Dare ya jaddada cewa Nijeriya kasa ce mai addinai da dama, wacce aka gina bisa juriya, zaman lafiya, da girmama juna tsakanin mabambantan addinai, al’ummomin da ya ce Tinubu ya shugabanta.

 

Dare ya ambaci maganar Shugaban Kasa inda ya jaddada cewa Nijeriya “kasa ce mai cikakken ‘yanci da girma, wadda aka gina bisa bangaskiya da juriyar jama’arta,” ya kara da cewa “Babu wani addini da ake zalunta, kuma babu wata al’umma da aka ware.

Yana nuna misali da rayuwar Shugaban Kasa a matsayin shaida ta juriya da fahimtar addinai, Dare ya bayyana cewa Shugaba Tinubu, Musulmi ne da yake auren fasto mai bin addinin Kirista.

Ya kuma ruwaito Shugaban yana cewa, “Gaba da kiyayya ba su da gurbi a gare mu. Soyayya ce abin da muke wa’azanta, kuma dole mu rika son juna.”

Dare ya bayyana cewa labarin “kisan kiyashi ga Kiristoci” babban rudani ne da ya kau da kai daga ainihin matsalolin tsaro da Nijeriya ke fama da su, inda ya bayyana cewa kasar na yaki da ta’addanci da ‘yan fashi da ke yin barna don samun riba da tayar da hankali, ba saboda addini ba.

Ya ce, “Wadannan ‘yan ta’adda suna kai hari kan fararen hula ba tare da bambance coci-coci, masallatai, kasuwanni, makarantu ko kauyuka ba, suna kashe ’yan Nijeriya masu bin addinai da kabilu daban-daban.”

Ya yi gargadin cewa fassara wannan rikici a matsayin yakin addini yana kara karfafa ’yan ta’adda ne tare da raunana hadin kan kasa.

Ya yi kira ga Cruz, Maher da sauran su da su nemi sahihan bayanai kafin su yada karya da ke bata sunan Nijeriya tare da karfafa ’yan ta’adda.

Dare ya kammala da cewa, “Gaskiya abu daya ce mai sauki , Nijeriya ba ta fuskantar kisan kiyashi ga Kiristoci; tana yaki ne da ta’addanci da ke kai hari ga kowa da kowa. Duk wanda ya yi zargi, to ya gabatar da hujja.”

A wani bangaren kuma majalisar dattawa ta zartar da kudurin tattauna lamarin da zaran sun kama aiki gadan-gadan daga hutun da suka dawo ranar Talata da ta gabata. Wannan na zuwa ne bayan da Sanata Ali Ndume da Sanata Sani Musa da Sanata Aliyu Wamakko da kuma Sanata Ibrahim Bomai suka gabatar da kudurin neman haka ga zauren majalisar ranar Talata.

A cikin kudurin da suka gabatar, sanatocin sun nemi bangarorin gwamnati da suke da ruwa da tsaki a kan lamarin musamman ma’aikatar kasashen waje da hukumomin tsaro su tabbatar da bayar da kididdiga da bayanai da suka kamata don karyata wannan frofaganda na kafafen yada labarai na kasashen waje suke neman bata sunan Nijeriya a idon kasashen duniya.

Sanata Ndume ya nuna damuwarsa na yadda ake yada labaran kanzon kurege a kan halin tsaron da kasar nan ke fuskanta. Yana mai cewa, dukkan bangarorin al’umma ke dandana matsalar rikicin ba wai wasu addinai ko kabilu ba.

Wani mai wasan barkwanci na kasar Amurka ne dai mai suna Bill Maher, ya yi ikirarin cewa, an kashe fiye da Kiristoci 100,000 a kisan kare dandi da ake yi wa Kiristocin Nijeriya.

Haka kuma wasu kugiyoyin musulmai kamar MURIC ta bayyana cewa, ayyukan ‘yan ta’adda a Nijeriya a cikin shekararun ya shafi duk wani dan Nijeriya ta hanyoyi daban daban. Haka kuma an tabbatar da cewa, lamarin ya ci rayukan musulmai fiye da 32,000 a cikin shekara uku. Don haka dukkan bangarorin ‘yan Nijeriya ke dandanawa” ya kuma kamata a hada hannu gaba daya don kawo karshen ayyukkan ‘yan ta’adda” in ji kungiyar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Da Ɗumi-ɗumi: Tinubu Ya Zaɓi Farfesa Amupitan A Matsayin Sabon Shugaban INEC  October 9, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta October 9, 2025 Manyan Labarai Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin October 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana kaduwa da rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci kuma jagoran Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Fitaccen malamin ya rasu a Bauchi ranar Alhamis yana da shekaru 101.

Abubuwa 20 da ya kamata ku sani game da Sheikh Dahiru Bauchi Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka

A cikin wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran da ya sadaukar da rayuwarsa wajen koyarwa, wa’azi da jagorantar al’ummar Musulmi.

Tinubu ya ce rasuwar malamin ba wai asara ce ga iyalansa da almajiransa kawai ba, har ma ga ƙasa baki ɗaya.

“Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba ne kuma murya ce ta daidaito da hikima. A matsayinsa na mai wa’azi kuma babban mai fassarar Alƙur’ani mai tsarki, ya kasance mai kira ga zaman lafiya da tsoron Allah. Rasuwarsa ta bar babban gibi,” in ji Shugaban Ƙasa.

Ya tuna da albarka da ya samu daga marigayin a lokacin shirye-shiryen zaɓen 2023.

Shugaban Ƙasa ya miƙa ta’aziyya ga almajiran malamin a faɗin Najeriya da wajen ƙasar, yana mai kira da su dawwamar da sunansa ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, tsoron Allah da kyautatawa ɗan adam.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi ta bar babban gibi a Najeriya – Tinubu
  • Shugaba Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta-baci Kan Harkar Tsaro Tare da Bada Umurnin Daukar Sabbin Jami’ai
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Tukur Mamu ya karbi N50m daga kuɗin fansar harin jirgin kasan Kaduna – DSS
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?
  • Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa