ya hallara a filin gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya da a bana ake gudanarwa a fadarsa, inda za a gudanar da hawan daba na musamman. Sarkin Daura ya karbi bakuncin Gwamnan Jihar Damagaram daga Jamhuriyar Nijar, Kanar Yosouf Labo da kuma Sarkin Damagaram, Aboubacar Sanda Oumarou a fadarsa, albarkacin...
shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci a cikin harshen Yahudanci ya bayyana cewa: ‘Yan sahayoniyya sune wadanda aka fi kyamata a duniya Shafin Jagoran juyin juya halin Musulunci na yaren yahudanci a shafin sada zumunta na X ya rubuta cewa: Makiyar al’ummar Iran na kan gaba a yau ita ce, gwamnatin ‘yan sahayoniyya wacce ita...
Yau 26 ga watan Agusta take ranar murnar zagayowar bikin Ranar Hausa ta Duniya. A halin yanzu shirye-shirye sun yi nisa domin fara gagarumin bikin Ranar Hausa ta Duniya a birnin Daura, Jihar Katsina. An shirya gudanar da gagarumin bikin na bana a birnin Daura ne, kasancewarsa inda ake gani a matsayin asalin Hausawa,...
Harin sama na Isra’ila kan cibiyar lafiya ta Nasser Medical Complex a Khan Younis ya kashe ‘yan jarida biyar ranar Litinin. Daga cikinsu akwai mai ɗaukar hoto Moaz Abu Taha da Mariam Abu Daqqa da mai ɗaukar bidiyon gidan talabijin na Palestine TV Hussam al-Masri, da kuma ɗan jaridar Al Jazeera Mohammad Salama da ma’aikacin...
A duk ranar 26 ga watan Agustan kowace shekara ake bukukuwan zagayowar Ranar Hausa ta Duniya. An fara wannan biki ne tun a shekarar 2015, inda wani tsohon ma’aikacin sashen Hausa na BBC kuma ma’aikacin TRT Hausa a yanzu, Abdulbaƙi Jari Aliyu ya ƙirƙiro tare da wasu masu amfani da shafukan sada zumunta. An...
Na yi imani babu rayuwa ba tare da harshe ba, domin duk wata al’umma tana da buƙatar harshe domin gudanar da rubuce-rubuce, kimiyya da fasaha. Amma an yi sakaci da nazarin harshen Hausa, duk da cewa yana cikin manyan harsunan duniya masu ƙarfi da adabi. Don haka zan fara bayyana matsalolin, sannan in kawo shawarwari....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan fara bikin harshen Hausa ta duniya shekaru goma da suka gabata ne dai manazarta suke bayyana irin cigaba da habbakar da yaren ya samu. Harshen Hausa ya samu zama a mataki na 11 cikin harsunan da ake amfani dasu a fadin duniya tare da fatan nan...
Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics. Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara...
Bikin ranar ba iya Nijeriya kawai ya tsaya ba. Ana gudanar da bikin a ƙasashe da dama irin su Ghana, Amurka, Turkiyya da kuma Dubai, inda al’ummar Hausawa ke yin rayuwa. A waɗannan wurare, ana shirya wasanni irin gargajiya kamar wasan Dambe, nuna abinci da kayayyakin al’adu, da kuma gudanar da taruka, tattaunawa kan harshen...
Kafar CGTN da jami’ar Renmin ne suka gudanar da nazarin ta hannun cibiyar inganta tuntubar juna tsakanin kasa da kasa a sabon zamani. An kuma gudanar da nazarin ne tsakanin mutanen manyan kasashen duniya da na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
A wannan Litinin ɗin Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sauka a Brasilia da ke ƙasar Brazil, inda ya fara ziyarar aiki ta kwanaki biyu, domin amsa gayyatar da ƙasar ta yi masa. Tinubu ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban Brazil, Inacio Lula da Silva, inda aka yi masa faretin ban girma irin na soji...
Amma, a cikin wata sanarwa mai kakkausar murya da ya fitar a ranar Litinin, Daraktan Yada Labarai na Gidan Gwamnati, Sanusi Bature DawakinTofa, ya karya rahoton da cewa “aiki ne na tatsuniyoyi, wadanda abokan hamayyar siyasa suka shirya su, domin bata wa gwamnati suna don su samu madafun iko gabanin zaben 2027. “Kowane tsabar...
Har ila yau, rahoton ya ce, matakin na Amurka muradu da dabarunta na siyasar duniya kadai yake karewa, yayin da take dogaro da karfin soja wajen haifar da tsaiko ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankuna da ma tsarin harkokin tekun na duniya. Bugu da kari, ya soki ayyukan Amurka yana cewa, sun saba...
Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiya sun bukaci hadin kan kasashen musulmi don magance matsalolin da al-ummar falasdinu take faskanta a gaza. Sun bayyana cewa akwai bukatar kasashen musulmi su san yadda zasu yi don nisar da abinci zuwa yankingaza da kuma kawo karshen kissan kiyashin da HKI take yi a yankin. Tashar taabijin...

Sin Ta Shiga Jerin Kasashe 3 Dake Sahun Gaba Wajen Gudanar Da Cinikayya Da Kasashe Da Yankunan Duniya 157
Shugabar hukumar kwastam ta kasar Sin Sun Meijun, ta ce Sin ta shiga jerin kasashe uku dake sahun gaba wajen gudanar da cinikayya da kasashe da yankunan duniya 157. Sun Meijun, ta bayyana hakan ne a Litinin din nan yayin taron manema labarai da ta gudana, inda ta ce a shekarar 2024 darajar hada-hadar...
’Yan Arewa a Kasuwar Alaba Rago, shahararriyar kasuwar ’yan Arewa a Jihar Legas sun roki gwamnatin jihar ta biya su diyya kan asarar da suka yi sakamakon rushe kasuwar da gwamnati nta yi. Sun bayyana cewa asarar da suka tafka ta haura Naira biliyan 20 bayan Gwamnatin Legas ta rusa masallatai sama da 40 da...
Kwamandan sojojin Iran ya yi barazanar mayar da martani mai muni da zai haifar da nadama ga makiya Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Amir Hatami ya jaddada cewa: Sojojin kasar Iran da jarumtarsu suna tsayawa da dukkan karfinsu wajen fuskantar barazanar makiya. A yayin ziyarar da ya kai Jami’ar Kimiyyar Sojin Ruwa ta...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya shekara arbain zuwa sama ya san irin tarbiyyan da ya samo daga wurin iyayen sa a da baya can, irin mu’amalan dake tsakanin sa da iyaye har ma da shakuwan dake tsakanin ‘ya’ya da iyaye. A yanzu kuwa abubuwa sun canza daga yadda aka...
A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II. Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya...
Ɗariƙar Tijjaniyya a Jihar Gombe, ta yi babban rashi bayan rasuwar ɗaya daga cikin fitattun malamanta, Sheikh Umar Bojude. Sheikh Bojude shi ne babban limamin Masallacin Juma’a na Alhaji Gidado Dalibi Yahaya (AG Dalibi). Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC a Gombe...
Amma abin takaici, duniya ba ta san laifukan da Japan ta yi wa kasar Sin a lokacin yakin ba sosai. Har yanzu gwamnatin Japan ba ta nemi afuwar Sin da sauran kasashen Asiya da ta jefa cikin ukuba ba. Har ma, ‘yan siyasar Japan masu tsattsauran ra’ayi na ci gaba da gurbata wannan tarihi,...
A yau ake gurfanar da wani majinyaci mai shekaru 40, zai gurfana a kotu, bisa zargin cin zarafin wata likita mai suna Fatima Umar Gamsa a asibitin Ƙwararru na tunawa da marigayi Janar Sani Abatch da ke Damaturu Jihar Yobe. Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya reshen Jihar Yobe, Dakta Umar Aji, ya ce kungiyar ta kai...
Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani. Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba ‘Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin ruwa da ya faru a garin Kojiyo dake karamar hukumar Goronyo a jihar sakkwato sun samu kansu cikin damuwa. Yayin da kalilan daga cikin wadanda abun ya rutsa dasu suka tsira da ransu, wasu da dama sun mutu,...
Wani mutum ya soka wa budurwarsa mai suna “Ima” wuka har lahira a unguwar Okereke Street da ke garin Fatalkwal na Jihar Ribas. Mutumin, wanda ake wa lakabi da “Doctor” ya daba wa budurwar tasa mai suna “Ima” wuka ne bisa zargin tana cin amanarsa. Lamarin ya faru ne da yammacin Lahadi, wanda shaidu a...
Wasu masu garkuwa da mutane sun yi hatsarin mota a hanyarsu ta zuwa rabon kudin fansar mutanen da suka sace a Jihar Nasarawa. Jami’an tsaro sun kwato bindigogi uku da tsabar kudi Naira miliyan 6.9 daga motar ’yan bingidar bayan hatsarin motar a yankin Garaku, daura da wani shingen bincike na Jami’an Kula da Lafiyar...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; Iran ba za ta amince da duk wani sauyi a kan iyakokin yankin siyasa ba Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya ce gabanin ziyarar shugaba Masoud Pezeshkian zuwa kasar Armeniya cewa tabbatar da yanayin siyasar yankin bai canza ba, shi ne batun tuntubar da shugaba Pezeshkian...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabu 16 a jihohi 12 na ƙasar nan. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaban...
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa shuwagabannin kasashen turai kan cewa ya amince da shawara shugaba Putin na musayar kasa don samar da zaman lafiya. Majiyoyi biyu wadanda basa son a bayyana sunayensu kuma kusa da Trump a taron na Alaska ya bayyanawa jaridar ‘The guardian’ ta kasar Burtania a jiya Asabar kan cewa,...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ondo, ta cafke wani matashi mai suna Azeez Bello, mai shekaru 29, wanda ya kitsa garkuwa da kansa domin karɓar kuɗin fansa Naira dubu 500 daga hannun iyayensa. Kakakin rundunar, Ayanlade Olushola, ya bayyana cewa Bello, ɗan asalin garin Ipele da ke Ƙaramar Hukumar Owo, ya yi haka ne bayan mahaifinsa...
Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa sojojin JMI a shirye suke su shiga yaki a ko dauce, amma yana ganin yiyuwar a sake shiga yaki da HKI nan kusa yana da wuya. Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto Abbas Argchi yana fadar haka, a daren Ashamis da ta gabata, a...
Ga hotunan yadda ake gudanar da zaɓen cike gurbi a sassan Najeriya.
A wasu yankunan Jihar Katsina da suka daɗe cikin fargaba da hare-haren ’yan bindiga, zaman lafiya ya fara dawowa sakamakon sulhu da al’umma suka yi da masu tayar da ƙayar baya. Wannan sulhu, wanda ba a haɗa gwamnati ba, ya bai wa manoma damar komawa gonakinsu cikin daminar bana. Manoma sun fara noma cikin...
Tun Farko tawagar gwamnatin ta Isa fadar hakimin Barnawa domin isar da sakon ta’aziyyar gwamnatin jihar kaduna na rashin matashi inda suka tabbatar wa da Hakimin cewa gwamnatin jihar kaduna zatayi duk Mai yiwuwa wajen ganin anyiwa matashi Abubakar adalci da kuma gano dalilin mutuwarsa. Hakazalika, tawagar gwamnan sun Kai ziyarar jaje gidan mamacin...
Tinubu ya kara da cewa tun bayan karbar mulkinsa, gwamnatinsa ta bayar da fifiko wajen samun damar kudi kuma ta yi alkawarin tallafa wa harkokin kasuwanci da zai habbaka samar da ayyuka da samun kwarewa da kuma masana’antu. Ya yaba wa gwamnatin Kuros Ribas kan kirkiro shirin tattaunawa da fasahar zamani a harkokin kasuwancin jihar,...
Da safiyar yau Jumma’a, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da rahoton tattalin arzikin kasar na watan Yuli, inda ta bayyana cewa, kasar Sin ta gaggauta daidaita manufofin tattalin arziki daga manyan fannoni, tare da inganta dunkulewar manyan kasuwanni cikin sassan kasar, ta yadda aka tabbatar da bunkasuwar tattalin arziki cikin tsari, da kara...
An sami gawar wani sojan HKI wanda ya taba yaki a Gaza wanda kuma ake zaton shi ya kashe kansa. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Jaridar HKI da yaren Hebru mai suna Yedioth Ahronoth yana fadar cewa an gano gawar sojan dan shekara 28 wanda ba’a bayyana sunansa ba a dajin...

Sin Ta Soki Lamirin Amurka Dangane Da Wanke Japan Daga Laifukan Da Ta Tafka Yayin Yakin Duniya Na Biyu
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya soki lamirin kasar Amurka, dangane da yadda ta wanke Japan daga laifukan da ta tafka, yayin yakin duniya na biyu. Jiang Bin, wanda ya yi sukan a Juma’ar nan, ya kira hakan a matsayin mummunan karan-tsaye ga ainihin abun da ya auku a tarihi, kana tozarta damuwar...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a uau shiri wanda yake kawo mako labarai masu muhimmanci a makon da ya gabata, wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakrwa , tsaro da sauransu. Sannan mu yi masu Karin bayani daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane...