Leadership News Hausa:
2025-11-27@20:50:11 GMT

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Published: 10th, October 2025 GMT

Cutar Kwalara Na Ci Gaba Da Yi Wa ‘Yan Nijeriya Kisan Mummuƙe

Yawan mace-mace ta hanyar cutar kwalarar, na faruwa ne duk da biliyoyin Nairori da aka ce gwamnati da abokan huldar kasa da kasa suna kashewa, domin kokarin ganin an dakile ta.

 

Wadannan kudade sun hada da kason kasafin kudi na shekara-shekara, wanda ya kunshi miliyoyin Nairori; akwai dala miliyan 700 da bankin duniya ya bayar domin samar da tsaftataccen ruwa sha, tsaftar muhalli a fadin kasa baki-daya, tallafin dala miliyan 2 daga Majalisar Dinkin Duniya, dubban daruruwan allurar rigakafin cutar kwalara da asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka bayar da sauran makamantansu.

Alkaluman da aka samu daga cibiyar NCDC, sun nuna cewa a cikin 2020, kasar ta samu rahoton kimanin mutane 3,513 da ake zargi da kamuwa da cutar da kuma mutuwar mutum 95. Adadin wadanda suka mutu ya karu kwarai da gaske a shekarar 2021 tare da mutum 111,062 da ake zargi da kamuwa da cutar, kazalika akwai mutum 3,604 da suka mutu a cikin jihohi 33, ciki har da babban birnin tarayya Abuja.

Har ila yau, kwayar cutar kwalara ta ‘Bibrio cholerae’ ce ta haifar da ita, cutar kwalara cuta ce da ake saurin kamuwa da ita; ta hanyar gurbataccen abinci da ruwa da kuma rashin tsaftar muhalli ke haifar da ita.

Barkewar cutar, ta fi yin kamari a lokacin damina, daga watan Mayu zuwa watan Oktoba, yayin da ambaliyar ruwa da gurbatattun hanyoyin ruwa ke kara ta’azzara wajen yaduwa. Alamomin cutar kwalara sun hada da yawan zawo, amai da murdawar ciki da kuma rashin ruwa a jiki. Za kuma a iya saurin tarar cutar ta hanyar amfani da ruwan gishi da sikari da kuma rigakafi, idan ba a yi saurin aiwatar da hakan ba, za a iya rasa rai cikin kankanin lokaci.

Shekarar 2021 na daya cikin wadda ake zargin mutane kimanin 111,062, sun kamu da cutar tare da mutuwar kusan mutum 3,604 a jihohi 33 ciki har da babban birnin tarayya Abuja tare da yara ‘yan shekara daga 5 zuwa 14 da suka fi kamuwa da cutar.

Jihohin Bauchi, Jigawa, Kano da Zamfara ne ke da kashi 53 cikin 100 na dukkanin masu fama da cutar.

A shekarar 2022, alkaluman yawan mace-macen sun ragu zuwa 592, wato da kashi 2.5 cikin 100, kazalika a cikin 23,763 da ake zargi sun kamu da cutar daga jihohi 32 ciki har da babban birnin tarayya Abuja, Jihohin Borno, Yobe, Katsina, Gwambe, Taraba da Kano, na da kashi 83 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar.

Daga cikin mutum 3,683 da ake zargin sun kamu da wannan cuta ta kwalara a 2023 a cikin jihohi 31, an samu rahoton mutuwar mutum 128 (kashi 3.5 cikin 100), inda yara ‘yan kasa da shekara biyar suka fi kamuwa da cutar, sai kuma wadanda ke tsakanin shekaru biyar zuwa 14. Jihar Zamfara ce ke da kashi 25 cikin 100 na dukkanin wadanda ake zargi da kamuwa; yayin da Jihohin Kuros Riba, Katsina, Bayelsa, Ogun, Ebonyi da kuma Neja ke da kashi 57 cikin 100.

Adadin ya sake karuwa a shekarar 2024 zuwa mutum 10,837 da ake zargin sun kamu da cutar da kuma mutuwar mutane 359 deaths (kashi 3.3 cikin 100) a fadin jihohi 36 na kasar nan a ranar 29 ga watan Satumba, wanda shi ne na karshe da cibiyar NCDC ta fitar kan bullar cutar ta kwalara a wannan shekarar. Har ila yau, yara ‘yan kasa da shekara biyar sun fi kamuwa da cutar, sai kuma wadanda ke tsakanin shekara biyar zuwa 14. Kazalika, Jihar Legas ta samu kashi 43 cikin 100 na kafatanin wadanda ake zargi da kamuwa da cutar.

A cikin watan Yulin bana, yayin da aka kaddamar da neman tallafin gaggawa na kimanin dala miliyan 20, domin yaki da cutar kwalara a Nijeriya da sauran kasashen yammacin Afirka da kuma Afirka ta tsakiya, daraktan yanki na UNICEF, Gilles Fagninou ya ce; “Zuwa karshen watan Yuni, Nijeriya ta samu rahoton bullar cutar kwalara kimanin 3,109 da kuma mutuwar mutum 86 cikin jihohi 34.”

Ya ce, yawan adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar ne yasa Nijeriya ta kasance a matsayin kasa ta biyu da cutar ta fi yin kamari a yammacin Afirka da kuma Afirka ta tsakiya.

Ya kara da cewa, “Mamakon ruwa da ambaliyar ruwan sama da kuma yawan wadanda suka rasa matsugunansu, duk suna kara ruruta wutar hadarin kamuwa da cutar kwalara da kuma jefa rayuwar yara cikin hadari. Yara kanana, sun fi fuskantar barazanar kamuwa da cutar kwalara, sakamakon dalilai kamar haka; rashin tsafta, rashin samun tsaftataccen ruwa sha, rashin tsaftace muhalli da kuma rashin isasshen ruwa a jikin mutum,” in ji shi.

 

Yadda Muka Rasa Su Cikin Kankanin Lokaci- Iyalai

Wata fita da matar Musa Aliyu ta yi da ‘ya’yanta uku cikin farin ciki, ta kare bakin ciki da kuka ga ‘yan’uwa; bayan halartarsu wani bikin daurin aure a unguwar da ke makwabtaka da cikin birnin Bauchi. Bayan ‘yan sa’o’i kadan da kammala cin abinci a wajen taron, sai suka fara amai da bayan gida a-kai-a-kai.

“Matata da ‘ya’yana uku, sun kamu da cutar bayan cin abinci a wajen wani wurin daurin aure a Bauchi, ‘yata ta farko ce ta fara kamuwa; kafin daga bisani sauran ‘ya’yan nawa biyu suka kamu da kuma mahaifiiyarsu,” wani mazaunin ‘Federal Low Cost Housing Estate’.

Duk da cewa, wasu daga cikinsu sun tsira da rayukansu; amma Muhammad Aliyu, mai shekaru 5 ya rasu. Yanzu haka, shekara hudu kenan da rasuwarsa, amma mutuwar tasa ta bar tabon dab a zai taba gogewa ba a dangin.

A shekarar 2021 a Bauchin, cutar ta yi wa ‘ya’yan Fatima su bakwai yankan kauna, wadanda mahaifinsu ya rasu shekara biyu da suka wuce. ‘Yar’uwar Fatima, Anisha Saidu, wadda ke zaune a Unguwar Kofar Ran ta bayyana cewa; ta rasu ne sa’o’i kadan bayan ta fara nuna alamun cutar ta kwalara.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Karyata Batun Yi Wa Kiristoci Kisan Ƙare Dangi October 10, 2025 Labarai ‘Yansanda Sun Kama Motar Hilux Ɗin Da Aka Sace A Kano A Hanyar Zuwa Nijar October 9, 2025 Labarai Jami’an Tsaro Sun Cafke Ɓarayin Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki Na Hanyar Mando Zuwa Jos October 9, 2025

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: da ake zargi da kamuwa sun kamu da cutar kamuwa da cutar cutar kwalara da ake zargin

এছাড়াও পড়ুন:

An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya

Sufeto Janar na ’Yan sandan Nijeriya, Olukayode Egbetokun, ya sanar da cewa sun aiwatar da umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na janye dakarunsu daga gadin ɗaiɗaikun mutane da ake kira VIP.

IG Egbetokun ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a yau Alhamis, yana mai cewa zuwa yanzu sun janye dakaru 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya.

Mbappe ya ci ƙwallaye 4 rigis a wasan Madrid da Olympiacos An rantsar da sabon shugaban kasa a Guinea-Bissau bayan juyin mulkin sojoji

“Wannan karon za mu aiwatar da umarnin da kyau saboda umarnin shugaban ƙasa ne,” in ji shi.

“Babu wani gwamna, ko minista, ko abokaina da za su kira su takura min saboda sun san cewa umarnin shugaban ƙasa ne. Ina kuma da tabbacin cewa ba za su uzzura wa kwamashinonin ’yan sanda ba ma.”

Ya ƙara da cewa za su tura jami’an da aka janye zuwa “wuraren da aka fi buƙatarsu, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci.”

Aminiya ta ruwaito cewa, a bayan nan ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da aika ’yan sanda ga manyan mutane domin ba su tsaro na musamman, yana mai mayar da su zuwa aikin tsaro da ya shafi al’umma baki ɗaya.

Kazalila, a ranar Laraba, 26 ga watan Nuwamba ne Tinubun ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro a faɗin ƙasar, inda ya bayar da umarnin a ɗauki matakan gaggawa domin magance matsalolin tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Shugaban ya ce a ɗauki sababbin ’yan sanda 20,000, ƙari a kan guda 30,000 da ya fara amincewa a ɗauk, wanda za a yi amfani da sansanonin horar da masu yi wa ƙasa hidima wajen horar da sababbin ’yan sandan da za a ɗauka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin Nijeriya
  • Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
  • Super Falcons za su ƙaurace wa wasannin Nijeriya saboda riƙe musu alawus
  • Tabarbarewar Tsaro na Barazana ga Siyasar Ƙasar Nan Gabanin Zaɓen 2027-Ado Doguwa
  • Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Oyo saboda aikata kisan kai
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Yi Wa Yara Miliyan 1.5 Rigakafin Cutar Shan Inna
  • ’Yan bindiga sun sace mutum 8 a Kano
  • NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta
  • Gwamna Namadi Ya Kaddamar da Titi Mai Tsawon Kilomita 13 a ‘Yankwashi